KANUN LABARAI
Ba za mu sanya jam’iyyar da bata da dan takara ba a takardar kada kuri’a-Sheka
Aminu Abdullahi
Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSEIC) ta ce jam’iyyun da suka sayi fom na takara ne kawai za su fito a jikin takardar kada kuri’a (ballot paper).
Shugaban hukumar farfesa Garba Ibrahim Sheka ne ya bayyana haka yayin zantawa da jaridar Kano Focus a ranar Litinin.
Sheka ya ce duk jam’iyar da bata da dan takarar shugaban karamar hukuma ko Kansila ba za a sanya ta a takardar kada kuri’a ba.
Ya ce hukumar zabe ta kasa ta basu sunayen jam’iyyu goma sha takwasne,
Amma cikin su matukar jam’iya ta gaza samar da dan takara na kansila ko shugaban karamar hukuma to tabbas ba za a sanya wannan jam’iya ba.
Ya kara da cewa sanya jam’iyyun da basu da dan takara a takardar kada kuri’a na rikita musu zabe.
“Ciresu zai sa kowacce jam’iya sunan ta ya fito kuru-kuru ta yadda kowa zai gane jam’iyar da zai zaba,” a cewar sa.
Wanda jam’iyya ta fitar a sayarwa da fom
Farfesa Sheka ya kara da cewa babu dan takarar da za su sayarwa da fom sai wanda jam’iyyarsa ta aike da sunan sa.
Ya ce dolene duk wanda zai sayi fom yazo da wata shaida da za ta nuna cewa shi ne wanda jam’iyya ta tsayar kafin mu amince masa.
“Babu wanda zai zo kai tsaye mu siyar masa da fom zamuyi amfani ne da sunayen ‘yan takarar da jam’iya ta bamu.
Dole ne dan takara yanuna mana wata shaida da za ta tabbatar cewa shi ne dan takarar da jam’iya ta tsayar,” a cewar sa.
Malam Sheka ya kara da cewa wajibine kowanne dan takarar da jam’iya ta tsayar ya sayi fom tare da bayar dashi a hukumar zaben ta jihar Kano.
Ya ce hukumar za ta rufe siyar da fom da kuma karba daga ranar 3 ga watan Disamba mai kamawa.
Doka bata hana ba
Wani lauya a nan Kano mai suna Ibrahim Abdullahi Chedi ya ce rashin kin sanya jam’iyun da ba su da dan takara a cikin takardar kada kuri’a ba laifi bane.
Ya ce inda lefin yake shi ne ace jam’iya nada dan takara da ya sayi fom amma kuma ba a sata a cikin takardar kada kuri’ a ba.
A cewar sa hakan ka iya jawowa a soke zabe gaba daya koda kuwa an sanar da wanda yaci.
“Za su iya yin haka don rage kudaden da za su kashe na buga takardar kada kuri’a lokacin zabe amma babu wata doka data ce dole ne hukumar zabe ta sanya jam’iyar da bata da dan takara a cikin takardar kada kuri’a wato ballot paper,” a cewar sa.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.