Connect with us

KANUN LABARAI

Yanayin sanyi: Hadarin da ke tattare da sana’ar wanki a Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

Wani kwararen likita a nan Kano Dr Bashir Bala Getso ya ce masu sana’ar wanki a lokacin sanyi na cikin hadarin kamuwa da cutuka masu hadarin gaske.

Kano Focus ta ruwaito Dr Bala Getso wanda shi ne shugaban kwalejin kula da lafiyar muhalli ta jihar Kano ya ce masu sama’ar za sui ya kamuwa da cutukan da suka hadar da ciwon sanyin kashi da nimoniya, ciwon kafa da kuma ciwon sikila.

Bala Getso ya ce kowanne dan adam akwai yadda jikinsa  ke karbar yanayi.

Ya kara da cewa masu sana’ar wanki ka iya kamuwa da cututtuka da kan dauki lokaci ba tare da an fahimce sub a ma baki daya..

Haka zalika akwai wasu cututuukan da kan tsahi sakamon yadda suke mu’amila da ruwa a koda yaushe da suka hada da ciwon sikila da nimoniya.

Malam Getso ya kuma ce wajibine masu sana’ar wanki su rage yawan lokutan da suke dauka suna yin wanki.

“I dan sunayin wanki kamar ranaku biyar a sati to kamata ya yi su mai dashi ranaku uku.

“Haka kuma idan suna yin wankin a wa biyar a rana kamata ya yi su rage awanni don kare lafiyar su,” a cewar sa.

Ya kara da cewa ga wadanda sana’ar ta zame musu dole musamman ma wadanda ke aiki a bakin rafi to kamata yayi su dinga bari sai rana ta fito.

Ya kuma ce yana da kyau a irin wannan yanayi na sanyi masu sana’ar wanki su rinka ziyartar likitoci domin samun shawarwari kan yadda za su kare kansu daga illolin da yanayin sanyi ke tafe dasu.

Suma masu sana’ar wakin da jaridar Kano focus ta zanta da su sun ce suna yin la’akari da yanayin na sanyi wajen kare lafiyar su.

Abdulrashid Ibrahim dake sana’ar wanki a unguwar Sharada ya ce kafin shigowar sanyi yana fara  sana’ar sa ne da misalin karfe shida na safe.

Amma yanzu saboda yanayin da ake ciki yakan bari rana ta fito sosai kamar karfe daya kafin ya fara.

Ya kuma ce farashin da yake yin wanki bai sauyaba dukkuwa da yanayin sanyin da ake ciki.

“Ina wanke riga da wanda ko da zani naira dari biyu idan za a saka sitati, idan kuma Babu sitati to naira dari da hamsin nake karba,” a cewar sa.

Malam Ibrahim ya ce baya zuwa asibiti domin a duba lafiyar sa amma duk inda yaji ana saida maganin gargajiya da ya shafi cutar sanyi to yana siya yayi amfani dashi.

Shima wani mai wanki Sa’idu Sulaiman dake unguwar Gwale Sani Mainagge ya ce duk da yanayin sanyin da ake ciki amma bai kara farashin kudin wanki ba.

Ya ce akwai masu wanki sosai da idan ya kara kudin masu kawo masa wanki za su koma kaiwa wasu daban.

Haka zalika ya ce yana sa rigar sanyi da safa ta hannu da kafa don kare kansa daga ciwon sanyin kasancewar illar sanyi kan dade a jikin mutum.

“Bamu da gida a nan kusa hakan tasa bama samun damar sirkawa da ruwan dumi,” a cewar sa.

Shi ma wani mai suna Shamsu Ibrahim dake unguwar Gwale ya ce suna shan wahala sosai lokacin sanyi.

Ya ce har yanzu bai canza lokacin da yake fara sana’ar sa ba , a cewarsa karfe shida yake farawa.

Ya kuma ce rashin kungiya tasa kullum masu wanki ke zama koma baya a cikin masu yin kananan sana’o’i a jihar nan.

Ya ce akwai bukatar kungiyoyi da gwamnati su rinka tallafawa masu sana’ar wanki da magunguna duba da irin halin da suke tsintar kansu a lokutan sanyi.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Hausa

Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.

Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.

Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.

Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.

Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.

“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.

“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”

Continue Reading

Hausa

Ba bu inda nace nafi Yan Najeriya shan wahalar Tsadar rayuwa, amma ina Fatan matsalar ta zamo tarihi -Dangote

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

Shugaban rikunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.

Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su .

Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote yayi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya.

“Duk abinda ya shafi yan Najeriya ya shafemu”, inji Sanarwar.

Dangote ya Kara dacewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun  da basu samu damar biya ba a baya.”

Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma tatar man fetur. A  bangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari,  gishiri da kayan dandanon girki ne kadai.

“Muma muna siyan muhimman kayan abinchi a kasuwa kamar yarda kowa ke siya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen  ciyar da al’umma.” Dangote.

 

Shugaban kamfanin yayi mamakin yadda ake neman haddasa sabani tsakanin Kamfanonin Dangote da bangaren gwamnatin tarayya, inda yace shi dan kasuwa ne ba dan siyasa ba, don haka babu inda yayi maganar kalubalantar Gwamnatin tarayya.

“Kamfaninmu ya kasance me bin dokokin kasa a koda yaushe tare da  neman sauki ga al’umma da fatan alheri.”

Saboda haka, sanarwar ta nemi Yan Nigeria su guji daudar sakon da yake ba daga kamfani yake kai tsaye ba, tare da yada  rade-radi da jita-jita.

Continue Reading

Upcoming Events

There are no upcoming events at this time.

Facebook

Twitter

Trending