Connect with us

KANUN LABARAI

Satar yaran Kano: Kotu ta bada umarnin kamo wadanda ake zargi uku da suka tsere

Published

on

Aminu Abdullahi

Babbar kotun jihar Kano dake zamanta a  sakatariyar Audu Bako ta bada umarnin  kamo mutane uku da aka bada belin su bayan an gurfanar da su gabanta bisa zargin  sata da siyar da yaran Kano a jihar Anambra suka kuma tsere.

Kano Focus ta rawaito cewa mai shari’a Dije Abdu Aboki ce ta bada umarnin yayin zaman ci gaba da shari’ar a ranar Laraba.

Mai shari’ar ta bada umarnin kamo Zainab Salisu da Umar Aliyu wadanda aka bada belinsu a baya suka kuma yi batan dabo.

An dai gurfanar da mutane goma ne dai ake zargi gaban kotun da hada baki wajen sace yara a unguwar Kawo Lambu suka kuma saiyar da su a yankin kudancin kasar nan.

Wadanda ake zargin sun hadar da Amina Ibrahim Alias (Gara) da Zainab Salisu da Yahya Salisu da kuma Umar Aliyu.

Sai Mustapha Rabi’u da Ibrahim Aliyu da Abubakar Salisu da Fatima Salisu da Tessy Chukwu Alias (Maman Emma) sai kuma Christiana Oju.

Haka zalika mai shari’a Dije Aboki ta sanya ranar ashirin da biyar ga watan da muke ciki domin cigaba da sauraron karar.

Mai shari’ar ta dage karar ne sakamakon rashin tafinta da zai fassarawa wacce ake zargi ta goma wato Christiana Oju tuhumar da akeyi mata.

Kasancewar bata fahimtar wani yare sai harshen inyamuranci wato ( Igbo), inda aka nemi masu

Christiana Oju dai itace wacce ake zargin ana kaiwa yaran a jihar Anambra tana siya.

Idan za a iya tunawa dai an fara sauraron karar ne a ranar ashirin da bakwai ga watan satumba na shekarar dubu biyu da sha bakwai a kotun majistire mai lamba a shirin da bakwai karkashin mai shari’a Salma Ahmad Danbatta kafin daga bisani a dawo da shari’a babbar kotun jiha.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending