KANUN LABARAI
Cin kayan marmarin da ba a wanke ba na haifar da ciwon hanta-masana
Zulaiha Danjuma
Masan harkar lafiya sun tabbatar da cewa cin ‘ya ‘yan itatuwa da ba awanke ba na haifar da ciwon hanta da ma wasu cutukan daban masu hadari.
A zantawar jaridar Kano Focus da wata kwararriyar likita a asibitin koyarwa na Aminu Kano Dakta Zainab Abdulkadir ta ce hadari ne mai girman gaske cin kayan itatuwan da ba a wanke ba.
Ire-iren kayan itatunwan sun hadarda kayan marmari, ganyayyaki, musamman ma wadanda aka fi sayarwa a hanya, kamar rake, dabino, magwaro, tumatiri yalo da dai sauran dangogin su.
Likitar ta ce yana daga cikin hanya mafi sauki da ake kamuwa da cutar hanta cin ‘ya ‘yan itatuwan da ba a wanke ba.

Haka zalika ta ce cin kayan marmari da ba a wanke ba na haifar da gudawa, ciwon zazzabi mai karfi, ciwon ciki mai radadi, da zawayi mamar yankewa.
Haka zalika likitan ta ce na daga hadarin cin ‘ya ‘yan itatuwan da ba a wanke ba cutar jijjiga da ka iya salwantar da ran mutum a kowanne lokaci.
Jama’a da dama basa wankewa
Wasu mutane da Kano Focus ta zanta da su sunce a mafiya yawan lokuta basa wanke kayan da suka saya kafin su faraci.
Sai dai wasu sunce sukan dan watsa ruwa sukuma murza da hannun su guda daya sannan su ci.
Bilkisu Abubakar mazauniyar Kano ce, ta ce ita dai ko ta sayi kayan marmari bata wankewa, haka ta ke afawa a bakinta.
“Ko da yake wani lokaci nakan wanke, amma maganar gaskiya bana wankewa.
“Saboda ni mantawa nake yi, saboda ba ruwa a kusa dani ma.
“Ko da yake na san zan iya kamuwa da cutuka, amma dai Allah zai kare.” A cewarta.
Wani matashi Aliyu Abdullahi ya ce yakan wanke wasu abubawan kama, amma irin su dabibo baya wankewa, a cewar sat un da aleda yake siya ba kazanta.
“Nakan wanke mangwaro saboda kwayoyin cutar da ke cikin sa da na ke tunani za su bani matsala.
Muna sayarwa ba wanki
Wani mai sana’ar sayar da rake mai suna Abba Salisu ya ce duk da kura da ake yi a halin yanzu hakan baya hana su sayar da rake, kuma ba ruwasu da wankewa.
“Muna feraye rakenmu kuma mu dauka mu zagaya, ko da yake munasa ruwa mu wanke amma da zarar mun fara kewayawa, kura na badewa, kuma hakan muke yankawa mutane.
“Gaskiyar magana bama wankewa, kuma duk wanda ya siya shi ya jowo, ko ya wanke ko kar ya wanke.” A cewarsa.
Shi ma wani mai sayar da Dabino mai suna Umar Hussain ya ce su basa sayar da dabino wankakke.
A cewarsa hakkin mai siyane idan ya siya to ya wanke abin sa kafin ya ci.
“Mafi yawan mutane basa tambayar ruwan wankewa idan sun saya, suna saye suke afawa a baka.
Shi ma wani mai sayar da Aya Anas Abubakar ya ce yana karade gari yana talla kuma baya rufe ayar ta sa.
Ya kuma ce duk wanta ya siya haka yake bashi, ba tare da wanke masaba.
A cewarsa suna yayyafa mata ruwa ne don karta bushe kuma tayi kyau, amma ba don wankewa daga kura ba.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
