Connect with us

KANUN LABARAI

‘Yan ta’adda sun tsinke kan uba, suka sassara dan sa a Kano

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Wasu ‘yan ta’adda da ba akai ga gano ko su waye ba sun datse kan wani dattijo Malam Nuhu Muhammad, suka kuma sassara dansa Nasiru Nuhu a karamar Hukumar Garko da ke nan jihar Kano.

Kano Focus ta ruwaito al’amarin da faru ne da misalin karfe biyu na daren ranar Lahadi a kauyen Tumpapi da ke karamar hukumar ta Garko.

A cewar dan uwan mamacin Muhammad Sani, sun jiyo hayaninya na tasowa ne daga gidan Malam Nuhu, da ke nuna ana bukatar akawo dauki.

Ya ce hakan ta sanya suka garzaya domin ganin me ke faruwa.

A cewarsa su na shigane kuma suka iske mai gidan tuni sun datse masa kai , yayin da shi kuma dansa suka sassara shi a kokarin san a kubutar da uban nasa.

‘Yan sanda a Kano sun kama dan sahun da ke sauke fasinja ya gudu da kayansu

KORONA: Hisbah ta fara binciken kwamandan da ake zargi da sace kayan tallafi

‘Yan sanda a Kano sun kama dan sahun da ke sauke fasinja ya gudu da kayansu

A cewar Sani dan nasa ya biyo bayan wadanda suka hallaka uban ne domin daukar fansa, hakan ce ta sanya suka juyo suka kuma sassarashi da adda.

“Ba wannan ne karon farko da yan ta’addan suka kaiwa Malam Nuhu Hari ba.

“Wata biyu da suka wuce ma sun je gidan nasa, suka kuma yi masa barazanar cewar za su kone gidansa baki daya.”

Tun da misalin karf 9:00 na safiyar litinin ne aka yi jana’azar mamatan biyu kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Da muka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ”yan sandan jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce za su bincika hakikanin al’amarin

Kiyawa mai mukamin mataimakin sufurtandan ‘yan sanda ya ce da zarar an bincika zai sanar da mu.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Hausa

Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.

Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.

Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.

Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.

Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.

“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.

“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”

Continue Reading

Hausa

Ba bu inda nace nafi Yan Najeriya shan wahalar Tsadar rayuwa, amma ina Fatan matsalar ta zamo tarihi -Dangote

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

Shugaban rikunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.

Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su .

Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote yayi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya.

“Duk abinda ya shafi yan Najeriya ya shafemu”, inji Sanarwar.

Dangote ya Kara dacewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun  da basu samu damar biya ba a baya.”

Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma tatar man fetur. A  bangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari,  gishiri da kayan dandanon girki ne kadai.

“Muma muna siyan muhimman kayan abinchi a kasuwa kamar yarda kowa ke siya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen  ciyar da al’umma.” Dangote.

 

Shugaban kamfanin yayi mamakin yadda ake neman haddasa sabani tsakanin Kamfanonin Dangote da bangaren gwamnatin tarayya, inda yace shi dan kasuwa ne ba dan siyasa ba, don haka babu inda yayi maganar kalubalantar Gwamnatin tarayya.

“Kamfaninmu ya kasance me bin dokokin kasa a koda yaushe tare da  neman sauki ga al’umma da fatan alheri.”

Saboda haka, sanarwar ta nemi Yan Nigeria su guji daudar sakon da yake ba daga kamfani yake kai tsaye ba, tare da yada  rade-radi da jita-jita.

Continue Reading

Trending