KANUN LABARAI
Zaben kananan hukumomi: Matashi ya sha fiya-fiya kan dan takara a Kano
Mukhtar Yahya Usman
Wani matashi mai suna Abubakar Umar ya yi yunkurin hallaka kansasa ta hanyar shan fiya-fiya saboda an karbe takarar shugaban cin karamar hukumar Rimin Gado daga hannun gwaninsa.
Kano Focus ta ruwaito Abubakar ya sha fiya-fiya ne a daren jiya Litinin da nufin ya huta da bakincikin da ke damunsa.
A zantawarsa da Kano Focus matashin ya ce ya zabi yin hakan ne saboda ya huce bakincikin da aka sanya masa na canza wanda suka zaba a matsayin dan takara.
Ya ce bayan da aka zo zaben fidda gwani na ‘yan takara, an zabi shugaban karamar hukumar Rimin Gado Garba Shu’aibu Rimin Gado a matsayin wanda zai sake tsayawa takara.

Ya kara da cewa gwanin nasa ya samu kuri’u 35 cikin 43 da aka kada amma aka hana shi takarar da gangan.
“Anyi zabe kuma ya samu kuri’u 35 cikin 43 da aka kada, amma wasu munafukai suka zagaye suka ziga gwamna ya kwace takarar.
“Da farko fa gwamnan ya amince da a bashi takarar amma kawai aka koma aka zugashi ya karbe ya baiwa wani.
“Kuma abin haushin ma shi ne wadanda suka yi mana wanna, su ne fa suka dinga yakar gwamnan a lokacin zaben da aka yi na baya-bayan nan.” A cewarsa.
Da yake maida bayani kan yadda al’amarin ya faru dan uwa ga Abubakar, Abdulhadi Maikudi ya ce an kirashi cikin dare ne kuma aka gaya masa ga halin da dan uwansa ke ciki.
Ya ce bayan ya je kansa ne kuma suka daukeshi zuwa babban Asibitin Rimin Gado domin bashi taimakon gaggawa.
Acewar Maikudi bayan an yi masa allurai ne kuma aka aike da su asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke nan Kano domin ci gaba da duba lafiyarsa.
Ya kara da cewa bayan bashi dukkanin taimakon da ya da ce tuni aka sallamesu suka koma gida inda yake ci gaba da murmurewa.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
