KANUN LABARAI
Zaben kananan hukumomi: Matashi ya sha fiya-fiya kan dan takara a Kano
Mukhtar Yahya Usman
Wani matashi mai suna Abubakar Umar ya yi yunkurin hallaka kansasa ta hanyar shan fiya-fiya saboda an karbe takarar shugaban cin karamar hukumar Rimin Gado daga hannun gwaninsa.
Kano Focus ta ruwaito Abubakar ya sha fiya-fiya ne a daren jiya Litinin da nufin ya huta da bakincikin da ke damunsa.
A zantawarsa da Kano Focus matashin ya ce ya zabi yin hakan ne saboda ya huce bakincikin da aka sanya masa na canza wanda suka zaba a matsayin dan takara.
Ya ce bayan da aka zo zaben fidda gwani na ‘yan takara, an zabi shugaban karamar hukumar Rimin Gado Garba Shu’aibu Rimin Gado a matsayin wanda zai sake tsayawa takara.
Ya kara da cewa gwanin nasa ya samu kuri’u 35 cikin 43 da aka kada amma aka hana shi takarar da gangan.
“Anyi zabe kuma ya samu kuri’u 35 cikin 43 da aka kada, amma wasu munafukai suka zagaye suka ziga gwamna ya kwace takarar.
“Da farko fa gwamnan ya amince da a bashi takarar amma kawai aka koma aka zugashi ya karbe ya baiwa wani.
“Kuma abin haushin ma shi ne wadanda suka yi mana wanna, su ne fa suka dinga yakar gwamnan a lokacin zaben da aka yi na baya-bayan nan.” A cewarsa.
Da yake maida bayani kan yadda al’amarin ya faru dan uwa ga Abubakar, Abdulhadi Maikudi ya ce an kirashi cikin dare ne kuma aka gaya masa ga halin da dan uwansa ke ciki.
Ya ce bayan ya je kansa ne kuma suka daukeshi zuwa babban Asibitin Rimin Gado domin bashi taimakon gaggawa.
Acewar Maikudi bayan an yi masa allurai ne kuma aka aike da su asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke nan Kano domin ci gaba da duba lafiyarsa.
Ya kara da cewa bayan bashi dukkanin taimakon da ya da ce tuni aka sallamesu suka koma gida inda yake ci gaba da murmurewa.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
Hausa
Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.
Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.
Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.
Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.
Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.
“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.
“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”
Hausa
Ba bu inda nace nafi Yan Najeriya shan wahalar Tsadar rayuwa, amma ina Fatan matsalar ta zamo tarihi -Dangote
Nasiru Yusuf Ibrahim
Shugaban rikunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.
Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su .
Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote yayi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya.
“Duk abinda ya shafi yan Najeriya ya shafemu”, inji Sanarwar.
Dangote ya Kara dacewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun da basu samu damar biya ba a baya.”
Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma tatar man fetur. A bangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari, gishiri da kayan dandanon girki ne kadai.
“Muma muna siyan muhimman kayan abinchi a kasuwa kamar yarda kowa ke siya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen ciyar da al’umma.” Dangote.
Shugaban kamfanin yayi mamakin yadda ake neman haddasa sabani tsakanin Kamfanonin Dangote da bangaren gwamnatin tarayya, inda yace shi dan kasuwa ne ba dan siyasa ba, don haka babu inda yayi maganar kalubalantar Gwamnatin tarayya.
“Kamfaninmu ya kasance me bin dokokin kasa a koda yaushe tare da neman sauki ga al’umma da fatan alheri.”
Saboda haka, sanarwar ta nemi Yan Nigeria su guji daudar sakon da yake ba daga kamfani yake kai tsaye ba, tare da yada rade-radi da jita-jita.