Connect with us

KANUN LABARAI

Ina rokon kotu ta ratayeni- dan garkuwa a Kano

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Wani matashi mai suna Anas Sa’idu da ya kashe wani matashi Tijjani Sa’idu bayan yayi garkuwa da shi ya nema da a ratayeshi.

Kano Focus ta ruwaito Anas dan shekaru 22 yayi garkuwa da Tijjani ne a kauyen Borodo hayin gwarmai da ke karamar hukumar Bebeji a nan Kano ya Kuma kashe shi tun a ranar 9 ga watan Nuwamba.

Anas dai yayi garkuwa da matashin ne kuma ya nemi kudin fansa naira miliyan daya da dubu dari uku.

A cewarsa kafin a kai ga bashi kudin fansarne kuma, ya tafi dashi gona soboda rashin inda zai tsareshi, a nan ne Kuma ya kashe shi.

“Bayan na tafi dashi gona ne sai na shake Masa wuya na kashehi.

“Bayan na kashe shi ne Kuma na haka rami na binneshi.

“Sai da na dauki kwanaki uku ni kadai Ina kokarin yadda zanyi da shi, daga bisani na haka rami na binne shi.” a cewarsa.

Da yake amsa laifinsa gaban jami’an tsaro Anas ya ce ya kashe shi ne don menan kudin fansa.

Ya Kuma ce bashi da ja akan laifin da ya aikata, a don haka yana bukatar kotu kada ta tausaya Masa, shima ta yanke Masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Ya ce ta hakan ne kawai zai kubuta daga zunubin da ya aikata a gaban Ubangiji.

Da yake jawabi ya yin da aka je tono mamacin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce sun samu rahoton aika-aikar da Anas ya aikatane, kuma nan take suka fara bincike.

Kiyawa mai mukamin mataimakin sufurtandan yan sanda ya ce tun aranar tara ga  muke watan da muke ciki ne kwamishinan yan sanda ya bada umarnin fara bincike bayan samun rahoton.

Ya ce sun dauki makwanni biyu suna gudanar da bincike har suka yi sa’ar kamo Wanda ke zargin.

Kiyawa ya ce Anas ya kashe Tijjani tsahon makwanni biyu da suka gabata ya kuma binneshi a gonarsa.

Kiyawa ya ce kawo yanzu an gama hada dukkanin bayanai, inda za su gurfanar da shi gaban kuliya domin ya girbi abinda ya shuka.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Hausa

Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.

Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.

Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.

Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.

Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.

“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.

“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”

Continue Reading

Hausa

Ba bu inda nace nafi Yan Najeriya shan wahalar Tsadar rayuwa, amma ina Fatan matsalar ta zamo tarihi -Dangote

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

Shugaban rikunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.

Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su .

Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote yayi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya.

“Duk abinda ya shafi yan Najeriya ya shafemu”, inji Sanarwar.

Dangote ya Kara dacewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun  da basu samu damar biya ba a baya.”

Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma tatar man fetur. A  bangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari,  gishiri da kayan dandanon girki ne kadai.

“Muma muna siyan muhimman kayan abinchi a kasuwa kamar yarda kowa ke siya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen  ciyar da al’umma.” Dangote.

 

Shugaban kamfanin yayi mamakin yadda ake neman haddasa sabani tsakanin Kamfanonin Dangote da bangaren gwamnatin tarayya, inda yace shi dan kasuwa ne ba dan siyasa ba, don haka babu inda yayi maganar kalubalantar Gwamnatin tarayya.

“Kamfaninmu ya kasance me bin dokokin kasa a koda yaushe tare da  neman sauki ga al’umma da fatan alheri.”

Saboda haka, sanarwar ta nemi Yan Nigeria su guji daudar sakon da yake ba daga kamfani yake kai tsaye ba, tare da yada  rade-radi da jita-jita.

Continue Reading

Trending