Connect with us

GAME DA MU

Yan sanda a Kano sun sake kana dan sahun da ke sauke fasinja ya gudu da kayansu

Published

on

Aminu Abdulahi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sake cafke direban adai-data sahu da ya kware wajen guduwa da kayayyakin fasinjoji ya yin da yake tuki.

Kano Focus ta ruwaito cewa an sake cafke direban adai-daita sahun ne mai shekaru 39 bayan da ya sake yin batan dabo da kayan wasu mata na kimanin naira dubu dari hudu a bakin barikin Bokabo.

Direban adai-daita sahun mai suna Muhammad Ahmad Muhammad Kabuga ya ce wannanne karo na biyu da aka sake kama shi da aikata irin wannan laifi.

Ya ce kaddarace ta sa shi yake aikata irin wannan muguwar dabi’a kuma yana fatan Allah ya shirye shi.

A nasa bangaren mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce sati biyu da suka gabata suka kama wanda ake zargin tare da gurfanar dashi a gaban kotu.

Kiyawa mai mukamin mataimakin sufurtandan ‘yan sanda ya ce kotu ta yanke masa hukuncin shekara biyu ko kuma biyan tarar naira dubu arba’in wanda kuma ya biya tarar nan take.

Saidai bayan da ya fito ne kuma sai ya sake yin awon gaba da kayayyakin wasu mata su biyar.

Kiyawa ya kuma ce wanda ake zargin ya tabbatarwa da rundunar cewa ya aikata duk kan lefukan da ake tuhumar sa da shi.

Ya kara da cewa bayan da suka ci gaba da bincike ne kuma sai suka same shi da jabun kudi kimanin naira dubu hamsin.

Ya kuma tabbatar da cewa yana siyan rafa daya a gurin wasu mutane akan naira dubu goma sha biyar kana daga bisani kuma ya shiga dasu cikin kasuwa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending