KANUN LABARAI
Ina hada baki ne da ‘yan unguwa su gayamin wanda ke da kayan da za a sata-Barawo
Aminu Abdullahi
Jami’an vigilante na unguwar Ja’o’ji a karamar Hukumar Kumbotso sun kama wani matashi da ake zargin ya kware wajen sace-sace a yankin.
Kano Focus ta ruwaito cewa barawon mai suna Abdul’alim Sani mazaunin unguwar Sheka ‘yar Kasuwa ya shiga hannun ‘yan sintirin ne bayan da ya haura wani gida a unguwar Ja’oji da karfe uku na daren ranar Talata.
Ya yin zantawar sa da jaridar Kano Focus wanda ake zargin Abdul’alim Sani yace an kamashi ne ya yin da ya haura wani gida da tsakar dare inda ya kwashe musu wayoyi guda biyu da na’ura mai kwakwalwa.
Ya ce akwai abokanansa da suke ba shi bayanai na wadanda suke da mashin ko suka siyi sabuwar waya a unguwar wanda dasu ne yake gudanar da muguwar dabi’ar tashi.

“ Eh muna amfani da mukullin dake bude kowane abu kuma sunayen abokanan nawa akwai Hassan Kabila Da Tunbur da kuma Yazid Dadi kuma duk ‘yan nan unguwar ne.
“Kuma idan na sato wayoyin ina siyarwa da wani abokina ne mai suna Tamilo,” a cewar sa.
Ya kara da cewa ya siyar da kwmafutar da ya sato a kan kudi naira dubu goma ga wani mai suna Abba Bari.
A nasa bangaren daya daga cikin wadanda barawon ya haurawa gida mai suna Alhaji Habibu Muhammad ya ce ya yi matukar farin ciki da ‘yan sinturin suka kama barawon.
Ya ce ba wannan ne karon farko da barawon yake yi masu sata ba dan kuwa ko akwanakin baya ma sai da ya haura ya dauke musu wayoyi da kayayyaki masu muhimmanci.
Sakataren kungiyar ‘yan sintiri ta unguwar Ja’oji Malam Musa Isah Murtala ya ce sun samu kira ne daga wani Alhaji Habibu Muhammad da karfe uku na dare inda ya shaida musu cewa wanda ake zargin ya haura masa gida.
Ya ce nan take suka garzaya gidan inda kuma sukayiwa barawon kofar rago tare da kamashi dumu-dumu da kayan da ya sata.
Ya kara da cewa barawon ya dade yana addabar unguwar ta Ja’oji kuma zasu miki shi zuga Hukumar yan sanda don girbar abinda ya aikata.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
