KANUN LABARAI
Matsalar tsaro: ‘Yan wasan Hausa a Kano na caccakar shugaba Buhari
Aminu Abdullahi
Jarumai da mawaka a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood a nan Kano na cigaba da nuna alhinin su bisa matsalar tsaro da arewacin kasar nan ke fuskanta.
Kano Focus ta bibiyi jaruman ta shafukan su na sada zumunta inda ta tattaro wasu daga cikin ra’ayoyin jaruman kan yadda matsalar tsaro ke cigaba da tagayyara kasar nan.
Mawaki kuma jarumi a masana’antar Ado Isah Gwanja ya ce sakaci da rashin iya jagoranci na shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne ummul aba’isin rashin tsaron da arewacin kasar nan ke fuskanta.
Ya ce kamata ya yi shugaban ya yi garanbawul a kunshin mutanen dake gwamnatinsa musamman wadanda ke bangaren tsaro.

“Har yanzu lokaci bai kure masa ba da ya kamata ya gyara tun kafin a zo ayi faduwar guzuma.
“Kada ya manta mu da shi muka zauna a fadar sa ya fada mana cewa wannan zango na biyun zai mai da hankali ne ga arewacin kasar nan amma sai gashi ya banzatar da mu a gefe,” a cewar Gwanja.
Korar Rahama Sadau ba zai tsarkake ‘yan fim ba-Jaruma Farida Jalal
Yanzu-yanzu: Kungiyar musu shirya-fina-finan Hausa a Kano ta kori Rahama Sadau
Hukumar ta ce fina-finai ta Kano ta fara tantance sha’irai
Shi ma mashiryin fina-finai Falalu A Dorayi cewa ya yi akwai tsananin tashin hankali ace kullum da an farka daga bacci sai anci karo da labarin kashewa da sacewa da kuma kone garuruwa a arewacin kasar nan.
“Rayukan Al’umma sun zama kamar ran kiyashi, su kuma wadanda Alhakin kula da rayukan da dukiyar jama’a yake hannunsu sun zama magen Lami.
“Abin bacin rai in dai ta tasu zamu jira domin suyi wani abu to sai dai mu mutu da takaici,” inji Falalu
Ya kara da cewa a sannu a hankali dai sha’anin tsaro na cigaba da ruguza duk wani tattalin arziki na arewa.
“Mutanen da suke safara an bi hanyar su an tare, ba iya kudin hannunsu ake karba ba, su din ake daukewa sukutum a nemi su kawo abin da suka tara a gida.
‘Yan wasan Hausa a Kano sun yi tofin alatsine ga shugaban Faransa
Dalibai su koma hadiman masallatai da coco-coci maimakon jiran gawon shanu-ASUU
Baku da inuwar da za ku tsaya takara ne- Martanin gwamnatin Kano ga Kwankwasiyya
Shi kuwa jarumi Ali Nuhu cewa yayi lokaci yayi da gwamnoni za su wanke kansu a wajan al’ummar da suke mulka.
Idan har domin jama’a suke yi to ya zama wajibi suyi magana ko kuma su dauki mataki mafi tsauri akan rashin tsaro a kasar nan.
Ya ce har yanzu talakawa na ganin sarakunan gargajiya a matsayin iyayensu, kuma suna da daraja mafi girma a idanun su fiye da yan siyasa.
Saidai ya ce da yawan sarakunan suna tsoron su rasa kujerun su ne fiye da ubangiji.
Ya ce ya kamata su tabbatarwa da talakawa suna tare dasu da kuma kare mutuncinsu.
Ya kuma ce Sanatoci da ‘yan majalissar wakilai sun manta cewa talakawa ne suka kaisu matsayin da suke kai a yanzu.
Ya ce lallai idan basu tashi tsaye ba akan kashe-kashen da akeyi a arewacin kasar la shakka suma tun a duniya ba za su ga dai dai ba balle kuma a lahira.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
