KANUN LABARAI
Kotu ta yankewa barawon dan sahu hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari
Aminu Abdullahi
Kotun magistrate dake zamanta a unguwar mariri ta yankewa direban adai-daita sahu da ya kware wajen guduwa da kayan fasinjoji da kuma mu’amila da kudaden jebu hukuncin shekaru bakwai a gidan gyaran hali.
Kano Focus ta rawaito cewa an gurfanar da direban adai-daita sahun Muhammad Ahmad Muhammad agaban kotun karkashin mai shari’a Salisu Idris Salama.
Yayin zaman kotun na ranar Laraba an karantowa wanda ake zargi tuhuma ta farko da ake zargin sa da amfani da kudin jabu wanda ya saba da sashe na 319 na kundin pinal kod inda nan take ya amsa laifin.
Hakan tasa mai shari’a ya yanke masa hukuncin shekaru hudu babu zabin tara akan laifin samunsa da amfani da kudin jabu.
An kuma sake karanto masa tuhuma ta biyu na zargin satar kayan masarufi anan ma ya amsa laifin nasa, nan ma mai shari’a ya yanke masa hukuncin shekara daya babu biyan tara.
Haka kuma ance ya biya naira dubu talatin da shida ko yin watanni tara a gidan gyaran hali.
Haka zalika an sake karanto masa tuhuma ta uku ta satar baburin adai-daita sahu inda nan ma ya amsa laifinsa shi ma mai shari’a yayen ke masa hukuncin shekaru biyu ko biyan tara na N70,000 sakamakon bai salwantar da baburin da ya sata ba.
Da yake jawabi Muhammad Ahmad ya ce yana rokon al’umma da suyi masa addu’a Allah yasa ya fita lafiya daga gidan gyaran hali.
Ya ce ya yi nadama matuka domin kuwa yana da ‘ya’ya guda hudu da wadanda yake riko gashi kuma duk zai tafi gidan gyaran hali ya barsu.
Hausa
Mutane 18,000 sun amfana da aikin ido kyauta ta Gidauniyar Mangal a Katsina
Kimanin marasa lafiya masu rauni 18,000 da ke fama da cututtukan ido daban-daban a jihar Katsina sun amfana da ayyukan kulawar ido da tiyata kyauta da Gidauniyar Mangal ta dauki nauyi tun bayan kafuwarta a shekarar 2016.
Wani mamba na kwamitin amintattu (Board of Trustees) na gidauniyar, Malam Hussaini Kabir, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin kaddamar da aikin tiyatar ido na zangon karshe na shekarar 2025 a Cibiyar Ido ta Katsina.
Kabir ya bayyana cewa kimanin mutane 7,000 ne suka amfana a shekarar 2025 kadai, daga sassan jihar Katsina, jihohin makwabta, har ma da wasu yankuna na Jamhuriyar Nijar.

A cewarsa, gidauniyar ta fara tantance wadanda za su amfana kimanin makonni biyu da suka gabata, inda marasa lafiya da dama suka samu magunguna kyauta da tabarau na likita.
Kabir ya kara da cewa wadanda ke bukatar tiyata an dauki nauyin dukkan zaman asibitinsu gaba daya, yana mai cewa kimanin marasa lafiya 2,000 aka tantance a yayin aikin zangon karshe da ake ci gaba da yi.

Ya sake jaddada kudirin gidauniyar na inganta samun kulawar lafiya, yana bayyana shirin a matsayin wani bangare na nauyin alhakin zamantakewar kamfanoni (corporate social responsibility).
“Manufarmu ita ce tallafa wa kokarin gwamnati tare da rage nauyin kudin kula da lafiya ga mafi rauni, musamman wadanda ke fama da matsalar biyan bukatun rayuwa,” in ji shi.

Wani likitan ido a cibiyar, Dokta Ahmad Hamza, ya bayyana cewa an gano marasa lafiya da dama na fama da cutar idon toka (cataract) da glaucoma, cututtuka da galibi ke bukatar tiyata.
Ya jaddada muhimmancin duba ido akai-akai, yana mai cewa gano cuta da wuri na taimakawa wajen hana asarar gani ta dindindin da cututtukan ido masu zuwa a boye ke haifarwa, kamar glaucoma, cataract da lalacewar macula (macular degeneration).

Daya daga cikin wadanda suka amfana, Malam Yusufa Usman, ya ce ya shafe sama da shekaru biyu yana fama da matsalar gani amma ba shi da ikon biyan kudin tiyata.
“Tsawon shekaru biyu ban iya gani sosai ba, amma yau na yi tiyata kuma ina da fatan ganina zai dawo.
Ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya saka wa Gidauniyar Mangal da alheri bisa wannan kyakkyawan aiki.
“Ina fatan sauran masu kudi za su yi koyi da wannan abin a yaba,” in ji Usman.

Wata mai amfana, Aisha Muntari daga kauyen Bakuru, ta bayyana kwarewarta yayin da take jiran a kai ta dakin tiyata.
Muntari ta ce ta kamu da matsalar ido kimanin shekara guda da ta wuce kuma ta kusa yanke tsammani kafin ta samu labarin shigar gidauniyar, tana mai bayyana kwarin gwiwar cewa nan ba da dadewa ba ganinta zai dawo.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
