Connect with us

KANUN LABARAI

Dokar sabunta kudaden haya a Kasuwar Sabo Gari karya kasuwancin Kano ne- Alin Bagadaza

Published

on

Mukhhtar Yahya Usman

‘Yan kasuwar Muhammad Abubakar Rimi da ke (Sabon Gari) sun nemi majalisar dokokin jihar Kano da tayi duba na tsanaki kan dokar sabunta kudaden shagunansu da aka kai gabanata.

Kano Focus ta ruwaito ‘yan kasuwar  sunyi wannan roko ne ya yin da suka kai ziyara majalisar dokokin ranar Talata.

Da yake jawabi a madadin ‘yan kasuwar, shugaban kungiyar Alhaji Alin Bagadaza ya ce dabbaka dokar dai-dai yake da kassara kasuwanci da ‘yan kasuwar.

Idan za a iya tunawa dai a bayane gwamnatin jihar Kano ta aike da wata doka zauren majalisar dokokin jihar Kano da ta nemi ‘yan kasuwar da su sake biyan kudaden shagunan su akan naira miliyan daya.

Tun bayan da gobara ta tashi a kasuwar, aka yi asarar dukiya mai dimbin yawa da kuma shaguna.

Hakan ta sanya ‘yan kasuwar suka gyara shagunan nasu da kudaden aljihunsu, sai dai gwamnati ta nemi da su biya naira miliya daya kan kowanne shago bayan sun gyara.

Ko al’umma a Kano za su rungumi sabon tsarin zabe ta internet

Zanga-zanga: Al’ummar Igbo sun nemi afuwar jama’ar Kano

EFCC ta cafke tsohon shugaban kasuwar Kofar Wambai a harabar kotu

Sai dai Alin Bagadaza ya ce hakika dabbaka wannan doka za ta kawo koma baya a harkokin ‘yan kasuwa da dama.

Ya kuma bayyana rashin gamsuwarsa akan jagorancin shugaban kasuwar Alh. Uba Zubairu Yakasai.

Ya ce zuwansa a matsayin shugaba a kasuwar ya haifar da lalacewar harkokin kasuwancinsu.

Da yake nasa jawabin shugaban majalisar  Abdul’azeez Garba Gafasa ya ce majalisar za ta tuntubi dukkanin wadanda dokar ta shafa domin tabbatar da ganin an yiwa kowanne bangare adalci.

Gafasa ya ce  majalisar za ta yi duk wani kokari da zai samar da zaman lafiya da bunkasa harkokin ‘yan kasuwar.

Ya kuma nuna gamsuwarsa bisa nuna halin da’a da bin matakin da ya dace wajen shigar da koken na su.

Ya kuma  ba su tabbacin cewa majalisar za ta yi kokarin ganin  dokar ta zama masalaha ga ‘yan kasuwar kafin su amince da ita.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending