KANUN LABARAI
Rufe makarantu: Zanga-zanga ta barke a manyan makarantun Kano
Aminu Abdullahi
Zanga-zanga ta barke a kwalejin ilimi ta Sa’adu Rimi da kuma kwalejin koyar al’amuran addinin musulunci ta Aminu Kano wato LEGAL da kuma kwalejin fasaha ta jihar Kano (polytechnic) sakamakon rufe makarantun da gwamnati tayi.
Kano Focus ta ruwaito a daren jiya ne gwamnatin Kano ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun da ke jihar nan, lamarin da ya harzuka daliban.
Ko da ya ke har yanzu ba a kai ga sanin dalilin da ya sanya gwamnatin rufe makarantun ba, rahotanni na cewa hakan na da nasaba da sace daliban makarantar Kankara da ke jihar Katsina.
Dubban dalibai ne dai suka yi cirko-ciroko a bakin makarantun nasu suna ala wadai da matakin rufewar da gwamnati ta dauka, da ga bisani kuma alhinin nasu ya rikide zuwa zanga-zanga.
A zagayen da Kano Focus ta yi ta iske makarantun a kulle ya yin da kuma dalibai suka yi cirko cirko a bakin Kofar makarantun nasu.
An kuma hangosu suna raira wakoki na nuna rashin jin dadinsu kan matakin rufe makarantun da gwamnati tayi.
Mubaraq Muhammad dake karatu a kwalejin ilimi ta Aminu Kano (Legal) ya ce ya yi matukar kaduwa da ya samu labarin cewa gwamnati ta bada umarnin sake rufe makarantu.
“Wancan hutun da muka sha ya mai dani baya yanzu kuma an sake kulewa gashi mun kusa fara jarabawa.
“Ilimi kullum koma baya ake samu a kasar nan, kuma matukar aka ci gaba da tafiya a haka, toni karatun ma denawa zanyi,” a cewar sa.
Aisha Sani Abdulkadir daliba ce da aka iske suna zaman alhini a bakin kwalejin, ta ce sai bayan da ta zo kofar makarantar ne sannan ta fahimci cewa an rufe makarantu sakamakon hana ta shiga da akayi.
Ta ce duk da an hanasu shiga makarantar sai kuma aka sa jami’an ‘yan sanda suka rinka korar su wanda hakan tamkar cin zarafi ne.
“Kaga wadan da za suyi shekara uku yanzu sai sun shekara hudu, masu shekara biyu kuma yanzu sai sun shekara uku, karatun mu yana ta tambal tambal,” a cewar ta
Ta kara da cewa dalibai suna cikin wani hali wanda zaman gida ke kara musu damuwa sosai.
Salma Muhammad cewa tayi rufe makarantun ya sa tillas su Dakata da rubuta jarabawa da sukeyi.
Ta ce a ranar Juma’a mai zuwa ne suke sa ran kammala jarabawar su sai gashi an fitar da wannan sanarwa.
Shi ma Abubakar Tahir dalibi a kwlejin LEGAL cewa ya yi amfada musu cewa sace yara da akayi a jihar Katsina ne yasa aka rufe musu makarantu.
Ya kara da cewa ba sunayin zanga-anga don tada fitina bane, sai don su nuna rashin goyon bayan su kan matakin da gwamnatin ta dauka.
Ya ce ko ya zauna a gida ma bashi da abinyi ko wata sana’a da za ta debe mishi kewa.
Ya kuma ce rashin sanin aikin shugabanin kasar nan ya sa suka gaza baiwa dalibai tsaro da al’ummar kasa wanda hakan yasa ake sace su.
Abubakar Muhammad dalibi a kwalejin fasaha ta jihar Kano cewa ya yi sun zo ne da zummar yin karatu sai aka hana su shiga.
Wasunmu sabbin dalibai ne wasu kuma sun ma fara jarabawa kuma ba a wani jima da dawowa daga zaman gida na korona ba.
“Ba wani dalili da aka fada mana kawai haka aka ce mu fito a rufe kuma ba a fada mana lokacin da za a dawo ba.
“Dole ne muyi zanga zanga don ancuce mu ba kadan ba, domin ni yanzu banma san ranar da zan gama makarantaba, kuma inaso nayi aure,” a cewar sa.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.