KANUN LABARAI
Masu satar bayanai ne ke samar da ‘link’ din dake bukatar a hada lambar NIN da ta layin waya-NIMC
Aminu Abdullahi
Hukumar samar da katin dan kasa NIMC ta yi kira ga al’umma da su kauracewa sanya lambarsu ta katin shaidar dan kasa a shafukan internet da ke yawo a kafafen sada zumunta da nufin hada ta da lambar wayarsu.
Kano Focus ta ruwaito cewa daraktan hukumar shiyyar Kano Lawan Yahya ne ya bayyana haka ya yin zantawarsa da manema labarai a ranar Alhamis.
Lawan Yahya ya ce akwai ‘yan damfara dake fitowa da sabbin hanyoyi a shafukan sada zumunta da suke daukar bayanan al’umma tare da damfararsu.
Ya ce bai kamata al’umma su rinka amfani da duk wata sanarwa da suka gani ba, ba tare da tabbatar da ingancin ta ba.
“Idan sunga irin wannan sanarwa kamata ya yi suje kamfanin kai tsaye ko su kira lambobin wayar kamfanin dan tabbatarwa.
“A kwai mutanen da zasu iya yin amfani da bayanin mutum don su cutar dashi,” a cewar sa.
Lawan Yahya ya ce wadanda sukayi rijistar katin dan kasa daga shekara ta 2003 aka basu kati ya zama wajibi su sake sabunta rijistar tasu.
Ya kara da cewa katin da aka basu a wancan shekarun baya dauke da lambar dan kasa wato (NIN).
Ya kuma ce duk wanda bai yi rijista daga lokacin da hukumar ta sake sabun ta yin rijistar ba, wato daga shekara ta 2012 zuwa yanzu kuma bashi da takardar da hukumar ke bayarwa, to bashi da katin shedar dan kasa.
“NIN lamba dake jikin takardar da aka bawa mutum itace mafi muhimmanci.
“Kuma ba a karbar ko sisi da sunan yin rigista, don haka duk wanda a ka nemi wani abu a hannun sa ya kawo mana korafi kai tsaye ofishin mu zamu dauki mataki.
“Akwai wadanda a yanzu haka muna kotu dasu sakamakon damfarar mutane da sukayi da sunan hukumar samar da katin dan Kasa,” a cewar sa.
Sai dai ya ce ga wanda takardar sa ta shaidar dan kasa ta bata ko ta lalace to zai biya N500 kafin a sake masa wata, sanann a banki zai je ya biya ba a Hukumar ba.
Ya ce ga wanda ya biya, shaidar biyan kawai zai kai musu ofishinsu don a fitar masa da wata takardar.
Haka kuma ya ce ga wanda zai canza suna ko karawa ko kuma ragewa shima N500 zai biya a banki, sannan ya kai musu takardar biyan domin canza masa.
Sai dai ya ce ga wadanda za su gyara shekarun su na haihuwa, za su biya N15,000 ne kafin a gyara musu.
“Koda mutum ya biya kudin dole ne sai ya gabatar mana da wata shaida, wacce za ta tabbatar da cewa suna bukatar canza shekarun nasu,” a cewar sa.
Lawan Yahya ya kara da cewa daga sanda aka fara rijistar katin dan kasa zuwa yanzu kasa da mutum miliyan uku ne kawai sukayi rijista a jihar Kano duk kuwa da cewa jihar na da al’umma fiye da miliyan goma sha biyar.
Ya ce hukumar ta hada kai da wasu kamfanoni sama da dari biyu da za su shiga lungu da sako da kauyuka domin yiwa al’umma rijista.
Ya kuma ce za a sanarwa dagatai da masu unguwanni rana da wadanda za su je suyiwa mutane rijista don gudun ‘yan damfara.
Hausa
Mutane 18,000 sun amfana da aikin ido kyauta ta Gidauniyar Mangal a Katsina
Kimanin marasa lafiya masu rauni 18,000 da ke fama da cututtukan ido daban-daban a jihar Katsina sun amfana da ayyukan kulawar ido da tiyata kyauta da Gidauniyar Mangal ta dauki nauyi tun bayan kafuwarta a shekarar 2016.
Wani mamba na kwamitin amintattu (Board of Trustees) na gidauniyar, Malam Hussaini Kabir, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin kaddamar da aikin tiyatar ido na zangon karshe na shekarar 2025 a Cibiyar Ido ta Katsina.
Kabir ya bayyana cewa kimanin mutane 7,000 ne suka amfana a shekarar 2025 kadai, daga sassan jihar Katsina, jihohin makwabta, har ma da wasu yankuna na Jamhuriyar Nijar.

A cewarsa, gidauniyar ta fara tantance wadanda za su amfana kimanin makonni biyu da suka gabata, inda marasa lafiya da dama suka samu magunguna kyauta da tabarau na likita.
Kabir ya kara da cewa wadanda ke bukatar tiyata an dauki nauyin dukkan zaman asibitinsu gaba daya, yana mai cewa kimanin marasa lafiya 2,000 aka tantance a yayin aikin zangon karshe da ake ci gaba da yi.

Ya sake jaddada kudirin gidauniyar na inganta samun kulawar lafiya, yana bayyana shirin a matsayin wani bangare na nauyin alhakin zamantakewar kamfanoni (corporate social responsibility).
“Manufarmu ita ce tallafa wa kokarin gwamnati tare da rage nauyin kudin kula da lafiya ga mafi rauni, musamman wadanda ke fama da matsalar biyan bukatun rayuwa,” in ji shi.

Wani likitan ido a cibiyar, Dokta Ahmad Hamza, ya bayyana cewa an gano marasa lafiya da dama na fama da cutar idon toka (cataract) da glaucoma, cututtuka da galibi ke bukatar tiyata.
Ya jaddada muhimmancin duba ido akai-akai, yana mai cewa gano cuta da wuri na taimakawa wajen hana asarar gani ta dindindin da cututtukan ido masu zuwa a boye ke haifarwa, kamar glaucoma, cataract da lalacewar macula (macular degeneration).

Daya daga cikin wadanda suka amfana, Malam Yusufa Usman, ya ce ya shafe sama da shekaru biyu yana fama da matsalar gani amma ba shi da ikon biyan kudin tiyata.
“Tsawon shekaru biyu ban iya gani sosai ba, amma yau na yi tiyata kuma ina da fatan ganina zai dawo.
Ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya saka wa Gidauniyar Mangal da alheri bisa wannan kyakkyawan aiki.
“Ina fatan sauran masu kudi za su yi koyi da wannan abin a yaba,” in ji Usman.

Wata mai amfana, Aisha Muntari daga kauyen Bakuru, ta bayyana kwarewarta yayin da take jiran a kai ta dakin tiyata.
Muntari ta ce ta kamu da matsalar ido kimanin shekara guda da ta wuce kuma ta kusa yanke tsammani kafin ta samu labarin shigar gidauniyar, tana mai bayyana kwarin gwiwar cewa nan ba da dadewa ba ganinta zai dawo.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
