Connect with us

KANUN LABARAI

Shekara guda a kwamishinan ‘yan sanda, na bunkasa al’amuran tsaro a Kano-Habu Sani

Published

on

Aminu Abdullahi

Rundunar ‘yan sanda jihar Kano ta ce tana aiki kafa da kafa da sauran al’umma domin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma jihar nan.

Kano Focus ta ruwaito cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Habu A Sani ne ya bayyana haka ya yin taron bayyana nasarorin da hukumar ta samu a shekara daya tun bayan zamansa kwamishinan ‘yan sanda a jihar Kano.

Habu Sani ya ce akwai mutane daban-daban dake taimakawa rundunar ta bangarori masu yawa, da hakan yasa ta shirya taron don karrama su.

Ya kuma ce akwai mutanen da suka siyawa rundunar motoci da gyara musu ofisoshi da gina sabbi, duk don tabbatar da tsaro.

Kwamishinan ya kara da cewa rundunar a jihar Kano ta karfafa ayyukan ‘yan sandan cikin al’umma da kuma sashen Operation Puff Ada dake yaki da miyagun laifuka a cikin al’umma.

“Bayan da nazo Kano na tsara yadda zan gudanar da ayyukana da karfafa bangaren sada zumunta na yanar gizo don isar da sakonni ga al’umma.

“Mun kuma koyar da matasa ayyukan dogaro da kai don magance matsalar zaman banza da shaye-shaye da kuma miyagun ayyuka,” a cewar sa.

A nasa bangaren dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada da Doguwa Alhassan Ado Doguwa ya baiwa rundunar gudunmawar naira miliyan goma yayin taron.

Doguwa ya ce majalisun dokokin tarayya na aiki don gyara dokar da ta kafa hukumar ‘yan sanda, duba da abubuwan da suka faru na zanga zangar Endsars a kasar nan.

Ya kara da cewa suna yin nazari don bunkasa asusun tallafawa ‘yan sanda da majalisa tayi doka akai.

Ya kuma bukaci al’umma da su rinka baiwa rundunar ‘yan sanda hadin kai don tabbatar da tsaro a cikin al’umma.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending