Connect with us

KANUN LABARAI

Shekara guda a kwamishinan ‘yan sanda, na bunkasa al’amuran tsaro a Kano-Habu Sani

Published

on

Aminu Abdullahi

Rundunar ‘yan sanda jihar Kano ta ce tana aiki kafa da kafa da sauran al’umma domin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma jihar nan.

Kano Focus ta ruwaito cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Habu A Sani ne ya bayyana haka ya yin taron bayyana nasarorin da hukumar ta samu a shekara daya tun bayan zamansa kwamishinan ‘yan sanda a jihar Kano.

Habu Sani ya ce akwai mutane daban-daban dake taimakawa rundunar ta bangarori masu yawa, da hakan yasa ta shirya taron don karrama su.

Ya kuma ce akwai mutanen da suka siyawa rundunar motoci da gyara musu ofisoshi da gina sabbi, duk don tabbatar da tsaro.

Kwamishinan ya kara da cewa rundunar a jihar Kano ta karfafa ayyukan ‘yan sandan cikin al’umma da kuma sashen Operation Puff Ada dake yaki da miyagun laifuka a cikin al’umma.

“Bayan da nazo Kano na tsara yadda zan gudanar da ayyukana da karfafa bangaren sada zumunta na yanar gizo don isar da sakonni ga al’umma.

“Mun kuma koyar da matasa ayyukan dogaro da kai don magance matsalar zaman banza da shaye-shaye da kuma miyagun ayyuka,” a cewar sa.

A nasa bangaren dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada da Doguwa Alhassan Ado Doguwa ya baiwa rundunar gudunmawar naira miliyan goma yayin taron.

Doguwa ya ce majalisun dokokin tarayya na aiki don gyara dokar da ta kafa hukumar ‘yan sanda, duba da abubuwan da suka faru na zanga zangar Endsars a kasar nan.

Ya kara da cewa suna yin nazari don bunkasa asusun tallafawa ‘yan sanda da majalisa tayi doka akai.

Ya kuma bukaci al’umma da su rinka baiwa rundunar ‘yan sanda hadin kai don tabbatar da tsaro a cikin al’umma.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Hausa

An kirkiro maganin kayyade iyali na maza

Published

on

Nasiru Yusuf

Tun daga shekarun 1960, lokacin da kwayoyin kayyade iyali na mata suka shiga kasuwa, masana kimiyya suke ta fadi-tashin ganin sun samar da wasu kwayoyin magani da maza za su rika sha domin hana daukar ciki.

Wata tawagar masana kimiyya ta sanar da sarrafa kwayar magani ta kayyade iyali da maza za su rika sha.

Masanan daga jami’ar Minnesota ta Amirka sun ce gwajin kwayar maganin hana daukar ciki na maza ya nuna gagarumin tasiri na kashi 99 cikin 100 ga namijin bera.

A cikin sanarwar da masu binciken suka fitar a ranar Laraba sun ce zuwa karshen wannan shekarar ta 2022 suke sa ran fara gwajin kwayar maganin ga dan Adam. Matakin da masu fafutukar daidaita jinsi suka jima suna maraba da shi.

Continue Reading

Hausa

Pantami ya ziyarci iyayen Hanifa Abubakar

Published

on

Nasiru Yusuf

Ministan Sadarwa Farfesa Isa Ali Pantami ya kai ziyarar ta’aziyya gidan su Hanifa Abubakar, yarinya ‘yar shekara biyar waddaa aka kama shugaban makarantarsu da laifin yi mata kisan gilla.

KANO FOCUS ta ruwaito cewa Pantami ya yi ta’aziyya ga mahaifin yarinya, Malam Abubakar, inda daga bisani mahaifin yarinyar ya jagoranci Minista shiga  cikin gida don yi wa mahaifiyar Hanifa da yan’uwanta ta’aziyya da nasihohi.

Malam Pantami ya yi nasiha ga iyayen Hanifa akan wajibcin hakuri lokacin jarrabawa mai tsanani irin wannan.

Farfesa Pantami, ya roki Allah Ya sanya marigayiya Hanifa Abubakar ta zama mai ceto a lahira ga iyayenta, ya kuma bawa iyayen hakuri akan wannan babban rashi da ya faru sanadiyar wasu azzalumai da suka nuna rashin imani.

Iyayen marigayiya Hanifa Abubakar sun godewa Malam da adduar fatan alheri akan nasihohi da addu’o’i da ya gabatar.

Continue Reading

Hausa

Abun da yakamata a sani game da ‘Tofa Cup’

Published

on

Jamilu Uba Adamu

Jamilu Uba Adamu 

Tarihi abune mai muhimmancin gaske, musamman na abun da yashafi wasanni.

Amma mu anan Nahiyar ta Afrika, musamman a arewacin Najeriya ba a dauki tarihi da muhimmanci ba.

Shi tarihi na wasanni, yakan taimakawa ma su sha’awar sa sanin abun da ya faru a baya, dama wadanda suka ba da gudummawa, har aka kawo yanzu don kara shirin yadda za a tunkari gaba.

Don haka ne, a wannan dan shafin wasanni zan  kawo tarihin gasar cin kofin Kwallon k’afa na Tofa. Wanda ake bugawa a Jihar Kano.

Wannan gasar cin kofi mai tarihi, wanda yanzu haka shine kofi mafi daraja a rukunin kofuna da ake bugawa a duk gasannin kofuna da hukumar Kwallon kafa ta kano take sakawa.

Itadai wannan gasar Kofi mai dinbin tarihi a harkar wasan kwallon k’afa a wannan Jiha ta Kano ta samu asali ne a tun shekarar 1979, a lokacin ana kiranta Danwawu Cup.

Alhaji Dan wawu (Ya taba rike matsayin mai kula da harkar wasanni na Arewa, a zamanin firamiyan Jihar Arewa na farko Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto). A wancan zamanin shi ne wanda yake daukar nauyin gasar, wacce aka fara da Kulub guda Takwas ( 8 ), wanda suka hada da; Zumunta dake Unguwar Fagge da Super Star (Goro Dutse) da Sanka Vipers (Unguwar Sanka) da Kofar Mata da Kofar Wanbai da Yakasai Rovers da Y.B.C Kano da Golden Star da kuma Gwagwarwa Yaks.

Sune kulubluka na farko da suka fara bugawa a shekarar da aka fara wannan gasa mai tarihi.

A shekarar 1985  gasar ta koma Tofa Cup, bisa daukar nauyin gasar da Alhaji Isyaku Umar Tofa ( Makaman Bichi ) ya yi, bayan rasuwar Margayi Alhaji Danwawu Fagge.

Daga baya a shekarar 1999, aka canzawa gasar tsari da kuma fasali, inda ta koma TOFA Firimiya Lig.

Wannan gasar kofi mai tarihi ta taimaka kwarai da gaske wajen bawa matasan yan kwallon kafa, damar gogewa da kwarewa har zuwa babban mataki na k’asa.

Yanzu haka a wannan shekara da muke ciki ta Dubu biyu da Ashirin da daya, akwai kulubluka sama da ashirin da biyar dake fafatawa a wannan gasa mai tarihi a kwallon kafa a jihar Kano.

Jamilu Uba Adamu,

Mai sharhin kwallon k’afa ne.

jameelubaadamu@yahoo.com

Continue Reading

Trending