KANUN LABARAI
Jami’an Vigilante a Kano sun kama barawon baburin Opay na zuwa burge ‘yan mata
Aminu Abdullahi
Jami’an Vigilante da ke unguwar Sharada sun kama matashin da ya gudu da baburin haya na Opay da ake zuwa burge yan mata da shi.
Kano Focus ta ruwaito matashin mai suna Muhammad Muhammad mazaunin unguwar Ja’en da ke karamar hukmar Gwale a nan Kano an kamashi ne bayan da ya bace da baburin tsahon kwanaki 24.
Jami’an sun kamashi a ranar litinin bayan da ya hayi baburin domin zuwa zance wurin budurwarsa, sai dai ya ki mayar da baburin kamar yadda aka yi rila’a da shi.
Muhammad ya ce wannan ne karon farko da ya taba karbar hayar baburin kuma tsautsayine yasa ya gudu dashi.

“Na je zance, daga nan ne kuma sai na gudu da baburin, gaskiya ba siyarwa nayi ba, kawai na cigaba da hawansa ne a matsayin nawa, kuma yanzu nayi nadama sosai bisa abinda na aikata,” a cewar sa.
A nasa bangaren mai bada hayar baburan Gaddafi Lawan ya ce ya karbi baburin nasa ne kirar LIFAN da sunan zai je zanje sai dai tunda ya karba bai dawo ba.
Ya kara da cewa wannan ne karon farko da ya taba baiwa wani hayar mashin ya gudu dashi.
‘Yan Vigilante sun kama dilan kwaya a kasuwar ‘yan Kaba
NOA ta nemi goyon bayan jama’ar Kano kan yaki da Covid-19
“Muna taimaka musune don su birge ‘yan matansu, amma kuma kaga shi maimakon ya dawo dashi sai ya gudu.
“Nagodewa Allah da aka kamashi, ba tare da ya siyar da baburin ba,” a cewar Gaddafi.
Shugaban kungiyar vigilante na unguwar Ja’en Yusuf Ibrahim Yakasai cewa yayi an sha kai musu korafi akan wanda ake zargi, kuma tuni suka mikashi hannun ‘yan sanda don girbar abinda ya shuka.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
