KANUN LABARAI
Dalibai a Kano na ci gaba da kokawa kan kin komawa makarantu
Aminu Abdullahi
Dalibai a jihar Kano na bayyana mabanbanta ra’ayoyi dangane da batun sake kulle makarantu da gwamnatin tarayya ke shirin yi.
Kano Focus ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta sanya ranar 18 ga Janairun 2021 a matsayin ranar komawa makarantu.
Sai dai hakan na neman gagara, biyo bayan ci gaba da yaduwar annobar Korana a jihar Kano dama kasa baki daya.
Muhammad Ibrahim dalibi ne da ke karatu a jami’ar Bayero da ke nan Kano ya ce akwai bukatar a yiwa batun kallo na tsanaki duba da yadda annobar ke cigaba da yaduwa a cikin al’umma.
Ya ce hadarin kamuwa da cutar Korona ba karamin abuneba, kuma babu wani dalili da zai sa malamin makaranta da gwamnati ke kyashin biyansa albashi ya sadaukar da rayuwar sa ga ‘ya’yan wasu.
“Idan korona ta kama malami ya mutu, gwamnati ko sunansa ba za ta sa a rubuta a majalisar kasa ba, don karramawa balle kuma a dauki dawainiyar iyalan sa”
Ma’aruf Muhammad da ke jami’ar kimiyya da fasaha dake Wudil ya ce kada jami’o’i su wahalar da dalibai musamman wadanda ke a nesa, ta yadda sai sun dawo kuma a ce an sake rufe makarantu.
‘Yan daba sun kashe malamin makaranta a Kano
Dole ne manyan makarantu su bi doka wajen yaki da cutar Covid-19 a Kano-Kwamishina
Rufe makarantu: Zanga-zanga ta barke a manyan makarantun Kano
“Ga tsadar kudin mota, ga matsalar tsaro akan titunanmu, idan har gwamnati ta sake rufe makarantu, ya tabbata cewa da kanta take son ruguza ilimin ‘ya’yan talakawa, duba da cewa ‘ya’yansu na cigaba da daukar karatu ta yanar gizo,” a cewar sa.
Muhammad Mustapha Kankarofi dake Yusuf Maitama Sule cewa ya yi bai kamata a bude makarantu a halin da ake ciki yanzu ba.
Ya ce akwai karancin kayan kariya daga cutar korona da jami’o’I ke fama dasu.
“Koda an bude, gwamnati ba za ta iya samarwa da jami’o’I isassun kayan kariya ba, kuma ana cunkoso sosai a ajujuwa, kuma kaga cutar nan tayanzu mai saurin yaduwa ce.
“ kafin a koma, a fara samar mana da sinadarin wanke hannu, da takunkumin rufe fuska kyauta, don kare kanmu.
“Idan gwamnati za ta iya yin wannan to zamu koma makaranta, amma idan ba za ta iyaba gwara kar a koma, domin rayuwar mu itace tafi muhimanci,” a cewar sa.
Sadiya Aliyu dalibace da ke karatu a jami’ar Yusuf Maitama Sule ta ce ya kamata a bude makarantu a ranar da aka sanya.
A cewarta tsahon lokacin da suka dauka ana yajin aiki zai tabarbara karatun idan ba a koma a lokacin da aka tsara ba.
“Kullum matsalar tsaro kara ta’azzara takeyi, sakamakon rufe makarantu, kwacen waya da zanga-zanga da fashi da makami wadannan da a ce makarantu a bude suke to za a samu raguwar aikatasu.
“Ni ina ganin gwara a daina yin karatun bokonma gaba daya, da irin wannan wasa da hankali da suke yiwa dalibai.
Kullum sai kaga ‘ya’yansu na bikin kamala makaranta saboda sunayi ne a jami’o’i masu zaman kansu.
“ Kuma ya kamata su san cewa rashin yin karatu ga ‘ya’yan talakawa wallahi barazana ce ga zaman lafiyar su, da ta iyalansu, duk kuwa da irin tsaron da suke takama suna dashi,” a cewar ta.
Muhammad Kabiru dake Yusuf Maitama Sule cewa yayi babu wanda ya kai talaka hakuri da bin doka.
Kuma duk da sun biya kudin makaranta sai dai an gaza koyar dasu abin da ya dace.
“Tunda su sunyi imani da wannan tsarin, mu su kyalemu mukoma makaranta idan yaso sai su kulle ‘ya’yan su a gida don kada su mutu amma wannan ba komai bane face ruguza kasa,” cewar sa.
Ya kara da cewa ya kamata shugabanni suji tsoran Allah akan maganar karatun dalibai, duba da yadda kullum ake samun koma baya a bangaren ilimi.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.