KANUN LABARAI
Yadda na rungumi sana’ar wanki da guga na watsar da boko-Dalibin jami’ar Bayero
Aminu Abdullahi
Abubakar Idris Bashir dalibi ne a jami’ar Bayero da ke nan Kano da ya ce shi kam yanzu sana’ar da ya runguma ta wanki da guga ta fiye masa zuwa makaranta.
Abubakar ya ce tunda kungiyar ASUU ta tsunduma yajin aiki ya shiga wani hali, sai dai daga bisani ya nemawa kansa mafita da ya rungumi sana’a.
A wata tattauna da jaridar Kano Focus Abubakar dan shekara 20 da ke zaune a unguwar tukuntawa kum ya ke karanta Geography a jami’ar ta Bayero ya ce tunda dai an zabi a kassara Ilimi shi kuma ya zabi ya kama sana’a.
A don haka ne kuma ya zabi ya fara sana’ar wanki da guga domin tallafawa kansa.

Na bata lokaci kan boko
Abubakar ya ce ada can ya bata lokacinsa da dama akan zuwa makaranta ba kuma ta samar masa da ko kwabo.
Yace kafin tafiya yajin aikin kungiyar ASUU naira dari biyar wahalar samu take yi masa sabanin yanzu da yake iya samun naira dubu biyu a rana.
A cewarsa a wata guda yana iya samun naira dubu hamsin zuwa sama.
”Yanayin kasarne sai a hankali da na dogara da cewa idan nagama makaranta zan samu aikin gwamnati ko na kamfani, to sai naga ya kamata na farka don na nemi na kaina ba tare da na dogara ga gwamnati ko wani ba.
“Kuma yanzu karatun ma bashi da tabbas in ka fara baka san lokacin da za ka gama ba.
“Kuna cikin yi sai ace an rufe makarantu sannan basu damu da mu ‘ya’yan talakawa ba,” a cewar sa.
Abokaina na min isgili
Ya kuma ce bayan daya lura cewa babu ranar bude makarantu hakan tasa ya fara tunanin me yakamata yayi don dogara da kansa.
“Na fara ne da wankin abokanaina lokacin da nace su kawo kayansu ina wanki da guga, wasu basu dauka da gaske nake ba, wasu kuma sai suka rinka cewa bai dace nayi sana’ar ba a isgilance
“Duk da haka ban karaya ba, a yanzu kaga bana tambayar kowa ya taimakamin da sisin kwabo, hasalima ni nake taimakawa wasu sanan nasiyi duk abinda raina yake so,”
Sana’ar na rufamin asiri
Ya kara da cewa sana’ar ta rufa masa asiri domin koda an koma makaranta zai iya biyan kudin makaranta da kansa ba tare da ya nemi tallafi daga gurin wani ba.
Sai dai yace matukar aka koma makaranta a yanzu ba lallai ya dinga samun wanki da guga kamar yadda yake samu ba, kuma hakan zai rage masa samun kudi.
Ya ce koda ba a sauya ranar komawa makarantun ba to tabbas zai rinka raba kafane don kuwa ba zai maida hankali kacokan akan karatu ba kamar yadda yayi a baya.
“Bazan karar da lokaci na a karatun bokoba, bayan kuma idan nagama ba lallai na samu aikin yi ba, amma kaga da wannan sana’ar idan Allah yasa mata albarka to sai na rufawa kaina asiri,” a cewar sa.
Haka zalika yayi kira ga ‘yan uwansa matasa dasu koyi sana’o’in dogaro dakai duba da halin da ilimi ya shiga a kasar nan.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
