KANUN LABARAI
Gwanda mu auri yayyen iyayenmu da mu auri samari marowata- Yan mata a Kano
Rafi’atu Ilyasu
Ƴanmata a Kano sunyi barazanar daina auren samari, sakamakon shiga ƙungiyar samari marowata, inda suka ce gwara su auri sa’anni iyayensu masu sakin aljihu.
Kano Focus ta ruwaito tun bayan da samari suka fara dunƙule hannu da rufe bakin aljihu ne, ‘yanmata suke ta cece-kuce a kan lamarin.
Har ta kai yanzu an fito d wasu kungiyoyi na marowata da ke koyar da tsuke bakin aljihu ga samari, da hana yan mata kudi duk da sunan yin hakan almubazzaranci ne.
A zantawar Kano Focus da wasu ‘yan mata a nan Kano sunce dasu auri mai dunkule hannu gwara su auri dattijo mai sakin hannu koda ya girmi ubansu.
Siddiqa Sadi Muhammad wata budurwace da ke zaune a unguwar Tudun yola, ta ce babu kira ba abinda zaici gawayi, ta ce matukar saurayinta ya shiga kungiyar za ta bashi dama ya fita.
Sai dai ta ce idan ya kekasa kasa ya ki ficewa to shakka babu za ta watsar dashi ta kuma nemi mai sakin aljihu.
“Wallahi babu ƙira babu abin da zai ci gawayi, muddin saurayina ya shiga wannan ƙungiya to zan bashi dama ya fita.
“Idan yaƙi fita zan iya rabuwa dashi, kuma idan na samu wanda hannunsa da aljihunsa ba a dunƙule ba, zan yi wuf da dashi ko da kuwa ba saurayibane.”
Ita kuwa Maimunatu Ɗahir Yunus da ke zaune a unguwar Sauna Kawaji, dake karamar hukumar Nasarawa,cewa tayi ko kadan bata amince da tsarin ba.
“Mu mata ba aikin yi ne damuba, samarin sune ke saka mana data, su ne suke saka mana kati don kiran a bokan arziƙi.
“Haka kuma su ne ke bamu kuɗin da mukeyin anko, su suke siya man kayan kwalliya, da abubuwan da ba za a rasa ba.”
“Idan a kace sun dunƙule hannunsu, tayaya zamu samu waɗannan abubuwa.
“Indai za su dunƙule hannu muma zamu ɗauki matakin da ya dace, kinga kenan sun daina zuwa hira gidanmu, kowa ya zauna a inda yake.”
“Har ga Allah in dai za a ɗora da wannan doka, to har dani a cikin ƴanmatan da za su sha wahala.”
Sheikh Ameer Sarki shi ne shugaban kungiyar samari marowata ta Kano, a zantawarsa da Kano Focus ya ce an kafa kungiyar ne domin kawar da almubazzaranci a cikin jama’a.
Ya ce manufar kafa kungiyar shi ne yaki da barnar kudi ba gaira ba sabar da samari ke yi akan ‘yan mata.
Ya ce jama’a basu fahinci manufar kungiyar ba ne, shi yasa suke yi mata wani kallo na daban.
“Maƙasudun wannan ƙungiya shi ne, kare mutuncin mata, domin wannan ƙungiyar babu wanda tayiwa gata sama da mata, sabo da gudun tozarci ko yaudara.”
“Mata a kan kansu suna cewa: ‘kiji tsoron namijin da zaizo yana kashe miki kuɗi’ a ƙarshe zakiga yana da wata manufa a kan ki.
Ameer ya cigaba da ce wa, kashe-kashe kudin ke rudar mata na fadawa matsala da ke rushe musu tarbiyya.
“Amma idan mutum ya dunƙulle hannunsa, ya rufe bakin aljihu, baima kashe miki kuɗi ba, bare yazo miki da wata maganar banza.
“Daga sanda muka aure mace, dole mu buɗe mata bakin aljihu, saboda muna shan zagi yanzu a gunsu, wasu ma sun daina kulamu.”
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.