Connect with us

KANUN LABARAI

Watanni 10 ba karatu, daliban Jami’ar Bayero sun sake fadawa hadarin yajin aiki

Published

on

Aminu Abdullahi

Harkokin karatu sun fara samun tasgaro a jami’ar Bayero dake jihar Kano sakamakon yajin aikin kungiyar ma’aikatan jami’o’i da ba malamai ba wato SSANU da NASU.

A zagayen da Kano Focus tayi a cikin jami’ar ta gano yadda ma’aikatan suka kulle wasu daga cikin ajujuwan karatu dake makarantar da kuma katse wutar lantarki.

Haka zalika ma’aikatan jami’ar sun tsaida duk wasu aikace aikace da suka shafi al’amuran dalibai da motocin makaranta dake jigilar dalibai.

Wasu dalibai da suka bayyana alhinin su bisa matakin da kungiyar ma’aikatan jami’o’in ta dauka sunce wanan wata hanyace da za ta haifar musu da matsala a karatun su.

Wani dalibi mai suna Abdullahi Haruna da ke sashen nazarin Kwamfuta ya ce kulle ajujuwan ba zai basu damar yin karatu ba saboda masu  yajin aikin ne ke da mukullayen ajujuwan.

Ya kara da cewa kamata ya yi a ce ajujuwan na bude tun daga karfe takwas na safe amma har zuwa yamma ba a bude musu koda a ji daya ba.

“Gashi muna gab da fara jarabawa kaga idan har aka cigaba da tafiya a haka bama samun damar yin lecture zamu samu matsala babba,” a cewar sa.

Wata daliba Maryam Sulaiman ta ce ko a daren ranar Litinin cikin duhu suka kwana a gidajen dalibai dake makarantar sakamakon kashe musu wuta da ma’aikatan su kayi.

Ta ce wasu guraren ma kananan inji suka kunna domin su samu haske da damar yin karatu.

“Kamar mu da muke kwana a gidajen dalibai dole za mu shiga matsala sosai muna fata za su duba halin da muke ciki su janye wannan yajin aiki da suke yi,” inji ta.

Abdulmalik Umar ya ce yajin aikin yajanyo kazanta ta yawaita a cikin makarantar sakamakon rashin yin shara.

“Sannan duk an bata bandakuna ba a sharesu a iya kwana hudun nan da akayi wani bandakin ma sai ya saka amai.

“Suma suna da muhimmanci sosai don idan ba tare da su ba abubuwa ba za su tafi yadda ya kamata ba.

“Sune suke share ko ina da bandaki da guraren kwanan dalibai,” a cewar sa.

Sai dai da aka tuntubi kungiyoyin da ke yajin aikin sunce ba gudu ba ja da baya a yajin aikin da suke yi, har sai an biya musu bukatunsu.

Shugaban kwamitin hadakar kungiyoyin ma’aikatan jami’ar Haruna Aliyu ya ce a watan Oktoban shekarar da ta gabata sun zauna da gwamnati inda suka kulla alkawaruruka da suka shafi rashin daidaito a bangaren albashi na IPPS.

Ya ce sun  kuma kulla  alkawari kan yarjejeniya akan rashin biyan ma’aikata da suka kammala aiki hakkokin su da kuma biyan ma’aikatan jami’a karin albashin da gwamnatin tarayya tayi musu.

Ya kara da cewa sun kashe wutar jami’ar gaba daya tun daga tushe dake baiwa makarantar wuta da kuma dakatar da ma’aikatan su dake asibitocin makarantar da sauran muhimman gurare.

“A ranar Alhamis za a sake zama kuma muna kan tattaunawa don sake daukar mataki na gaba,” a cewar sa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending