Connect with us

KANUN LABARAI

Gididdiba gidan rediyo: Rikici ya kunno kai tsakanin gwamnatin tarayya da ta Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

A jiya Alhamis ne al’ummar unguwar tukuntawa suka wayi gari da ganin wani allo da gwamnatin tarayya ta kafa a Kofar gidan rediyon Tukuntawa da ke nuna cewa wurin mallakintane ba na gwamnatin Kano ba.

Kano Focus ta ruwaito an rubuta a jikin allon cewar wannan wuri mallakin gwamnatin tarayya ne, duk  wanda ya yi amfani da shi za a dauki matakin shari’a a Kansa.

wannan dai na nuna yadda gwamnatin tarayya ta ke gargadin gwamnatin Kano kan batun sayarda gidan rediyon da take shirin yi.

Idan za a iya tunawa dai tun a makon da ya gabata ne gwamnatin Kano ta yanka filaye a cikin filin gidan rediyon inda ta ce tayi hakanne bisa barazanar tsaro da gurin keyi ga al’ummar yankin.

Al’umma dai sun dade suna zargin gwamnatin da saida muhimman wurare da al’umma ke amfani dasu wajen neman rufin asiri.

Sai dai da misalin karfe goma sha daya da rabi na ranar Alhamis ne ma’aikatar ayyuka da wutar lantarki da gida je ta kasa tare da jami’an tsaro suka sanya alama a kofar gidan rediyon dake nuna cewa gurin mallakin gwamnatin tarayya ne ba na jihar Kano ba.

Wasu mutane dake gudanar da sana’a a kusa da gidan rediyon sun yiwa Kano Focus bayanin yadda lamarin yake.

Bala Usman ya ce wadanda suka sanya alamar sun zo ne tare da jami’an tsaron farin kaya na Civil Defence da karfe sha daya da rabi na safiya.

Sai dai ya ce da karfe biyu na ranane kuma ma’aikatan dake sauke arear gidan rediyon suka hake alamar tare da shigar da ita cikin gidan rediyon.

Warisu Dauda ya ce sanda jami’an suka zo gurin basu hantari kowa ba, inda ya ce sun sanya alamar ne ta re da yin gaba abin su.

Sai dai da muka tuntubi shugaban gidan rediyon Kano Malam Gali Sadiq ya ce ko kadan gidan rediyon ba mallakin gwamnatin tarayya bane.

Ya ce tun a shekarar 1984 gwamnatin tarayya ta mallakawa gwamnatin Kano gidan rediyon.

Haka zalika ya ce suna zargin ma wasu ne kawai masu san tada husuma suka kirkiri kafa allon amma ba gwamnatin tarayyaba.

Wannan ce ma ta sanya suka bada umarni a cire allon da aka kafa, ya kuma ce tuni suka shigar da korafi ga jami’an tsaro kan cewa wasu mutane sun kafa musu alluna.

Gali Sadiq ya  ce idan ma gwamnati tarayyace, to kamata yayi tabi hanyoyin da suka kamata abi, su kuma yi magana da gwamnati Kano amma ba kawai su kafa alloba.

Kokarin jin ta bakin gwamnatin tarayya kan al’amarin ya ci tura amma zamu ci gaba da bibiya mu kawo muku dalilan da ya sanya suka dauki matakin sanya allon.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending