Connect with us

KANUN LABARAI

Da gan-gan gwamnati ta ki biyan kudin NECO-Iyayen yara

Published

on

Aminu Abdullahi
Iyayen yara da dalibai na cigaba da kokawa bisa yadda gwamnatin jihar Kano ta gaza biyan kudin jarabawar kammala karatun sakandire (NECO) da dalibai suka rubuta a watannin baya.
Kano Focus ta ruwaito cewa tun a watan Janairun shekarar da muke ciki ne a ka saki jarabawar  ta (NECO)  ta makarantu masu zaman kansu, sai dai sakamakon daliban makarantu gwamnati ya gaza fita a jihar nan.
Wani mahaifi mai suna Abubakar Isma’il da yaron sa ya rubuta jarabawar a makarantar sakandire dake Sabuwar Kofar ya ce dansa ya samu gurbin karatu a jami’a da kuma ake gab da fara tantance su sai dai rashin sakamakon jarabawar l na neman yiwa yaron nasa kafar ungulu wajen samun gurbin karatu.
Ya ce tuni aka saki sakamakon jarabawar na makarantu masu zaman kansu, amma har yanzu gwamnati ta gaza biyan kudaden daliban da suka zana jarabawar a makarantun gwamnati.
Ya kara da cewa idan har gwamnati ta gaza biyan kudin don sakarwa ‘ya’yan su sakamakon jarabawar to la shakka  za su rasa guraben karatu a jami’a a wannan shekarar.
Balarabe Musa mahaifine da yaron sa ya rubuta NECO a Kwalejin Rumfa ya ce rashin baiwa ilimi muhimmanci ne yasa har yanzu gwamnati ta gaza biyan kudin jarabawar.
Ya kara da cewa ya kamata gwamnati ta duba halin da ‘ya’yansu ke ciki musamman yadda suke neman rasa guraben karatu.
Sadiya Hassan ta ce dama can gwamnatin jihar Kano ta saba yin jinkiri wajen biyan kudin jarabawar dalibai a jihar Kano.
Ta ce bai kamata a ce ana samun tasgaro a irin wannan al’amari ba duba da cewa hakan na kara haddasa lalacewar ilimi.
” Yarinyata ta samu gurbin karatu amma kaga idan ba taje da takardun shaidar kammala sakandireba ba za a tantance ta ba.
” Sai ta kara jiran wata shekarar tukunna a irin wannan ne kuma sai kaga karatun yara ya lalace,” a cewar ta.
Binta Garba da ‘yar ta ke karatu a makarantar sakandire ta Liman Idris Maikalwa a unguwar Na’ibawa ta ce tana rokon gwamnatin jihar Kano da tayiwa Allah da Annabi ta biya kudin jarabawar ‘ya’yan su.
“Saidai fa muka biya gwamnati kudin rubuta jarabawar nan naira dubu 12 da 500 kowa hakama nima na biyawa yarinya ta.
“Mun riga mun biya kudin mu amma meyasa gwamnati zataki biyan hukumar kudin don Allah a taimaka a biya don su samu su shiga Jami’a,” a cewar ta.
Sani Salisu Dan hassan shine shugaban kungiyar iyayen yara ya ce za su je duk inda ya dace don tabbatar da cewa an saki sakamakon jarabawar daliban.
Ya kara da cewa wannan rikon sakainar kashi ne da ake yiwa ilimi, duk da cewa kwamishinan ilimi yayi alkawari  za a saki sakamakon amma har  yanzu shiru.
Sai dai duk kokarin da muka yi don jin tabakin kwamishinan ilimi na jihar Kano Sanusi Sa’idu Kiru abin ya ci tura.
Sa’idu Kiru ya ce da wakilin namu da ya sameshi a ofis domin jin bayani.
Koda yaje sai kwamishinan ya ce yaje ya ga babbar sakatariyar ma’aikatar, inda itama tace masa ai sunyi waya da kwamishina ya koma ofishin sa.
Saidai duk da tsahon lokacin da ya dauka yana jiran sa amma bai samu damar ganin sa ba.
Wannan na nuna cewa gwamnatin Kano na son yin wasa da hankulan jama’a ne kawai amma Basu da abin fada

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Malaman Tijjaniyya na Kano sun kai wa Khalifa Muhammad Sanusi ll mubaya’a

Published

on

Nasiru Yusuf

Majalisar Shura ta Dariqar Tijjaniyya ta Jihar Kano ta kai wa Maimartaba Sarkin Kano na 14 Malam Muhammadu Sanusi II mubaya’a bisa nadin da aka yi masa na babban Khalifan Shehu Ibrahim Inyass a Nigeria.

KANO FOCUS ta ruwaito cewa Malaman sun yi wa Malam Muhammadu Sanusi ll mubaya’ar ne ranar Asabar karkashin jagorancin Sheikh Abdullahi Awaisu Limanci.

Malaman da suka kai ziyarar mubaya’ar sun hada da Khalifa Tuhami Shehu Atiku da Shehi Shehu Maihula da Imam Muhammad Nura Arzai da kuma Sheikh Dayyabu Dan Almajiri.

Sauran sun hada da Khalifa Hassan Sani Kafinga da Khalifa Bashir Musa Kalla da Khalifa Fatihi Uba Safiyanu da Khalifa Kamilu Yalo da Sheikh Tijjani Maisalati Indabawa da kuma Sheikh Kabiru Zango.

Tawagar kuma ta kunshi zuriyar Shehu Ibrahim Inyas mazauna Kano karkashin jagorancin Sayyada Rahama Ibrahim Inyas.

Continue Reading

Hausa

Majiyyata sun koka kan yajin aikin likitoci a Asibitin Malam Aminu Kano

Published

on

AKTH

Aminu Abdullahi

Yajin aikin likitoci masu neman kwarewa a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano ya jefa marasa lafiya cikin mawuyacin hali.

A zagayen da Kano Focus tayi ta gano yadda yajin aikin likitoci masu neman kwarewa ya gurgunta harkokin kula da lafiyar majiyyata a asibitin.

Wani majinyaci mai suna Abba Shehu ya ce mafi yawansu ‘yan’uwansu ne ke kulawa da su.

Ya kara da wasu kuwa an salleme su zuwa gida sakamakon karancin wadanda za su kula da su.

Ya kara da cewa a ya yin da aka shiga kwana na uku ana yajin aikin ya gaza samun allurar da yakamata a yi masa.

“Typhoid ke damuna, a da ina samun kulawa sosai, sa6anin yanzu. Iya magunguna kawai na sha, amma ba bu wanda zai yi min allura,” a cewarsa.

Maryam Yusuf cewa ta yi, ta fara rashin lafiya ne daga ciwon kai wanda har takai ga ta kwanta.

Ta kara da cewa tazo ganin likita, amma cikin rashin sa’a aka ce bai zo ba, duk da cewa ciwon yana damunta.

A nasa bangaren, shugaban kungiyar likitoci masu neman kwarewa reshen asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano Mujahid Muhammad Hassan, ya ce ba za su koma bakin aiki ba har sai an biya musu bukatunsu.

Ya ce kaso saba’in da biyar na likitocin asibitin suna cikin kungiyar, kuma sune suke gudanar da yajin aikin.

Ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta gaza biya musu bukatarsu ta kara kudaden ‘hazard allowance’ da suka yi ‘yarjejeniya a shekarar da ta gabata.

“Kudin da ake baiwa ma’aikatan lafiya na ‘hazard allowance’ bai wuce dubu biyar ba a wata.

“A kwai likitocin da ake cewa ‘house officers’ ba a biya su albashinsu na watanni uku ba, shima muna bukatar a biyasu dukkan hakkokinsu kafin mu janye yajin aiki,” a cewar sa.

Ya kuma ce dole ne a biya su ‘allowance’ kaso hamsin cikin dari na cikakken albashin kowane ma’aikaci.

Ya ce “Dole ne a biya mu bashin ‘allowance’ na yaki da annobar COVID-19 a manyan asibitocin jihohi.”

Continue Reading

Hausa

Rashin kasuwa ya sa ma su sayar da zo6o komawa sana’ar kunu

Published

on

Aminu Abdullahi

Kasuwar zobo da kunun aya da lemo da kuma lamurje na neman 6acewa a jihar Kano biyo bayan hana sayar da kayan hadin lemukan da gwamnatin jihar tayi.

Kano Focus ta ruwaito yadda wasu ma su sana’ar zo6o suka koka bisa yadda a yanzu sana’ar ke neman rugujewa sakamakon rashin masu siye.

Talatu Hassan ta ce ada tana yin cinikin zobo na naira dubu uku a kowace rana saidai a yanzu dakyar take sayar da na Naira dari biyar sakamakon rashin ma su siye.

Ta kara da cewa kayan hadin suna da matukar tsada kuma ba ko ina ake samun su ba sakamakon haramta sayar da su da akayi.

” Idan munje kasuwar ma a boye ake siyar mana da su wani lokacin ma haka muke dawowa ba tare da mun siyo ba.

” Jarina ya karye kowa yana jin tsoron siya don kada ya kamu da wata annoba a zahirin gaskiya muna cikin wani hali,” a cewar ta.

Aisha Lawan ta ce tana saidai zo6o da lemo da kunun aya na Naira dubu hudu kafin bullar annobar da ake zargin sinadaren hadawa ne suka haddasata.

Saidai ta ce a yanzu tana sayar da iya zo6o ne kawai ba kuma tare da ta sanya masa sinadaren da ta saba sawa a baya ba.

“Yanzu ba a siyar dasu sai ansha wahala ake samu ina yin zo6o na dari uku ko biyar ne a kullum shima da siga kawai nake hadashi.

“Gaskiya a yanzu yafi tsada tunda ba bu kayan hadi dake saka shi zaki, kawai iya dafaffen Zobo ne da sikari,” inji ta.

Ta kuma ce kamata yayi gwamnati ta samar da doka mai tsauri da za a hukunta duk wanda aka kama yana saida sinadaren da suka lalace maimakon haramta siyarwa gaba daya.

” Kaga yanzu azumi na zuwa kuma mun fi yin ciniki da azumi fiye da yadda muke yi a baya, don ni na yanke shawarar fara tuyar awara tunda yanzu ba bu kasuwar zo6o,” a cewar ta.

Rukayya Abdullahi ta ce yanzu ta koma sana’ar sayar da awara da Kunu saboda daina siyan zobo da aka yi.

“Tun daga lokacin da aka ce annobar nan ta bulla kuma a sanadiyyar kayan hadin zobo, nake tafka a sara.

” Dole ce ta sanya na koma sana’ar saida kunun tsamiya da awara domin idan na zauna ba bu mai ba ni,” inji ta.

” ya”ya na uku kuma mahaifinsu ya rasu shekaru biyar da suka gabata,” a cewar Rukayya.

A na su bangaren wasu mutane sun bayyana fargabar da suke da ita na shan Zobo.

Saifullahi Usman ya ce duk da cewa mahukunta na alakanta annobar data faru da shan zobo wanda aka hada da sinadaren da suka lalace amma har yanzu yana siya ya sha.

Ya ce a yadda ake zafi a gari yana bukatar abinda zai sanyaya masa makoshi mai zaki kuma bashi da halin da zai sayi lemo dan kamfani wanda hakan tasa yake cigaba da siyan dan hadi,” a cewar sa.

” Ni ba zan iya kashe fiye da naira dari ba don kawai nasha lemon roba na kamfani na gwammace nasha zobo na Naira hamsin na hada da abincin dari da hamsin.

Kullum sai na siya amma dai yawan sa bai kai na da, da nake siya ba,” inji shi.

Zainab Jibril ta ce daga lokacin da annobar ta bulla zuwa yanzu bata kara shan wani abu da tasan ana hadawa da sinadarin ba.

Ta ce wani lokacin ma takan gwammacewa ta hada da kanta maimakon siyan na waje.

“ina fata a shawo kan wannan matsala kafin azumi, don al’umma za su shiga cikin wani hali matukar aka tafi a haka,” inji ta.

Continue Reading

Trending