KANUN LABARAI
Alkalan da za su jagoranci mukabalar Kano
Mukhtar Yahya Usman
Babban limanin Kano Farfesa Sani Zaharadden da kuma shugaban masallacin Abuja Farfesa Shehu Galadanci ne za su yi alkalanci a mukabalar da za a gudanar tsakanin Sheikh bduljabbar Kabar da sauran malaman Kano.
Kano Focus ta ruwaito kwamishinan al’amuran addini na jihar Kano Muhammad Tahar Adam Baba Impossible ne ya sanar da hakan ga maneman labarai ranar Lahadi.
Kwamishina ya ce an zabi malaman ne saboda kwarewarsu da kuma fahintarsu da addini, ana kuma ganin basu da wani bangare.
Sannan ya ce ya mikawa Abduljabbar takardar gayyata hannu-da hannu somin gujewa cewar sakp nai je ba.
“Ni a matsayina na kwamishina ni aka umarta da na kai wa Abduljabbar takarda.
Kuma na kai masa ita har gida, hannu da hannu har ma ya saka hannu na shaidar karɓa.”
Kwamishinan ya ce sauran malamai waɗanda suka rubuta takardar ƙorafi da murya ɗaya za su bayyana sunayen malaman da za su fafata da Abduljabbar zuwa ranar Laraba.
Za a gudanar da muƙabalar ce a Fadar Sarkin Kano Aminu Ado Bayero.
Haka zalika kwamishinan ya ce za a gudanar da mukabalar ne bisa abubuwa tara da malamai su yi korafi a kai.
Haka zalika cikin wadanda ake sa ran za su halarci taron a matsayin babban bako akwai Sarkin musulmi Muhammd Sa’ad Abubakar.
Hausa
Mutane 18,000 sun amfana da aikin ido kyauta ta Gidauniyar Mangal a Katsina
Kimanin marasa lafiya masu rauni 18,000 da ke fama da cututtukan ido daban-daban a jihar Katsina sun amfana da ayyukan kulawar ido da tiyata kyauta da Gidauniyar Mangal ta dauki nauyi tun bayan kafuwarta a shekarar 2016.
Wani mamba na kwamitin amintattu (Board of Trustees) na gidauniyar, Malam Hussaini Kabir, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin kaddamar da aikin tiyatar ido na zangon karshe na shekarar 2025 a Cibiyar Ido ta Katsina.
Kabir ya bayyana cewa kimanin mutane 7,000 ne suka amfana a shekarar 2025 kadai, daga sassan jihar Katsina, jihohin makwabta, har ma da wasu yankuna na Jamhuriyar Nijar.

A cewarsa, gidauniyar ta fara tantance wadanda za su amfana kimanin makonni biyu da suka gabata, inda marasa lafiya da dama suka samu magunguna kyauta da tabarau na likita.
Kabir ya kara da cewa wadanda ke bukatar tiyata an dauki nauyin dukkan zaman asibitinsu gaba daya, yana mai cewa kimanin marasa lafiya 2,000 aka tantance a yayin aikin zangon karshe da ake ci gaba da yi.

Ya sake jaddada kudirin gidauniyar na inganta samun kulawar lafiya, yana bayyana shirin a matsayin wani bangare na nauyin alhakin zamantakewar kamfanoni (corporate social responsibility).
“Manufarmu ita ce tallafa wa kokarin gwamnati tare da rage nauyin kudin kula da lafiya ga mafi rauni, musamman wadanda ke fama da matsalar biyan bukatun rayuwa,” in ji shi.

Wani likitan ido a cibiyar, Dokta Ahmad Hamza, ya bayyana cewa an gano marasa lafiya da dama na fama da cutar idon toka (cataract) da glaucoma, cututtuka da galibi ke bukatar tiyata.
Ya jaddada muhimmancin duba ido akai-akai, yana mai cewa gano cuta da wuri na taimakawa wajen hana asarar gani ta dindindin da cututtukan ido masu zuwa a boye ke haifarwa, kamar glaucoma, cataract da lalacewar macula (macular degeneration).

Daya daga cikin wadanda suka amfana, Malam Yusufa Usman, ya ce ya shafe sama da shekaru biyu yana fama da matsalar gani amma ba shi da ikon biyan kudin tiyata.
“Tsawon shekaru biyu ban iya gani sosai ba, amma yau na yi tiyata kuma ina da fatan ganina zai dawo.
Ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya saka wa Gidauniyar Mangal da alheri bisa wannan kyakkyawan aiki.
“Ina fatan sauran masu kudi za su yi koyi da wannan abin a yaba,” in ji Usman.

Wata mai amfana, Aisha Muntari daga kauyen Bakuru, ta bayyana kwarewarta yayin da take jiran a kai ta dakin tiyata.
Muntari ta ce ta kamu da matsalar ido kimanin shekara guda da ta wuce kuma ta kusa yanke tsammani kafin ta samu labarin shigar gidauniyar, tana mai bayyana kwarin gwiwar cewa nan ba da dadewa ba ganinta zai dawo.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
