Connect with us

Hausa

Juna biyu: Tsakanin rama azumi da ciyarwa-Fatawar malamai

Published

on

Zulaiha Danjuma

Limamin masallacin juma’a na Usman bn Affan da ke Kofar Gadon Kaya Malam Abdallah Usman ya ce mace mai cikin da tasha azumi ramawa za ta yi ba ciyarwa ba.

Abdallah Usman ya bayyana hakan ne ya yin zantawarsa da jaridar Kano Focus a wani bagare na rahotannin guzurin azumi ranar Litinin.

Malamin ya ce maganar ciyarwa da ake yi ba dai-dai ba ne kuma ana tafaka kuskure ne.

“Duk me cikin da ya halalta tasha azumi idan ta sha azumi  za ta rama ne idan ta haihu.

“Amma maganar ciyar wa da’ake yi kuskure ne ba dai-dai bane”

Sai dai wasu malaman na ganin ciyarwar ma ta wadatar ga mai juna biyun da ta haihu.

Malam Nuhu Muhammad Tukuntawa ya ce duk macen da ta ke da ciki ta sha azumi za ta rama ne kamar yadda malam ya ambata a sama.

Sai dai ya ce akwai hadisan da suka nuna cewa matukar mace ta ciyar to ba sai ta rama ba.

“An ce idan ta sha azumi to ta rama anan ba maganar ciyarwa.

“Idan kuma ta ciyar to kada ta rama tunda dama abubuwa guda biyu ake nema”

“Saboda abin da ake jin tsoro shi ne cikin ne ya hanata yin azumin kuma za ta sake haihuwa, kuma ga danta da za ta shayar, wanda yake ko wanne daga cikin su ana iya ajiye azumi a kansa”

“Shi yasa aka bada rinjayen cewa idan ta ciyar ba sai ta rama ba, saboda abin da aka ganin gaba za ta sake wata wahala.

“Saboda shayarwa da ciki ana ajiye azumi akan su, shi ne abinda malamai suka tsaya akai”

Wadanne lokuta ya kamata mai juna biyu ta ajiye azumi?

Acewar malam Abdullah Gadon Kaya ba kowanne ciki ne aka amince a ajiye azumi saboda shi ba.

A cewarsa a shari’a cikin da aka tabbatar zai cutar da ita ko dan da ke cikinta to sai a bata hukuncin mara lafiya.

Ya ce matan da ke da yaron ciki wata daya zuwa uku da basu san ma suna da shi ba to wadannan azumi bai sauka akansu ba

Sai dai a cewar Malam Nuhu, babu wata ka’ida da aka ce ga cikin da ya kamata a jiye azumi

A cewarsa abinda ake tsoro shi ne jin wahalar mai juma biyun, amma ba yanayinsa ba.

“Wata za a ga ta daina al’ada da zarar ta dauki ciki, wata daga nan ake gane  tana da ciki saboda yanayin ta gaba daya zai canza.

Wata daga nan za ta fara zubar da yawu da kuma ciwon ciki da sauran cutuka”

“Gwargwadon yadda ta samu kanta da yanayin cutar , za ta iya ajiye azumin ko da cikin na wata uku ne.

“Da yake lokacin yafi wahala lokacin ne ake amai, ake rashin lafiya, kawai sai ta ajiye inta samu lafiya sai ta ci gaba.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil wasan yara ne – Prof. Alkafawy

Published

on

Malam Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Majalisar Malamai ta Kasa ta bayyana yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta Jihar Kano da cewa wasan yara ne.

A wata sanarwa da KANO FOCUS ta samu Mai dauke da SA hannun Sakataren Kungiyar Farfesa Muhammad Sadik Alkafawy ya sanyawa hannu ranar Alhamis ta ce abun da aka yi ba ya bisa doka.

Ga cikakkiyar sanarwar:

“Majalisar  Malamai ta Kasa ta sami labarin yunkurin wata jama’a da ke kiran kanta Malamai, amma ta bari wasu wadanda ba su nufin alheri su yi amfani da su a kawo baraka tsakanin jama’ar Musulmi. Wannan abin takaici ne.

“Tun daga ranar da a ka assasa Majalisa zuwa yau ba a taba samun tabargaza irin wannan ba. Don haka Majalisa ta Kasa na yin kira ga wadannan mutane su tsoraci Allah su kauce ma son zuciya.

“Hakika Majalisar Malamai reshen jihar Kano ta yi daidai da tace wadanda su ka shiga wannan bankaura ba ‘ya’yanta ba ne tun daga jiha balle na Kasa. Yaya za a yi wanda ba ya cikin Majalisa ya ce ya kori wanda a ka kafa Majalisa da shi?.

“A wurin Majalisa ta Kasa abinda a ka yi ba ya bisa doka, kuma wasan yara ne. Hasali ma fata mu ke Allah ya ba shi shugabancinta na Kasa baki daya, amin.

“A karshe, Majalisar kasa ta yi mawafaka da duk abinda Majalisar Kano ta tsaya a Kai. Alhamdu Lillah.”

Continue Reading

Hausa

Tijjanawa ba sa goyon bayan nadin Pakistan shugaban Majalisar Malamai – Alkarmawi

Published

on

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

 

 

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم 

وصلي الله علي النبي الكريم 

Majalisar Malamai ta jihar Kano tana da mahimmanci ga Musulmin Arewacin Nigeria gaba daya ba Kano ba kawai, don ko ba komai Al’ummar Musulmi suna kara samun hadin kai da magana da murya daya sanadiyar wannan majalisar kuma babban abun bukata shine hadin kan Musulmi.

Amma sabon shugabanci da akai jiya (Litinin) da aka nada Malam Abdallah Saleh Pakistan (Shugaban Izala na jahar kano) zai iya rusa majalisar ma gaba daya, Saboda Shugabancin yana bukatar malamin da yake Zaune lafiya da duk akidun Musulunci da suke Kano, wanda Pakistan kuwa yana da matsala da wasu bangarorin.

Shawarata kowa a nan shine Asami malamin da yaki da kyakkywar alaka da kowa ya jagoranci Alumma Sai asami kai wa ga gaci.

Don haka a madadin Tijjanawa, gaskiya gabadayanmu musamman na jihar Kano muna sanar da cewa ba ma tare da Shugabacin Malam Abdallah Saleh Pakistan.

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Shugaban Khuddamur Rasul SAW na Afrika

Continue Reading

Hausa

Gamayyar Malaman Kano sun nesanta kan su daga tsige Malam Ibrahim Khalil

Published

on

Sheikh Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Gamayyar Malaman Jihar Kano da suka kunshi jagororin darikun Tijjaniyya da Qadiriyya da kuma Salafiyya sun yi watsi da sanarwar tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin majalisar malamai.

Wata sanarwa da KANO FOCUS ta ci karo da ita dauke da sa hannun sakataren gamayyar Malaman, Dr Sa’idu Ahmad Dukawa ranar Talata malaman sun ce ba da yawunsu aka dauki wannan mataki ba, kuma ba sa goyon bayansa.

Malaman da suka sahale a fitar da sanarwar sun hada da Shugaban Darikar Kadiriyya na Afrika ta Yamma Sheikh Karibullahi Sheikh Nasiru Kabara da Sheikh Abdulwahab Abdallah da Sheikh Ibrahim Sheh Maihula da Dr. Bashir Aliyu Umar da kuma Imam Nasir Muhammad Adam ( Shugaban majalisar Limaman masallatan Juma’a).

Sauran sun hada da Farfesa Musa Muhammad Borodo da Farfesa Muhammad Babangida da kuma Dr. Ibrahim Mu’azzam Maibushira.

Continue Reading

Trending