Connect with us

Hausa

Sarki Sunusi II baya Cryptocurrency- Naziru Sakin Waka

Published

on

Deposed Emir Sanusi

Aminu Abdullahi

Mawaki Naziru M Ahmad da akafi sani da sarkin waka ya ce ba gaskiya bane zance da wasu ke yadawa cewa tsohon sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu na yin kasuwanci cryptocurrency.

Kano Focus ta ruwaito mawakin ya bayyana hakanne a cikin sakon video da ya wallafa a shafin sa na internet a ranar lahadi.

Ya ce ba gaskiya ba ne yadda wasu ke yaudarar al’umma da cewar tsohon sarkin yanayi da nufin jan hankalin mutane cikin tsarin crypto.

“Na tambaya kuma an tabbatar min da cewa bayayi, don haka ya kamata al’umma su fadaka a dena yaudarar su,” a cewar sa.

Ya ce mutanen da ke cikin tsarin Cryptocurrency sun jahilci kalaman da ya yi dangane da yadda suke zuba kudi a cikin tsarin.

Ya ce wadanda ke cikin tsarin sun jahilce shi domin ko kadan bai ce kada a yi cryptocurrency ba ko tsarin bai da ce ba.

Ya ce yayi mamaki yadda yaga mutane na zagi da cin mutuncinsa dangane da kalaman da ya yi.

“Ni dai na ce ba sako tsakanina da dan crypto domin kuwa shi dan crypto kana bashi kudi ya kaiwa wani zaije ya zuba su ne kawai a crypto ya ce zai samu kudi.

“Kuma idan ka aike shi ya siyo maka abu kafin yakai ya saka su, ko a bashi kudi ya biya kudi makaranta ko albashin ma’aikata maimakon ya biya su sai ya zuba su a cikin crypto,” a cewar sa.

Naziru ya ce ya sha yin aike da kudi amma sai wanda ya aika yaje ya zuba su a cikin tsarin crypto ba sau daya ko sau biyu ba.

Ya kara da cewa ko kadan bai cewa dan crypto cima zaune ba ko mai neman arziki a banza ba.

“ Kuma ni bance musu marasa wayo ba ko barayin zaune ba, haka zalika ni bance crypto baya yi ba.

Ya kuma ce akwai hanyoyin yin kasuwanci da yawa da yakamata mutane su bi don samun kudi.

“Akwai manyan ‘yan kasuwa irin su Aliko Dangote da Mustaphs AMASCO da BUA ba za su taba baka shawara akan crypto ba.

Sai dai su sayar da taliya da sauran su irin su Mudanseer duk ba crypto suke yi ba.

“In dai ilimin kasuwanci ne ai a gurin irin wadan nan mutanen da na fada muku zamu koyi darasi domin a gurin su muka ga ta bulle, a cewar sa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil wasan yara ne – Prof. Alkafawy

Published

on

Malam Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Majalisar Malamai ta Kasa ta bayyana yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta Jihar Kano da cewa wasan yara ne.

A wata sanarwa da KANO FOCUS ta samu Mai dauke da SA hannun Sakataren Kungiyar Farfesa Muhammad Sadik Alkafawy ya sanyawa hannu ranar Alhamis ta ce abun da aka yi ba ya bisa doka.

Ga cikakkiyar sanarwar:

“Majalisar  Malamai ta Kasa ta sami labarin yunkurin wata jama’a da ke kiran kanta Malamai, amma ta bari wasu wadanda ba su nufin alheri su yi amfani da su a kawo baraka tsakanin jama’ar Musulmi. Wannan abin takaici ne.

“Tun daga ranar da a ka assasa Majalisa zuwa yau ba a taba samun tabargaza irin wannan ba. Don haka Majalisa ta Kasa na yin kira ga wadannan mutane su tsoraci Allah su kauce ma son zuciya.

“Hakika Majalisar Malamai reshen jihar Kano ta yi daidai da tace wadanda su ka shiga wannan bankaura ba ‘ya’yanta ba ne tun daga jiha balle na Kasa. Yaya za a yi wanda ba ya cikin Majalisa ya ce ya kori wanda a ka kafa Majalisa da shi?.

“A wurin Majalisa ta Kasa abinda a ka yi ba ya bisa doka, kuma wasan yara ne. Hasali ma fata mu ke Allah ya ba shi shugabancinta na Kasa baki daya, amin.

“A karshe, Majalisar kasa ta yi mawafaka da duk abinda Majalisar Kano ta tsaya a Kai. Alhamdu Lillah.”

Continue Reading

Hausa

Tijjanawa ba sa goyon bayan nadin Pakistan shugaban Majalisar Malamai – Alkarmawi

Published

on

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

 

 

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم 

وصلي الله علي النبي الكريم 

Majalisar Malamai ta jihar Kano tana da mahimmanci ga Musulmin Arewacin Nigeria gaba daya ba Kano ba kawai, don ko ba komai Al’ummar Musulmi suna kara samun hadin kai da magana da murya daya sanadiyar wannan majalisar kuma babban abun bukata shine hadin kan Musulmi.

Amma sabon shugabanci da akai jiya (Litinin) da aka nada Malam Abdallah Saleh Pakistan (Shugaban Izala na jahar kano) zai iya rusa majalisar ma gaba daya, Saboda Shugabancin yana bukatar malamin da yake Zaune lafiya da duk akidun Musulunci da suke Kano, wanda Pakistan kuwa yana da matsala da wasu bangarorin.

Shawarata kowa a nan shine Asami malamin da yaki da kyakkywar alaka da kowa ya jagoranci Alumma Sai asami kai wa ga gaci.

Don haka a madadin Tijjanawa, gaskiya gabadayanmu musamman na jihar Kano muna sanar da cewa ba ma tare da Shugabacin Malam Abdallah Saleh Pakistan.

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Shugaban Khuddamur Rasul SAW na Afrika

Continue Reading

Hausa

Gamayyar Malaman Kano sun nesanta kan su daga tsige Malam Ibrahim Khalil

Published

on

Sheikh Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Gamayyar Malaman Jihar Kano da suka kunshi jagororin darikun Tijjaniyya da Qadiriyya da kuma Salafiyya sun yi watsi da sanarwar tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin majalisar malamai.

Wata sanarwa da KANO FOCUS ta ci karo da ita dauke da sa hannun sakataren gamayyar Malaman, Dr Sa’idu Ahmad Dukawa ranar Talata malaman sun ce ba da yawunsu aka dauki wannan mataki ba, kuma ba sa goyon bayansa.

Malaman da suka sahale a fitar da sanarwar sun hada da Shugaban Darikar Kadiriyya na Afrika ta Yamma Sheikh Karibullahi Sheikh Nasiru Kabara da Sheikh Abdulwahab Abdallah da Sheikh Ibrahim Sheh Maihula da Dr. Bashir Aliyu Umar da kuma Imam Nasir Muhammad Adam ( Shugaban majalisar Limaman masallatan Juma’a).

Sauran sun hada da Farfesa Musa Muhammad Borodo da Farfesa Muhammad Babangida da kuma Dr. Ibrahim Mu’azzam Maibushira.

Continue Reading

Trending