Connect with us

Hausa

Yadda ake yiwa ‘ya’ya bleaching a Kano tun suna ciki

Published

on

Aminu Abdullahi

Mata da dama masu juna biyu a Kano ne ke yin allura ko shan magani da nufi yiwa ‘ya ‘yan da ke cikinsu bleaching domin su haifosu farare.

A wani bincike da Kano Focus ta yi ta gano yadda galibin matan ke yin wanna mummunar ta’ada domin dai yaransu su zo a farare.

Ita dai wannan dabi’a ta samo asali ne daga kasar Ghana tun a shekara ta 2018.

Haka kuma dabi’ar ta ci gaba da yaduwa a hankali a kasar nan har ta gangaro jihar Kano.

Da hakan tasa matan kan sha magunguna ko allura don yiwa ‘ya’yan dake cikin su bleaching, ta yadda za su zo duniya a matsayin farare.

Magani na haifarwa jariri cutar caner da zuciya

Sai dai Likitoci sun yi gargadi mai zafi dangane da wanna dabi’a ta yiwa ‘ya’ya bleaching a ciki.

Dakta Usman Tijjani Aliyu kwararen likitan fata kuma babban sakataren hukumar kula asibitoci na jihar Kano ya ce magungunan da masu juna biyun ke amfani da su na da illa sosai.

Ya ce magungunan na haddasa ciwon koda, da zuciya, da kwakwalwa da cutar kansa ga jariri, tun yana cikin mahaifiyyar sa.

Ya kara da cewa duk kan cutukan da magungunan ke haddasawa jariri a cikin mahaifiyyarsa, itama uwar tana cikin barazanar kamuwa dasu.

Likitan ya ce su kansu magungunan irin su Glutathione da Hydroquinone da kuma Mercury na raunana kashin mai juna biyu da sanya fatarta ta zama mara kwari.

Hakan na jawo saurin mutuwa

Likitan ya ci gaba da cewa matan dake yin wanna ta’ada sun fi saurin mutuwa ko nakasa yayin da suke da karancin shekaru.

Ya kuma ja hankalin masu juna biyu da su kaucewa yin haka don kare lafiyar su da ta jariran su.

Ra’ayoyin mata

Sai dai wasu mata a nan Kano sun bayyana ra’ayoyinsu kan yiwa ‘ya’ya bleaching tun suna ciki.

Shamsiyya Yusuf ta ce batasan cewa ana yiwa ‘ya’ya bleaching tun suna ciki ba.

Ta ce koda ta san ana yin hakan to zai yi wuya tayi saboda hatsarin da hakan ke dauke dashi.

“Wannan abune mai ban mamaki bantaba jinsa ba sai yanzu,” a cewar ta.

Talatu Hassan ta ce tasan ana yiwa ‘ya’ya bleaching tun suna ciki shekaru hudu da suka gabata.

“A kwai wacce na sani tana yiwa masu juna biyu allura don su haifi “ya”ya farare kuma allura tana yin aiki sosai.

” Koda kuwa miji da matar duk bakake ne idan akayi zaka ga sun haifi yaro fari,” a cewar sa.

Wani mai siyar da kayan kwaliya Abubakar Abdul’aziz da ke unguwar Maidile ya ce yana siyar da wasu daga cikin kayan kwaliyyar da aka ambata.

Sai dai ya ce ko kadan bai san cewa masu juna biyu suna amfani dashi wajen yiwa ‘ya’yan da ke cikin su bleaching ba.

 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil wasan yara ne – Prof. Alkafawy

Published

on

Malam Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Majalisar Malamai ta Kasa ta bayyana yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta Jihar Kano da cewa wasan yara ne.

A wata sanarwa da KANO FOCUS ta samu Mai dauke da SA hannun Sakataren Kungiyar Farfesa Muhammad Sadik Alkafawy ya sanyawa hannu ranar Alhamis ta ce abun da aka yi ba ya bisa doka.

Ga cikakkiyar sanarwar:

“Majalisar  Malamai ta Kasa ta sami labarin yunkurin wata jama’a da ke kiran kanta Malamai, amma ta bari wasu wadanda ba su nufin alheri su yi amfani da su a kawo baraka tsakanin jama’ar Musulmi. Wannan abin takaici ne.

“Tun daga ranar da a ka assasa Majalisa zuwa yau ba a taba samun tabargaza irin wannan ba. Don haka Majalisa ta Kasa na yin kira ga wadannan mutane su tsoraci Allah su kauce ma son zuciya.

“Hakika Majalisar Malamai reshen jihar Kano ta yi daidai da tace wadanda su ka shiga wannan bankaura ba ‘ya’yanta ba ne tun daga jiha balle na Kasa. Yaya za a yi wanda ba ya cikin Majalisa ya ce ya kori wanda a ka kafa Majalisa da shi?.

“A wurin Majalisa ta Kasa abinda a ka yi ba ya bisa doka, kuma wasan yara ne. Hasali ma fata mu ke Allah ya ba shi shugabancinta na Kasa baki daya, amin.

“A karshe, Majalisar kasa ta yi mawafaka da duk abinda Majalisar Kano ta tsaya a Kai. Alhamdu Lillah.”

Continue Reading

Hausa

Tijjanawa ba sa goyon bayan nadin Pakistan shugaban Majalisar Malamai – Alkarmawi

Published

on

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

 

 

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم 

وصلي الله علي النبي الكريم 

Majalisar Malamai ta jihar Kano tana da mahimmanci ga Musulmin Arewacin Nigeria gaba daya ba Kano ba kawai, don ko ba komai Al’ummar Musulmi suna kara samun hadin kai da magana da murya daya sanadiyar wannan majalisar kuma babban abun bukata shine hadin kan Musulmi.

Amma sabon shugabanci da akai jiya (Litinin) da aka nada Malam Abdallah Saleh Pakistan (Shugaban Izala na jahar kano) zai iya rusa majalisar ma gaba daya, Saboda Shugabancin yana bukatar malamin da yake Zaune lafiya da duk akidun Musulunci da suke Kano, wanda Pakistan kuwa yana da matsala da wasu bangarorin.

Shawarata kowa a nan shine Asami malamin da yaki da kyakkywar alaka da kowa ya jagoranci Alumma Sai asami kai wa ga gaci.

Don haka a madadin Tijjanawa, gaskiya gabadayanmu musamman na jihar Kano muna sanar da cewa ba ma tare da Shugabacin Malam Abdallah Saleh Pakistan.

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Shugaban Khuddamur Rasul SAW na Afrika

Continue Reading

Hausa

Gamayyar Malaman Kano sun nesanta kan su daga tsige Malam Ibrahim Khalil

Published

on

Sheikh Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Gamayyar Malaman Jihar Kano da suka kunshi jagororin darikun Tijjaniyya da Qadiriyya da kuma Salafiyya sun yi watsi da sanarwar tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin majalisar malamai.

Wata sanarwa da KANO FOCUS ta ci karo da ita dauke da sa hannun sakataren gamayyar Malaman, Dr Sa’idu Ahmad Dukawa ranar Talata malaman sun ce ba da yawunsu aka dauki wannan mataki ba, kuma ba sa goyon bayansa.

Malaman da suka sahale a fitar da sanarwar sun hada da Shugaban Darikar Kadiriyya na Afrika ta Yamma Sheikh Karibullahi Sheikh Nasiru Kabara da Sheikh Abdulwahab Abdallah da Sheikh Ibrahim Sheh Maihula da Dr. Bashir Aliyu Umar da kuma Imam Nasir Muhammad Adam ( Shugaban majalisar Limaman masallatan Juma’a).

Sauran sun hada da Farfesa Musa Muhammad Borodo da Farfesa Muhammad Babangida da kuma Dr. Ibrahim Mu’azzam Maibushira.

Continue Reading

Trending