Hausa
Raddi kan kalaman Sheikh Abduljabbar Kabara -Farfesa Ahmad Murtala
Bismillahir Rahmanir Rahim
Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga Annanbinmu Muhammad da Alayensa da Sahabbansa baki daya.
Bayan haka, a yau Litini, Ranar Arfa, 09 na watan Zul-Hijja, 1442 H.-19 July, 2021 M., zan amsa tambayoyin da a ka yi ta turowa a wadannan kwanaki, wasu kuma suka yi ta bugowa bayan titsiyen da malaman Jihar Kano suka yi wa Abduljabbar Nasiru Kabara a rananr Asabar 10 ga watan July, 2021- 28 ga Zul-Ka’adah, 1442, game da tuhumomin cin zarafi da tawaye hakkin Annabi (S.A.W) da suka bayyana a cikin karatukan sa. A kan wadannan tambayoyi aka rubuta wannan bayani. Amma wanda yake so ya fahimta abin da aka rubuta da kyau sai ya daure ya karanta bakai daya. Allah ya bamu sa’a da dacewa.
1-Ya tabbata, ko kokwanto ba bu, cewa Abduljabbar ya yi karatuka da yawa wadanda a ciki yake karyata hadisai na Sahihul Bukhari da Muslim da sauran littafan hadisai haka da ka, ba tare da ya bi tsari da hanyoyi na ilimi, wadanda masana Hadisin Annabi (S.A.W) suke bi su auna hadisai domin tantance ingantattu daga marasa asali tushe ba. Zamu kawo kadan daga irin abin da yake fada domin a gane irin bayanan da zasu zo nan gaba:
i-Ya ce, “Kai mafi inganci na biyu ma shi ya ruwaito 1365, 1428…Fyade ne Annabi ya yi wa Nana Safiyya, daraja ta daya fyaden…”
“بل روى صاحب الأصح الثاني، كتاب النكاح: باب فضيلة إعتاقه أمته ثم يتزوجها.. أن اغتصاب النبي لصفية كان اغتصابا بالدرجة الأولى”.
ii-Ya ce, “Wata mace ta zo gun Manzan Allah, فعرضت عليه نفسهاko! تعرض عليه نفسهاTa zo tana yi masa kwarkwasa, shi ne bijirar da kai ko? Shi ake cewa kwarkwasa ko? يا رسول الله إن لي إليك حاجة Ina sha’awarka. فقال: أم فلان! انظري أي السكك شئت حتى أقضي حاجتك Ummu Fulan fa Ummu Sulaimin fa kenan, karara babarsa yake nufi, ta je ta ce da Annabi tana sha’awarsa, kuma ya ce jeki ki nemi gu ki jirani, zan zo na biya miki bukatar ki فخلا معها في بعض الطرق حتى فرغت من حاجتها ya je ya sameta a inda ta buya ya biya mata bukatarta. A Bukhari da Muslim…Na fito muku da hanyoyin da suke tabbata wannan hadisi nama ita wannan mata baa san wacece ce ba. Babban dalili kan cewa kirkirarran labari ne, har yau ba a san wacece ba. Duk da girman abun! Matar da har zata zo ta fidda Annabi daga gida, ya bita kwararo, ya je ya yi mu’amalla da ita, ta da namiji da mace da ita. Amma yau duk ka hadasu ba su an sunanta ba”.
iii-Ya ce, “Ko jiya an turo min, sun yi zanen Ma’aiki da Nana Sauda maganar hijabi. Sun saki. Ga Umar, wai yana wa Annabi fada, ta fito tumbir sai bireziya. Ka san haka yake a ciki wai ba a suturcewa…Ita ayar hijabin ba ita ba ce Anas ya ce yana dakin Nana Zainab ta sauka ba. Kuma yana Bukhari. Kuma Bukharin nan ya kuma ruwaito wa mutane wannan tabarar. Ga ta yau a Faransa an yi Katun na Ma’aiki. Dama abin da muke fada kenan. Kuma duk ku rubuta sauran hadisan nan suna tafe kansu. A Bukhari aka rubuta Annabi ba ya tsare matansa, Umar ne ya tilastashi. Sannan wahayi ya sauka aka hanashi, yake wa matansa fada. Sannan dole wahayi ya zo ya sa shi ya suturce su. Yawo suke yi kamar ‘yan mami market, haka yake a Bukhari. Kuma fa yana Bukharin nan fa Anas yana cewa duk yana cikin marawaitan wannan karyar ta daga Umar da sauke Ma’aikin Allah, cewa Annabi ba ya kula da suturce matansa sai da Umar ya casa shi…”.
Na kawo misalai uku ne kurum daga ingatattun hadisan da suka shafi littafan Bukhari da Muslim, wadanda Abduljabbar yake karyatawa. Amma Allah shi ne shaida na kawosu yadda ya fadesu a karatukansa.
Akwai kuma audio wanda shi ne aka sanya masa a zaman titsiye ranar Asabar kuma ya tabbar da abin da yake ciki; cewa muryarsa ce kuma shi ya fada! Domin titsiyen a kan wadannan kage-kagen nasa ne, wadanda ya gaza bada amsa sai dai dawurwura!
Saboda takaita yanayin rubutu ban kawo sauran abin da yake fada ba a kan wasu hadisan, ingantattun da raunanan baki daya ba. Su ma suna da yawa. Ga su nan suna tayo a kan kafofin sada zuminci.
2-Ga wanda duk ya saurari abin da Abduljabbar yake fada zai ga salon ta’asa kala-kala a karatukan da maganganun nasa, wadanda suka kunshi abubuwa, a dunkule, kala hudu kamar haka:
i-Za a ga yana karyata ingatattun ruwayoyin hadisan da Imamu Bukhari da Imamu Muslim suka ruwaito a mafiya ingancin littafai bayan Littafin Allah, wadanda malaman Ahlus Sunnah na duniya suka ingantasu tuntuni. Wannan ya hada har da karyata samuwar wasu sahabbai kamar su Anas bn Malik da sauransu, wadanda ya shaci wuri a Filin Mushe, ya sha ruwan sanyi ya zauna yana karyatasu haka da ka!
ii- Wasu ruwayoyin basu da inganci bisa bayanan da masana hadisin suka yi tintini, misali ruyawar da ta siffata yadda aka daura auren Annabi (S.A.W) da Nana Khadija da ruwayar da ta ce Annabi ya sumbaci gaban Alhasan da ruwayar da ta ce ba a binne Annabi (S.A.W) da wuri ba, da saurasnsu. A maimakon ya yi karatu ko ya tambaya a fada masa rashin ingancinsu, shikenan ya guntsa ya fadawa dalibansa cewa wadannan ruwayoyin basu da inganci a wuce wurin. Amma ina!! Sai kurum ya shiga nuna cewa suna da inganci kuma malaman hadisi sun ruwaitosu ne wai don a dangantawa Annabi (S.A.W.) wadannan ruwayoyin a tawayi hakkin Annabi (S.A.W) da gangan! Daga nan sai ya shiga kutuntuma maganganu!
iii-Wadansu ruwayoyin kuma suna da inganci amma sai ya fassarasu da son zuciya, irn halin wanda yake da wata nufaka ga Annabi da Sahabbansa! Ya murguda fassara; abin da ya nuna cewa shi burinsa dai sai an ga Sahabban Annabi (S.A.W) a matsayin wasu mutane na daban, baibai bisa yadda yake fassarawa, amma ba fassarar da malamai suke ba.
iv-Wasu kuma babu wadannan bayanan da yake fada a cikin hadisin ko ta kusa ko ta nesa, kamar misalai guda ukun da aka kawo a sama, sai dai wadannan bayanai a kwakwalwarsa kurum suke. Sai ya fito da su don son ya yi karyar cewa an muzantawa Annabi (S.A.W). Alhali bayanansa su ne suke dauke da danganta muyagun maganganu da sifofi zuwa ga Annabi da Sahabbai ba ainihin hadisan ba!
3-Ga wanda ya karanta tarihi da kyau zai tabbatar da cewa abubuwan da Abduljabbar yake yi bai gaza irin abin da wasu masu tinani irin nasa a can baya suka yi ba. Haka nan abin da suka yi, bai gaza irin abin da yake yi ba. Amma abin da yake tabbatacce a tarihi shi ne cewa ba a taba samun wanda ya bi tafarkin cutarwa da mugustawa ga Annabi (S.A.W) da Sahabbansa ba face Allah ya wulakantashi, ya kaskantashi a kan idon duniya. Misalan da za a kawo suna dada tabbatar da haka:
i-An taba yin wani mutum a lokacin tabi’ai mai suna Amru bn Ubaid, wanda shi ne suka kafa akidar Mu’utazilah. An san shi da cin zarafin Sahabbai da wulakanta sauran malamai. Kadan daga abubuwan da ya rika yi:
a-Wata rana an karanta masa wani ingataccen hadisi na Annabi sai ya kada baki ya ce, “Da zan ji wannan hadisin daga A’amash yana fadarsa, da na ce da shi karya kake! Da zan ji Zaidu bn Wahab ya kawo shi, da ma ko daga kai na kulashi ba zan yi ba! Da zan ji Abdullahi bn Mas’ud yana fadarsa, da ba zan karba ba! Da zan ji Manzon Allah yana bada shi, da na ki karba. Da zan ji Allah ya fadeshi, da na ce da shi, a gaskiya ba a kan irin wannan ka dauki alkawarimu ba.”-(Tarikhu Baghdad na Hafiz Al-Baghdadi:12/170; Siyaru A’alam Annubala’i:6/104).
b-Wannan mutumin dai shi ne mai cewa, “Da Sayyadina Aliyu bn Abi Dalib da Usaman da Dalha da Zubairu, zasu yi shaida a wurinsa a kan wani abu kamar hancin takalmi, da ba zai karba ba!”.-(Tarikhu Baghdad na Hafiz Khadib Al-Baghdadi:12/178).
ii-Haka nan an yi wani mutum mai suna Ahmad bn Yahya da aka fi sani da Ibnu Rawandi (ya mutu:298 H). Shi ma yana sauraran ‘yan Shi’a, yana karanta littafansu. Don haka shubha ta yi masa yawa a kwakwalwarsa. Sai da take ya yi littafi mai suna ‘Addamigu’-wai Littafin da ya wargaje Kur’ani da shi! A cin Littafin ya yi gegare da cin fuska da zagi ga Annabi (S.A.W) sau goma sha bakwai. Sannan ya kara da wasu muyagun tunani irin layin da Abduljabbar ya dauka. Ga misalan wasu daga cikin irin tabargazarsa:
a-Ya ce, da Allah ya ce ‘Hakika kaidin Shaidan ya kasance mai rauni ne’-(Nisa’i:76).
“إن كيد الشيطان كان ضعيفا”
Sai Ibnu Rawandi ya ce, ya ya za a ce kaidinsa yana da rauni bayan ga shi nan don tsananin kaidi ya fito da Annabi Adam daga Aljanna, ga shi kuma duk mutane suna ta wahala da kaskanta saboda kaidin nasa!-( Al-Muntazam na Ibnul Jauzi:6/99-)
b-A wani lokacin kuma yana cewa, dangane da fadar Allah, ‘Duk lokacin da fatunsu suka zagwanye sai mu canza musu wasu fatun daban ba wadannan ba’-(Nisa’:56). “كلما نضجت جلودهم بلدناهم جلودا غيرها”
Sai Ibnu Rawandi ya ce, ‘Ga shi Allah yana yiwa fata azaba, bayan ba ita ce ta yi masa laifi ba!’-(Al-Muntazam na Ibnul Jauzi:6/99).
A karshe dai gwamnati ta sa an tsire Ibnu Rawandi, aka kashe shi a wulakance bai wuce shekara talatin da shida ba.
iii-Ibrahim Sayyar wanda aka fi sani da Annazzam, daya daga cikin shuwagabannin Mu’utazilah a karni na uku (ya mutu:231 H.). Yana daga cikin masu sakin baki ga Sahabban Annabi. An fada masa cewa Abdullahi bn Mas’ud ya ruwaito hadisin tsagewar wata. Ya kuma ce ga yadda watan ya tsage a Makka! Maimakon ya fadi alheri sai Annazzam ya ce karya Ibnu Mas’ud yake! Ta ya ya ma wata zai wani tsage! Shi bai yarda ba, wannan labarin kanzan-kurege ne! Da sauran shegantaku!-(Tawilu Mukhtalafil Hadisi na Ibnu Kutaibah: sh/25)
iv-Ibrahim Al-Fazari wani mawaki ne a kasasr Andalus. Amma sai ya rika amfani da wakensa wajen gegare da cin zarafi ga Annabi (S.A.W), abin da ya bayu a ka sami shaidu sama da mutum talatin suka shaida cewa yana fadar hakan. A nan gwamnan lokacin ya sa aka caccaka masa wuka, aka kone gawarsa.-(Asshifa:2/218; Tartibul Madarik na Alkali Iyad:2/307).
An kawo wadannan misalai ne domin a tabbatar da cewa masu irin halin Abduljabbar tuntuni akwai su. Ba wai shi ne ya fara ba. Kamar yadda gwamnati ta yanke hukunci akan irinsu shi ma ba yau aka soma ba.
4- Abduljabbar ya yi maganganu masu nauyi matuka da da’awar cewa ya fito da su ne daga ruwayoyin da ya tattara guri guda na wasu hadisai. Ma’anar wannan shi ne ya yi tasa fahimtar ta kashin kansa, sannan ya fito da wadannan bayanai, ba wai hadisan ne kai taye suka fadar hakan ba. Amma idan aka duba a nutse za a ga cewa bayanan da yake yi, baki dayansu, sun doru a kan wasu abubuwa guda biyar. Su ne:
i-Rashin fahimtar kalmomin larabci da yadda ake amfani da su: Misalin hadisin mata mai tabin hankali da yake maganar حاجة sai shi Abduljabbar ya mayar da kalmar ta koma شهوة wadda ba ita ake nufi ba a hadisan. Kalmar ‘Haja’ tana nufin wani abu da mutum yake son ya samu ko ya cimma kaiwa gareshi. Allah ya yi amfani da kalmar dangane da Annabi Yu’kub da ya ce, “Sai dai wata bukata a ran Yu’kubu da ya biya ta”- (Yusuf:68) “إِلَّا حَاجَةً فِي نَفْسِ يَعْقُوبَ قَضَاهَا” da fadin Allah dangane da dabbobin ni’ima, “Kuna da wasu amfanukan da su. Sannan don ku sami damar kaiwa ga wasu bukatarku da suke zukatanku”-(Gafir:80). “وَلَكُمْ فِيهَا مَنَافِعُ وَلِتَبْلُغُوا عَلَيْهَا حَاجَةً فِي صُدُورِكُمْ
Amma abin mamaki sai Abduljabbar ya dauko ma’anar kalmar sha’awa ya ce ita hadisin na biyu da muka bada misali a sama, take nufi. Tare da cewa matar ta nuna cewa bukatu ce da ita irin bukatu na matsalolin yau-da-gobe kamar yadda tsarin maganar ya tabbatar. A inda ta ce: “إن لي إليك حاجة”. Wannan shi ne abin da duk ruwayoyin suka kawo. Amfani da kalmar إليك shi ne yake bayyana cewa matsalolinta take so a taimaka mata ta warware mata su! Amma abin mamaki sai ga Abduljabbar yana canza hadisin yana mayar da shi wani abu daban. Duk wanda ya ji karatun zai ji inda ya ce, ‘ta zo ta ce “ألك بي حاجة”- wato “Kana da bukatata!” Haka Abuljabbar ya mayar da waccan kalma da aka kawo tun farko. Yin hakan ba kankanin kuskure ba ne na rashin sanin yadda ake tasarrufi da kalmomin larabci, ya canza shi, ya yi watsi da asalin ruwayar!
Wani abin la’akari kuma shi ne a larabcin asali ba a amfani da kalmarحاجة haka nan yadda take da ma’anar sha’awa شهوةkwata-kwata. Ba a inda larabawan asali suke yin irin wannan gamin-gambizar, sai a dabagar Abduljabbr! Kalmar Sha’awa suna kawota ita da kanta idan ita suke nufi ko wata kalmar da zata dauki ma’anarta. Wanda bai san irin wannan amfani da kalmar ba kamar su Abduljabbar, sai su markade komai wuri daya, su ci da bagu, su wuce kurum ana yi musu ihu wai sun burge a wurin jahilan gari!
Muhimmin abu dai shi ne, Abduljabbar bai san yadda lugar larabci take ba yadda ya kamata. Amma yana da cika-baki da hargagin ana nuna an san komai! Idan da zai yiwa kansa adalci da sai ya daina tabargazar da yake yi. Don ba shi da kwarewa a harshen larabci, wanda saninsa kuma shi ne tushen fahimtar Kur’ani da Hadisai!
ii-Cakuda al’adun Larabawa da na Hausawa: Wani abu wanda yake da alaka da wancan shi ne, Abduljabbar yana cakuda al’adar Hausawa da al’adun Larabawa idan ya zo fassara hadisai. Maimakon ya fassara hadisan a kan yadda al’adun larabawa suke, saboda rashin sani da kokarin rikita lamura sai ya koma ya fassarashi da yadda Hausawa suke daukar abubuwa. Wani lokacin ma a kan al’ada irin ta maguzawan Hausawa!
Misali, Abduljabbar ya yai maganar mayafi ko gwadon da Abuhuraira yake yafe da shi. A lafazin hadisain ya ce, ‘sai ya shinfida wani gwado, wanda ba ni da wani tufafin a jikina, sai shi” “فبسطتُ نمرةً ليس عليّ ثوب غيرها”
A nan sai Abduljabbar ya dauka hausawa ne suke magana. Domin bai san cewa kalmarنَمِرة tana nufin gwado guda daya babba, wanda mutum zai iya daura wani bangaren nasa ya kuma yi duk abin da yake so da daya bangaren ta fuskar yafa shi ko idan yana so ma zai iya mayar da shi ya zamo abin rufa idan zai kwanta, da sauransu. Don mutum ya shinfida wannan bangaren, al’aurarsa ba zata bayyana ba. Ba wai dan karamin mayafi ba ne, wanda idan a ka cireshi shi komai zai iya bayyana ba. Shi kuma Abduljabbar cewa yake, “wai zigidir yake haihuwar uwarsa a gaban Annabi”. Wannan kuskure ne. Larabawa suna da mayefai kala-kala. Akwai guda daya. Akwai kuma guda biyu da za a yafa daya a daura daya. Suna kiran wannan da sunan حُلّة. Rashin sanin wannnan al’adar ta Larabawa yasa Abduljabbar ya yi irin wannan tabargazar a fassara!
iii-Kirkiro mummunar fassara mara tushe: Wata matsalar da Abduljabbar ya fada cikinta zundum ita ce yadda yake zarce iyaka da daukar ruwayoyin a kan mummunar fassarar ga hadisan Annabi (S.A.W.) haka nan da ka, ba tare da wani malami magabaci ya taba yin irin wannan fassarar ba. Duk mutum mai imani idan abu ya shafi Annabi (S.A.W.) yana kaffa-kaffa kada ya kirkiro wata fassara ko magana ta kashin kansa, mara asali ya dangantata da Annabin! Domin yanzun nan sai mutum ya fice daga Musulunci bai kula ba. Sannan malamai na Allah suna jan hankali daliban ilimin cewa duk abin da ya shafi irin wannan bangare, sai mutum ya bada wata fassara, to ya zamo yana da wata madogara cikin manyan malamai magabata. In ba haka ba mutum zai kwafsa! Imamu Ahmad bn Hambal ya ce, “Kada ka kuskura ka yi magana a kan wata mas’ala, alhali baka da wata madogara akanta daga wani babbabn malami”-(Manakibu Ahmad na Ibnul Jauzi: sh/178)
قال الإمام أحمد بن حنبل-رحمه الله-:”إياك أن تتكلم في مسألة ليس لك فيها إمام”
Duk ruwayoyin da Abduljabbar yake kawowa, da fassarorin da yake fada shi kadai yake yin irinsu, shi ya kirkiresu ba haka malamai suke fassarawa ba. Saboda me zai kirkiro tasa!!?
Sayyadina Aliyu bn Abi Dalib yana cewa, “Idan aka fada muku hadisi daga Annabi (S.A.W), to ku yi masa tunani mai kyau, mafi nuna shiriya, kuma mafi takawa”-(Sunanu Ibn Majah, L:20)
قال علي بن أبي طالب-رضي الله عنه-:”إذا حُدّثْتُم عن رسول الله صلى الله عليه وسلم حديثا، فظنوا به الذي هو أهيَاه، وأهْدَاه، وأتْقاه”.
iv-Amfani da muyagun kalmomi a wajen sifata Annabi: Duk wanda ya saurari abin da Abduljabbar yake fada zai tabbatar da cewa mutumin nan yana sakin baki ga Annabi da Sahabbansa da kalmomin ‘yan-tasha na cin zarafi da tawaye hakkinsu. Wannan a bayyane yake a cikin abubuwan da yake fada. A duba a ga irin wadannan muyagun kalmomi na rashin arziki da ya iya fada yana tunanin Annabi a zuciyarsa! Ko ina imaninsa yake a lokacin! Ga shi dai ya ce, “Annabi dan giya ne”; “fyade kenan”; “irin wannan kokarin maida Annabi langwai, mata-maza, surkududu”! Shin akwai bukatar sai Abduljabbar ya yi amafani da irin wadannan kazaman kalmomin sannan zai ce wata ruwaya karya ce a wurinsa!?
Dangane da Sahabbai kuma ga abin da yake fada game da Anas bn Malik (R.A.). Wai “Anas ya kaskanta mutumcin Ma’aiki”; “yana nuna Annabi mugun matsoraci ne”; “Anas ya kuma kirkirowa”; “Anas yake sukuwa irin wannan yana zamiya”, da sauransu.
Wannan rashin ladabi a magana shi kansa matsala ce babba, wadda Allah ba zai bar Abduljabbar ya sha da ita ba! Kamar yadda Allah bai bar Macron, Shugaban Kasar Faransa, ya sha ba, sakamakon maganganu na cin zarafi ga Annabi (S.A.W.) sai da Allah ya aiko wanda ya wanka masa mari daga cikin mutanensa!
v-Karyar tattara ruwayoyi da yawa wuri daya: Abduljabbar ya gwanance a zuba karyar cewa yana hada ruwayoyi da yawa wai don ya sami damar fito da karyar da aka yiwa Annabi (S.A.W). Wannan duka ba bu tushe a abin da yake fada! Domin dalilai sun nuna ba ya ma iya fahimtar ilimin ballantana ma ya iya tantance ruwayoyin! Yana cakuda ruwayoyi mabambanta, ya zo ya ce wannan cigaban wacce ce, tare da cewa ba su da wata magama ko alaka! Misali ruwayar da ya kawo ta matar da ta ce tana da bukatar zata gana da Annabi. Sai ya nuna ya tattaro hanyoyinta a Sahihul Bukhar da Sahihu Muslim. Bayan a hakika ruwayar ba bu ita a Sahihul Bukhari. Muslim ne kurum ya ruwaitota. Ruwayar da take cikin Sahihul Bukhari (L:5120) ta shafi wata mata da ta zo ta ce tana son Annabi ya aureta, wadda bata da wata alaka ko ta kusa ko ta nesa da wancan hadisin na matar da take neman a taimaka mata a matsalolinta na yau-da-gobe! Wannan misali ne a bayyane na irin aika-aikar da Abduljabbar yake yi da sunnan hada hanyoyin hadisai!
عن ثابت البناني قال : كنت عند أنس وعنده ابنة له قال أنس جاءت امرأة إلى رسول الله صلى الله عليه وسلم تعرض عليه نفسها قالت يا رسول الله ألك بي حاجة؟ فقالت بنت أنس ما أقل حياءها! واسوأتآه واسوأتآه! قال: هي خير منك. رغبت في النبي صلى الله عليه وسلم فعرضت عليه نفسها”.
Abin da ya rudi Abduljabbar kuma shi ne yake nuna cewa bai san ma yadda ake hada hanyoyin hadisai ba, ita ce kalamar “ألك بي حاجة” sai ya dauka wannan irin waccan da aka fada a daya hadisin ce. Bayan ba haka ba ne. Wannan tana nufin shin kana da bukatar ka aureni!? To amma don Allah ya tona asirin masu karya, sai Abduljabbar bai gane ma abin da ake nufi! Duk da haka ya tafi yana ta zagin Anas a bayanansa!
Bayan haka, idan Abduljabbar gaskiya ya taka menene ya hana ya dauko ruwayar da Musnadu Ahmad (L:14078) da Ibnu Hibbana (L:4527) da Musnadu Abi Ya’ala (L:3472) da sauran littfan hadisai da suka ruwaito wadda ta bayyana cewa matar nan wasu bukatu ne na yau-da-gobe, matar take neman tallafin Annabi don ta samu ta zartar da su. Ga ruwayar: Daga Anas ya ce, wata mata wadda akwai wani abu a hankalinta ta ce: Ya Rasulallah ina da wata bukata?! Sai ya ce, Ya Ummu Fulan ki duba duk inda kike duk hanyar da kike so na zo! Sai ya je ya tsaya tare da ita, ya gana da ita, har ta sami biyan bukatarta”. Wannan lafazin Musnadu Ahmad ne.
“عن أنس أن امرأة كان في عقلها شيء فقالت : يا رسول الله إن لي حاجة فقال يا أم فلان انظري إلى أي الطريق شئت. فقام معها يناجيها حتى قضت حاجتها”.
Wadannan bayanai a dunkule su ne suke nuna irin tsarin da Abduljabbar ya dauka, tsari ne na tawaye hakkin Annabi da Sahabbansa. Ba wai sai ya nufaci cin zarafin kai tsaye ba.
5-Akwai dalilai masu yawa da suke nuna cewa maganganun Abduljabbar sun kunshe matsalolin da aka fada a karkashin lamba ta 4. Idan muka yi la’akari da wadannan dalilai zamu dada tabbatar da cewa lallai ya ci zarafin Annabi. Ga yadda suke:
i-Allah ya ce, “Ya ku wadanda suka bada gaskiya, kada ku daga sautinku sama da sautin Annabi, kada kuma ku bayyana masa magana kamar yadda wasunku suke bayyanawa wasu, gudun kada ayyukanku su rushe ba tare da kun sani ba. Hakika wadanda suke runtse muryoyinsu a wurin Manzon Allah, wadannan Allah ya jarrabi zukatansu da yin takawa, suna da gafara da lada mai girma. Hakika wadanda suke kiranka ta bayan daki, yawancin wadannan ba su da hankali”-(Al-Hujurat:2-4)
“يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَرْفَعُوا أَصْوَاتَكُمْ فَوْقَ صَوْتِ النَّبِيِّ وَلَا تَجْهَرُوا لَهُ بِالْقَوْلِ كَجَهْرِ بَعْضِكُمْ لِبَعْضٍ أَنْ تَحْبَطَ أَعْمَالُكُمْ وَأَنْتُمْ لَا تَشْعُرُونَ. إِنَّ الَّذِينَ يَغُضُّونَ أَصْوَاتَهُمْ عِنْدَ رَسُولِ اللَّهِ أُولَئِكَ الَّذِينَ امْتَحَنَ اللَّهُ قُلُوبَهُمْ لِلتَّقْوَى لَهُمْ مَغْفِرَةٌ وَأَجْرٌ عَظِيمٌ. إِنَّ الَّذِينَ يُنَادُونَكَ مِنْ وَرَاءِ الْحُجُرَاتِ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْقِلُونَ”-(الحجرات:2-4)
ii-Allah ya jawo hankalin Muminai a bayyane cewa a girmama Annabi (S.A.W) da cewa, “Don ku yi imani da Allah da Manzonsa, ku taimaka masa, kuma ku girmamashi”-(Al-Fatah:9) “لِتُؤْمِنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ وَتُعَزِّرُوهُ وَتُوَقِّرُوهُ”
Wadannan ayoyi kadan ne daga cikin ayoyin da suke koyawa Musulmi yadda za a yi ladabi ga Ma’aikin (S.A.W). Bayanan da suka kunsa ya kuma shafi cewa lallai a girmama Annabi yana raye ko baya raye. Idan har Abduljabbar so yake ya kare mutumcin Annabi ya kamata ya nemi kalmomin da suka dace ya yi amfani da su. Ba wai ya rika cewa ‘a buge aka daurawa Annabi aurensa na fari’; ‘Yake rayuwa kamar bamaguje a cikin iyalinsa. Ba shi da tsarin hatta kwanciya kamar yadda bunsuru yake a garke haka Ma’aiki yake’; ‘A dakin matar aure. A ina? A gadonta! A ina? Kan cinyarta!”; da sauransu-wai so ake a kore wadannan daga Annabi! Anya! Amma a dubi irin yadda aka fadesu gatse-gatse! Kalmomin ba bu haske a kansu, ba alamun risinawa da mutumtawa da kankan da kai ga Manzon Allah kamar yadda Allah ya nemi a yi da cewarsa وتوقروه””.
A hakika ko so mutum yake ya karyata wadannan ruwayoyi, ya bayyana ba gaskiya ba ne su, ai ya wajaba ya san maganar ta shafi Annabi, don haka sai ya yiwa bakinsa linzami, ba wai ya zamo mahaukaci ba. Mu duba mu ga yadda masana hadisai suke bayanin ruwayoyin karya a cikin littafansu! Ba za a ga sun bi irin wannan tsarin na rashin ladabi a magana ba. Mutum ya duba Littafin Al-Maudu’at na Ibnul Jauzi’ ko ‘Al-La’ali’ Al-Mas’nu’ah’ na Imamu Suyudi, da sauransu, zai ga irin yadda suke bayanin ruwayoyin karya, ba da irin wadannan kalmomin na rashin arziki ba!
Imamu Ibnul Arabi Al-Maliki ya yi bayani mai gamsarwa a kan wannan ayar. Ga abin da ya ke cewa, “Alfarmar Annabi (S.A.W) duk daya ce, yana raye da bayan rasuwarsa. Maganarsa da aka ruwaito bayan rasuwarsa dole a daukakata kamar maganar da aka ji daga lafazinsa take. Idan aka karanta maganarsa, to dole duk wanda yake wurin kada ya daga muryarsa, kada kuma ya kawar da kai. Kamar dai yadda ya zama dole mutum ya yi a majalisin Annabi (S.A.W) a loakcin da zai ji shi yana furta wannan maganar. Allah Madaukaki ya fadakar a kan cewa wannan alfarmar zata wanzu har abada a duk lokuta, a inda ya ce, ‘Idan ana karanta Kur’ani ku yi shiru, ku saurara’. Abin la’akari shi ne maganar Annabi (S.A.W) ita ma bangare ce ta Wahayi. Tana da alfarma irin yadda Kur’ani yake da shi, sai dai wasu ‘yan abubuwa da aka yi bayani a littafan Fikihu”-(Ahkamul Kur’an na Ibnul Arabi Al-Maliki:4/; A dada duba Tafsirin Ruhul Ma’ani na Al-Alusi:13/290)
قال ابن العربي المالكي:”حرمة النبي صلى الله عليه وسلم ميتا كحرمته حيا، وكلامه المأثور بعد موته في الرفعة مثل كلامه المسموع من لفظه ؛ فإذا قرئ كلامه وجب على كل حاضر ألا يرفع صوته عليه، ولا يعرض عنه، كما كان يلزمه ذلك في مجلسه عند تلفظه به. وقد نبه الله تعالى على دوام الحرمة المذكورة على مرور الأزمنة بقوله تعالى:”وإذا قرئ القرآن فاستمعوا له وأنصتوا”. وكلام النبي صلى الله عليه وسلم من الوحي وله من الحرمة مثل ما للقرآن إلا معاني مستثناة، بيانها في كتب الفقه”.
Rashin jan linzami da tsayar da mutum a iya iyakanrsa da hanashi ci gaba da irin wannan ta’asa da Abduljabbar yake yi, yana dada cusa shi cikin bata. Irin wannan shi ne abin da Sheikh Ibnu Ashur ya yi ishara gareshi da cewa, “Rashin barin munana ladabi ga Manzon Allah yana sawa rai ya saba da wuce gona-da-iri a yin hakan. Mutum ba zai gushe yana yin hakan ba har sai girmama Annabi (S.A.W.) ya rika raguwa a ziciyarsa. Sai mutum ya koma daga mummuna ya zarce zuwa wanda ya fishi muni. Har a karshe ya tike da rashin damuwa da yin ladabi ga Annabi baki daya. Wannan kuma kafirci ne. Wannan shi ne ma’anar fadin Allah, ‘Ku baku sani ba’-shi ne saboda wanda yake curuwa daga mummuna yanayi zuwa wanda ya fi muni, ba zai kula ba cewa ya fara nisa cikin munanan muyagugun abubuwansa ba (na maganganu da ayyuka), sakamakon sabawa da ya yi har kuma sabon ya dilmiya shi cikin halaka. In ba a yi sa’a ba ya zamo kafirci shi ne karshen lamarinsa a lokacin da ransa ya ci gaba da kutsawa cikin irin wadannan muyagin maganganu da ayyuka”-(Attahriru Wat Tanwiru na Ibnu Ashur:28/185)
قال الإمام ابن عاشور:”وأقول: لأن عدم الانتهاء عن سوء الأدب مع الرسول صلى الله عليه وسلم يعود النفس بالاسترسال فيه. فلا تزال تزداد منه وينقص توقير الرسول صلى الله عليه وسلم من النفس، وتتولى من سيء إلى أشد منه حتى يؤول إلى عدم الاكتراث قل بالتأدب معه وذلك كفر. وهذا معنى”وَأَنْتُمْ لا تَشْعُرُونَ”. لآن المنتقل من سيء إلى أسوأ لا يشعر بأنه آخذ في التملي من السوء بحكم التعود بالشيء قليلا حتى تغمره المعاصي .وربما كان آخرها الكفر حين تضرى النفس بالإقدام على ذلك”.
Wannan bayani kamar yana bayyana yadda Abduljabbar ya taso da gwasale malamai har yake zuwa irinsu Imamul Bukhari, ya tsallaka zuwa irinsu Imamu Malik, ya kai zuwa ga Sahabbai. Duk wadannan kuma suka zamo wani tsani da zai ta sirfa maganganu ga Annabi da Sahabbansa! Wa’iyazu Billah!
iii- Wani abu da zai dada sawa a gane cewa Abduljabbar ya tafka ta’asa a game da hakkin Annabi (S.A.W.), bai yi ladabi gareshi ba shi ne hadisin Anas bn Malik (R.A.) wanda ya ce, “Wani mutum ya kira wani a makabartar Baki’a’, ya ce, Ya Abal-Kasim! Sai Annabi ya waiwaya-ya dauka shi ake kira-. Sai mutumin ya ce, ba kai nake nufi ba! Daga nan sai Annabi (S.A.W) ya ce, ‘Ku sa suna irin nawa, amma kada ku sa alkunya irin tawa’”-(Bukhari, L:2121).
“عن أنس رضي الله عنه دعا رجل بالبقيع يا أبا القاسم فالتفت إليه النبي صلى الله عليه وسلم فقال لم أعنك! قال سموا باسمي، ولا تكتنوا بكنيتي”.
A kan wannan hadisin malamai sun nuna cewa wajibi ne a kaucewa duk wani abu da zai jawo tawaya ga hakkin Annabinmu. Imamu Makrizi ya fito da maganar a fili, baro-baro yadda kowa zai gane da yake cewa, “Dole a kare hakkin Annabi kada a cutar da shi. Tunda Annabi ya amsa kira ga wani mutum da ya kirawo Ya Abal-Kasim, sannan ya ce bai Annabi yake nufi ba, wani mutumin daban yake nufi! Yin hakan kurum ya sa Annabi ya hana a sa alkunya irin tasa, domin kada ya rika cutuwa ta hanyar amsa kiran da aka yiwa wani ba shi ba. Don kada ma munafukai da masau izgilanci su sami damar cutar da shi da yin wulakanci ta hanyar kiransa, idan ya amsa su ce ai ba kai muke kira ba. Don wannan Annabi ya tsare kafar cutar da shi ta kowace fuska!-(Imta’ul Asma’I na Al-Makrizi:14/375)
قال الإمام المقريزي-رحمه الله-:”وحماية عن أذاه إذا كان النبي صلّى الله عليه وسلّم استجاب لرجل نادى: يا أبا القاسم، فقال لم أعنك إنما دعوت هذا! فنهى صلّى الله عليه وسلّم حينئذ عن التكني بكنيته، لئلا يتأذى بإجابة دعوة غيره ممن لم يدعه، ويجد بذلك المنافقون والمستهزءون ذريعة إلى أذاه والإزراء به فينادونه، فإذا التفت قالوا : إنما أردنا هذا لسواه، تعنيتا له واستخفافا بحقه على عادة المجان والمستهزءين، فحمى صلّى الله عليه وسلّم حمى أذاه بكل وجه”.
Abin da za a duba shi ne mutun ya raya a ransa kamar yana gaban Annabi (S.A.W), shin zai iya gudunduma irin wadannan maganaganu! To, matukar ba za a iya yin irin wadannan muyagun maganganu a gaban Annabi (S.A.W.), to lallai in an zo kariya gareshi a zabi kalmomi masu kyau da haske da mutumci a fada! Rashin yin haka shi ne cin zarafin gareshi – Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gareshi-. Duk wanda ya san ba zai iya sirfa irin wadannan maganganu a gaban Annabi da yana da rai, saboda cin fuska ne, to ya wajibinsa ne ya kiyaye ko da baya ganin Annabi a gabansa, ya yi kalmomi masu kwarjini da haske, ba na wuakanci irin na Abduljabbar ba!
Wadanda suke cewa Abduljabbar misalai kurum ya ke fada, don yana amfani da Kalmar “kamar” da sauransu, su sani cewa matsalar tasa daman a daidai bada wadannan misalan take! Domin ba a kafa mummunan misali irin wannan da Annabi (S.A.W). Duk abin da ya shafeshi ana kafashi ne da abu mai kyau da tsarki, mai dadin ji kawai! Zancen cewa misalai ne don a kore irin wannan tunanin ma bai taso ba. Imamu Ibnu Rushd (Kakan) ya kawo kissar Umar bn Abdul’aziz da cewa, “Umar bn Abdul’azi ya fadawa wani mutum cewa: a nemo mana wani sakatare, amma wanda mahaifinsa yake balarabe! Sai wani sakataren daban da yake wurin ya ce, Ah! amma ai mahaifin Annabi (S.A.W) kafiri ne! Sai Umar bn Abdul’aziz ya ce, wato ka sanya wannan ya zamo ya zamo misali kenan! Take sai ya cire shi. Sannan ya fada masa cewa ba zaka kara zama sakatare na ba har abada”! A kan wannan kissa, Imamu Ibnu Rushd ya yi ta’aliki da cewa, “Wannan saboda Allah Madaukaki ya yi umarni da a girmama Annabi (S.A.W) da risinawa da mutumtawa da kankan da kai ga Annabi. Duk wanda ya buga wani misali da Annabi a irin wadannan abubuwa, to ya sabawa abin da Allah ya iyakanta na umarnin lallai a girmamashi da risinawa da mutumtawa da Kankan gareshi. A kan haka, mutum ya cancanci a ladabtar da shi, a koya masa ladabi”-(Al-Bayanu Wat Tahsil na Ibnu Rushd- Kakan: 16/396-399)
قال الإمام ابن رشد الجد-رحمه الله-:”روي أن عمر بن عبد العزيز قال لرجل: أنظر لنا كاتباً يكون أبوه عربياً ، فقال كاتب له قد كان أبو النبي كافراً، قال له جعلت هذا مثلاً فعزله. وقال لا تكتب لي أبداً، وهذا لأن الله تعالى أمر بتعزيزه وتوقيره ، فمن ضرب به المثل في مثل هذا فقد خالف حد الله فيما أمر به من تعزيزه وتوقيره ، فوجب عليه في ذلك الأدب”.
Wannan bayani nasa a fayyace yadda abubuwa suke a wajen masana. Yana kuma daga abin da ya sa aka fada, aka nanata cewa Abduljabbar ya cancanci hukunci daidai da irin gatsalin da yake yi a maganganun da ya fuskanci Annabi da su!
6-Sai dai har yanzu akwai wadanda suke ganin kamar Abduljabbar yana da uzuri na tawili cewa shi dai bai nufaci Annabi (S.A.W.) da maganganunsa. Shi cewa yake wadannan hadisai suna nuna Annabi zai iya zamowa kaza! Ko kuma hadisan susuranta Annabi da wata irin sura. Don haka gwara a karyatasu kurum a huta!
Wannan yunkuri na wanke Abduljabbari ba abin karba ba ne. Saboda dalilai masu yawa. Ga kadan daga cikinsu:
i-Abubuwan da yake karyatawa Hadisai ne na Annabi (S.A.W.). yawancinsu ma daga Sahihul Bukhari da Muslim. Wadannan littafai tun da aka yi su gwarazan malamai, hanshakai a sanin ililmin hadisi irinsu Abu Zur’ah Arrazi, Abu Hatim Arrazi, Abu Mas’ud Addimashki, Imamu Darkudni, Abu Zarr Al-Harawai, Abu Ali Al-Jayyani, Ibnu Hazm, da sauransu suka duba su da kyau ta hanyar da aka sani na wannan ilimi suka tabbatar da cewa lallai an tato ruwayoyi masu kyau da inganci. Sun yi magana a kan wasu kwayoyin hadisai akan cewa su ma ingatattu ne amma ba su kai kololuwar da sauran suke kai ba. Wannan ita ce maganar da suka yi akan hadisan kurum. Amma ba karyata hadisan suka yi ba ko suka zargi su Imamu Bukharin da son bata Musulunci ba! Irin wannan muyagun maganganun Abduljabbar ne kadai ya zo yake yinsu a yanzu. Wannan fa tare da cewa bai san komai ba a ilimin hadisi. Don haka ba wata mahada tsakaninsa da wadancan malamai.
Tunda Abduljabbar da ka ya shiga raddin wadannan had isai, ba a kan tsarin ilimin hadisi ba, wane uzuri da tawili za a yi masa, bayan ya na sane ya cusa kansa cikin abin da bai san shi ba. Kuma ya rika fadar magangnau a kan Annabi (S.A.W.) da Sahabbansa.
ii-A hirar da BBC ta yi da Abduljabbar ya fada cewa, “Da ina cewa ba dan Shi’a ba ne ni. Amma yanzu bayan bincike da ya yi zurfi na gane Shi’ar ma ta fi Sunnar Hujjoji. Na ga ba dalilin da za a rika tsoratani da wannan. Duk wanda ya ce mini Shi’a kake sai na tambayeshi menene Shi’a a wurinka. Amsar da ya bani ita ce zata biyo bayan amsar da zan bashi. Idan ya ce zagin Sahabbai? Sai na ce a ina na zagesu har ka nasabtani da Shi’a! Sai ka ga ba amsa. Ina dai fadar abun da ya zo, yadda ya zo. Wannan make-maken da ake yi bana yi Ga Annabi ya fadi ata magana, wasu su fadi wata magana na koma bayansu na bar Annabi. Ba zan iya ba!.Kuma bari in fada maka bincike ya tabbatar mini a 75 Shi’a ta fi sun gaskiya akan rigingimun da ake yi da su. Saba’in da biyar. Ga littafan nan, in da na Shi’a tsirari ne, duk Sunna ne kewaye da ni. Ni ka ce min dan Sunna ma shine damuwata. Ya fi damuna. Ma’anar Ahlus Sunnah ba Sunnar ba, Ahlus Sunnah!”.
Wadannan bayani sun cewa ba wani tawali da za a iya yiwa wanda yake ga irin wannan hukunci ga littafan Ahlus Sunnah. Tunda ya nutsu na Shi’a sun fi gaskiya, dole ya san yadda zai yi ya karyata na Sunnah din! Musamman ma saboda zubi da tsarin abin da yake fada ya tabbata yana tsamosu ne ko ya ‘wanko’ kacokan daga daya daga makiya Sunna da hadisan Annabi (S.A.W). Wato daga littafan Oriestalists (turawa da suke sukan Musulunci) da na Shi’a da na ‘Yan Kala-kato. Wadannan ukun su ne ‘manazartarsa’, a cikinsu kuma yake dabdala da kaiwa-da-komowa! Duk da yana iya bakin kokarinsa kada a gano a ina yake debo maganganu! Amma tsarin yadda suke cin zarafin Annabi sak shi ma shi ya dauka yake maimaitawa!
A kan wannan, a tsaya a duba da kyau a gani wane uzuri ko tawili za a yiwa mai manufa irin wannan mummunar manufa.
iii-Wane tawali Abduljabbar yake da shi bayan ya makalewa maganganun ‘yan Shi’a da arna masu kokarin karanta Musulunci don su kawo masa tarnaki (Orientalists)! Misalin cin zarafi da karyata Anas bn Malik (R.A.) da dauka cewa kwata-kwata ma ba a taba yin wani mutum wai shi Anas bn Malik a cikin sahabbai ba, ra’ayi ne da ya cakuda akidar Shi’a ta zagi da zinuwa ga Anas bn Mali da kuma ra’ayin wani bature wais hi G.H.A. Juynboll wanda shi ne farkon wanda ya fara kokwanton samuwar Anas bn Malik. Daga nan ne wasu ‘yan Shi’ar zamani suka dauka suka café har Abduljabbar ya sami nasa kason na barna! Shi kuma wai hujjarsa a kore samuwara ita ce wai ba a kawo magana a kan Anas bn Malik ba a cikin Littafin Maghazi na Muhammad bn Ibnu Is’hak! A tunanin Juynboll duk wanda ba a fada a cikin Littafin ba, to ba bu shi! Wannan shirme ne a ilimi da kasala a bibiyar littafai! A yaushe wani littafin guda daya cikin irin littafan farko ya kunshe duk abubuan bukata da ruwayoyin da mutanenda suka yiwa Annabi hidima!?
Rashin karbar tawalin da za a yiwa Abduljabbar shi ne duk littafan Musulunci cike suke da tabbatar da samuwar Anas bn Malik a matsayin wanda ya yiwa Annabi hidima shekara goma. Sannan ya ruwaito dimbin hadisai daga Annabi (S.A.W). Ta ya ya wani zai dorawa kansa makanta ba-gaira-ba-dalili don ya kore samuwar wannan babban Sahabi!! Allah ya saka masa da alheri bias hidima da tsayawa da ya yi wajen ruwaito hadisan Annabi da koyar da su! Kalubaken da muke jafawa Abduljabbar da ‘yan badarandar turawa da Shi’a shi ne in sun isa masu bincike, su kawo wani malami magabaci kafin wannan arnen Juynboll wanda ya karyata samuwar Anas bn Malik!?
iv-Zamu dada gane cewa ba za a iya daukar maganar Abduljabbar a kan tawaili ba. Saboda Ahmad bn Abi Sulaiman dalibin Imamu Suhnu ya yi magana a kan wani mutum da aka yi masa magana kan wani abu, sai mutumin ya ce, a a! na rantsa da girman Manzon Allah! Sai mutumin ya kara da cewa: Allah ya yi maganin manzon Allah! Sannan ya fadi ta maganar mara kyau! Sai aka ce masa me kake fada ne makiyin Allah! Sai ya fadi wata magana mafi muni a kan ta farko, sannan a karshe ya ce, ai shi abin da yake nufi da manzon Allah shi ne: kunama! A nan ne Ahmad bn Abi Sulaiman ya ce da wanda ya tambayeshi: ka yi shaida a kansa zan zamo tare da kai-yana nufin cewa a kan a zartarwa da mutumin kisa, da kuma ladan da za a samu bayan haka. A kan wannan mas’ala Habibu bn Rabi’ ya yi ta’aliki a kan wannan maganar da cewa, “Da’awar tawili a kan wannan magana da mutumin a irin wannan bayanannen lafazi ba za a karbeta ba. Saboda maganar da ya yi wulakanci ce, kuma bai daukaka Annabi da ita ba, bai kuma girmamashi da maganar ba. Don haka ne ya wajaba a halatta jijinsa”.-(Subulul Huda War Rashad na Assalihi Asshami:12/24).
قال الإمام الصالحي الشامي نقلا:”قال أحمد بن أبي سليمان صاحب سحنون: في رجل قيل له: لا، وحق رسول الله! فقال: فعل الله برسول الله كذا وكذا وذكر كلاما قبيحا! فقيل له: ما تقول يا عدو الله ؟ فقال أشد من كلامه الأول! ثم قال: إنما أردت برسول الله العقرب! فقال ابن أبي سليمان للذي سأله: اشهد عليه وأنا شريكك – يريد في قتله وثواب ذلك. قال حبيب بن الربيع: لأن ادعاءه التأويل في لفظ صراح لا يقبل، لأنه امتهان، وهو غير معزز لرسول الله صلى الله عليه وسلم، ولا موقر له، فوجب إباحة دمه”.
Wannan bayani ya dada tabbatar da cewa girmama Ma’aikin Allah da gwarzanta lamarinsa shi ake bukata daga Musulmi ba sakin baki da surutai ratata ba! Hukunci yana tabbata ga duk wanda ya fadi wata magana ta suka ko wadda zata bayu zuwa ga izgilanci ga Annabi (S.A.W). Ba wani bambanci ko da gaske aka fadi wannan magana ko kuma da wasa duk daya ne domin ba a girmama Annabi (S.A.W) ba!
v-Zamu dada fahimtar yadda ake kare matsayin Annabi (S.A.W) ba a son a danganta wani abu da zi bayu zuwa yin wani mummunan tunani a kansa a cikin wannan labari na Sayyadina Umar. Abdurrahman bn Abu Laila ya ce, Umar bn Khaddab ya ga Abu Abdulhamid wanda sunansa ‘Muhammad’, wani mutum yana cewa Allah ya yi maka kaza da kaza, yana zaginsa da bakaken maganganu a kansa! Sai Umar ya ce da shi mazo kusa dani ka ji! Sai ya ce, ina ganin Manzon Allah ko cewa- ‘Muhammad’- ana zaginsa saboda kai! Daga yanzu ba za kara kiranka da sunan Muhammad ba matukar ina raye! Sai ya sa masa sunan Abdurrahm!-(Addabakat na Ibnu Sa’ad, L:5820 da 5828)
عن عبد الرحمن بن أبي ليلى أن عمر بن الخطاب نظر إلى أبي عبد الحميد واسمه محمد ورجل يقول له: فعل الله بك يا محمد، وفعل وفعل! سمعه يسبه. فقال: ادن يا ابن زيد! ألا أرى رسول الله- أو قال محمدا- يسب بك! والله لا تدعى محمدا ما دمت حيا. فسماه عبد الرحمن”.
Sayyadina Umar ya nuna kishinsa a kan ya ji ana fadawa wani mai suna Muhammad maganganu, ba wai fa Annabin kansa ba, amma ya kasa daurewa sai da ya dauki mataki! Ina ga wanda zai zo yana kuta maganganu da da’awar wai so yake yake kare Ma’aikin Allah ko ta ina!!
vi-Lamarin Annabi (S.A.W.) ya wuce wasa, amma bari mu sauka kasa sasai a babin tattaro hujja. Ana so mutum ya daina zargin mutuane da irin shirmen da kwakwalwarsa zata raya masa. Har Imam Abu Kilaba ya na fadar magana ta hikima da ta shafi mutum da sauran ‘yan uwansa gamagarin mutne cewa, “ Idan labarin wani abu da ba ka so ya zo maka daga dan uwanka, to ka nema masa uzuri iya yadda zaka iya! Idan baka samo uzurin da zaka yi masa ba, to sai ka ce a ranka, wala’alla yana da uzurin da ni ban sani ba”-(Hilyatul Auliya’ na Abu Nu’aim: 2/285)
الإمام أبو قلابة في قوله:”إذا بلغك عن أخيك شيء تكرهه فالتمس له العذر جهدَك! فإن لم تجد له عذرا، فقل في نفسك لعل لأخي عذرا لا أعلمه”.
Don Allah, duk da ba bu gami, wane uzuri Abduljabbar yake da shi da ba zai kare Annabinsa ba! Duk da cewa duk abin da Annabi ya yi daidai ne, domin an ba shi ikon ya kafa Shari’ah! Amma idan da Abduljabbar gaskiya yake so, kuma in da da hankali ya wahaba a kansa ya kare Annabinsa ta hanyar daukar wadannan ruwayoyi a kan ma’anoni na kusa, masu saukin fahimta da haske!
7-Tuntuni malamai sun yi bayani dalla-dalla akan wanda ya zagi Annabi ko ya ci zarafinsa ko ya tauye hakkinsa da cewa hukuncin kisa ne a kansa. Daidai ne babu kokwanto a kansa, matukar ya tabbata, an tsayar da hujja a kan cewa an yi zagin ko an ci zarafi ko an tawaye hakkin na Shugaba (S.A.W.). Wani mutum ya takurawa Sayyadina Abubakar da magana mai zafi sai Abu Barzata Al-Aslami ya ce barni na kasheshi?! Sai Sayyadina Abubakar ya yi masa tsawa yana hanashi. Sannan ya ce da shi: ai wannan haddi ba wanda za a yi shi don an tabashi bayan Annabi”-(Sunanu Nasa’i:)
عن أبي بَرْزَةَ الأسلمي رضي الله عنه قال: “أغلظَ رجلٌ لأبي بكرٍ الصديق، فقلت: أقتله؟ فانتهرني؛ وقال:” ليس هذا الحد لأحدٍ بعدَ الرسولِ صلى الله عليه وسلم”.
An sami sabani mai rauni kan shin ko za a bawa wanda ya fadawa Manzon Allah Maganganu za a bashi dama ya tuba. Sai wasu malamai a Mazahabin Imamu Malik irinsu Al-Makhzumi da Ibnu Abi Hazim da suke ganin za a bawa Musulmi damar ya tuba.Haka nan ma Yahudawa da Nasara in suka yi zagin. Wannan maganar Imamu Al-Mawwak ya hakaito. Nan da nan kuma ya rugujeta ya kawo abin da yake shi ne mashahuri, sananne a tsakanin malaman Malikiyya shi ne abin da aka ruwaito daga Ibnu Kasim yana cewa, “Hakika wanda ya aibata Manzon Allah za a kasheshi, ba kuma za a nemi tubansa ba. Sannan gadonsa na jama’ar Musulmi ne baki daya. Saboda daidai yake da Zindiki wanda ba za a gane tubansa ta kan harshensa ba. Wannan abu ne da yake can zuciyarsa”-(Attaju Wal Iklil na Al-Mawwak).
قال الإمام المواق-رحمه الله-:”قال المخزومي وابن أبي حازم: لا يقتل المسلم بالسب حتى يستتاب ، وكذلك اليهود والنصارى .وقد تقدم نقل ابن يونس عن ابن القاسم : وإن من عاب رسول الله صلى الله عليه وسلم قتل ولم يستتب وميراثه لجميع المسلمين وهو بمنزلة الزنديق الذي لا تعرف توبته بلسانه ويراجع ذلك في سريرته”.
Ga kadan daga cikin irin yadda malamai suka yi bayanai don tabbatar da hukunci ga wanda ya ci zarafi da zagi ga Manzon Allah:
i-Alkali Iyad ya fada cewa, “Ka sani Allah ya datar damu baki daya cewa: duk wanda ya zagi Annabi ko ya aibatashi ko ya danganta masa wata nakasa a kansa ko a nasabarsa ko a addininsa ko wani abu daga halayensa ko ya yi masa gagre ko ya sifatashi da wani abu ta hanyar zagi ko izgilanci ko kaskanta lamarinsa ko tawayar hakkinsa da aibatashi, to kurum mai zagin Annabi ne. hukuncinsa hukuncin mai zagin Annabi. Za a kasheshi kamar yadda zamu yi bayani. Ba wani bangare da cikin wadannan abubuwa da zamu togace akan wannan manufa ko a yi kokwanto akansa. Shin bayyanawa ya yi ko kuwa jirwaye-da-kamar wanka ya yi. Haka nan wanda ya la’anceshi ko ya yi addu’a mara kyau a kansa ko ya yi burin wata cutuwa ta sameshi ko ya danganta masa irin abin da bai dace da matsayinsa ba ta hanyar zargi ko wasa da matsayinsa ta amfani da maganganun yasassu da basu dace ba, ko ya ayyarashi da wani abu da ya gudana na bala’i da jarrabar Allah da ya yi masa, ko ya yi masa zumbe da wani abu daga cikin abubuwan da suke sun halatta gareshi ta hanyar ‘yan adamtaka, wadanda ya saba da su. Wadannan duka haduwar malamai (Ijma’i) da shuwagabannin masu bada fatawa tun daga lokacin Sahabbai har zuwa yau”-(Asshifa na Alkali Iyad).
قال الإمام القاضي عياض-رحمه الله-“اعلم وفقنا الله وإياك: أن جميع من سب النبي صلى الله عليه وسلم، أو عابه، أو ألحق به نقصا في نفسه أو نسبه أو دينه أو خصلة من خصاله، أو عرض به، أو شبهه بشئ على طريق السب له، أو الإزراء عليه، أو التصغير لشأنه، أو الغض منه والعيب له: فهو ساب له. والحكم فيه حكم الساب، يقتل، كما نُبيّنه. ولا نستثني فصلا من فصول هذا الباب على هذا المقصد، ولا يمترى فيه، تصريحا كان أو تلويحا. وكذلك من لعنه أو دعا عليه أو تمنى مضرة له أو نسب إليه ما لا يليق بمنصبه على طريق الذم أو عبث في جهته العزيزة بسخف من الكلام وهجر ومنكر من القول وزور أو عيره بشئ مما جرى من البلاء والمحنة عليه أو غمصه ببعض العوارض البشرية الجائزة والمعهودة لديه وهذا كله إجماع من العلماء وأئمة الفتوى من لدن الصحابة رضوان الله عليهم إلى هلم جرا”.
Hakika duk wanda ya saurari yadda Abduljabbar yake bayani ya san cewa yana budewa wadanda suke sauraransa dammar su rika yin irin wadannan munanan tunani ga Shugaban halitta!
ii-Imamu Ibnu Rushd (Kakan) ya ce, “Ibnu Wahab ya ruwaito daga Imamu Malik ya ce, ‘duk wanda ya ce kwajallen Annabi (S.A.W.) ya yi dauda yana nufin aibatashi da wannan, za a kasheshi. An kuma ruwayar daga Imamu Malik yan cewa dangane da wani mutum da ya ayyara wani da talauci. Sai wancan ya ce, kana ayyarani da talauci, to ai Annabi ma ya yi kiwon dabbobi! Sai Imamu Malik ya ce, wannan sai an ladabtar da shi saboda ya ambaci sunan Annabi a inda bai dace ba”-(6/396-399)
A duba wannan bayani na ilimi daga Imamu Malik da kyau. An fadi sunan Annabi a inda bai dace a fada ba. Ina ga wanda zai rika fadarsa amma yana cusa maganganu, wai yana karshe!! Bayan ba zai yiwa mahaifansa irin wannan kariyar hade da muyagun kalmomi ba!!
قال الإمام ابن رشد الجد-رحمه الله-:”وقد روى ابن وهب عن مالك أنه قال: من قال إن إزار النبي عليه السلام وسخ أراد به عيبه قتل ، وروى عنه فيمن عير رجلاً بالفقر فقال له: تعيرني بالفقر وقد رعى النبي عليه السلام الغنم إنه يؤدب لأنه عرض بذكر النبي عليه السلام في غير موضعه”.
8-Bayan an gama tumurmusa Abduljabbar da hujjojin Kur’ani da Sunna a fagen dagar titsiye, sai kuma ga shi ya fito yana bada hakuri har sau biyu. A na karshen ma yana cewa ya janye maganganunsa. Amma ashe tuban muzuru ya yi! Sai jijidakai na sabo ya debe shi ya koma yana wai kokarin bada amsa ga tambayoyin da aka yi masa, ya kasa bada amsarsu a gaban duniya. Abin da ya aikata a lokacin ya yi daidai da irin abin da Allah ya sifata wasu mutne da shi da cewa, “Tir da duk makaryaci mai sabo. Yana jin ayoyin Allah ana kaanta masa su, sai ya dage cikin girman kai kamar bai ji ayoyin ba, to ka yi masa bushara da da azaba mai radadi. Idan ya san wani abu na ayoyinmu sai ya rikesu abin izgilanci, to irin wadannan suna da azaba ta wulakanci”-(Al-Jasiya:7-9)
قال الله تعالى:”وَيْلٌ لِكُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٍ. يَسْمَعُ آيَاتِ اللَّهِ تُتْلَى عَلَيْهِ ثُمَّ يُصِرُّ مُسْتَكْبِرًا كَأَنْ لَمْ يَسْمَعْهَا فَبَشِّرْهُ بِعَذَابٍ أَلِيمٍ. وَإِذَا عَلِمَ مِنْ آيَاتِنَا شَيْئًا اتَّخَذَهَا هُزُوًا أُولَئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ مُهِينٌ”- (الجاثية:7-9)
Akwai bambanci tsakanin azaba mai radadi da azaba ta wulakanci. Mai radadi a ji mutum zai jita kamar irin yadda Abduljabbar ya ce a lokacin titsiye ya ji shi kamar a kurkuku! Amma azabar wulakanci kuwa ita ya fata gani da ya dawo bai yi cikakken tuba ba! Idan kuma bai tuba ba ragowar ayoyin yana can a Surayul Jasiya sai mutum ya karanta! Sai mu yi la’akari da wannan. Allah ya tsaremu.
9-A karshe, hakika ya tabbata cewa Abduljabbar ya munana ladabi ga Annabi. Ya kamata a san cewa akwai hakki kala uku dangane da Annabi; hakkin Allah, da hakkin shi kansa Annabi (S.A.W) da kuma hakkin daukacin Musulmi.
A cin zarafin manzonsa, an fadawa masoyinsa maganganu a fakece, abin da zai bayu zuwa suka ga Kur’ani da Sunnar Ma’aiki
Hakkin Musulmi kuma shi ne an fadawa Annabinsu wadanda suka fi so a kan komai magana ta cin zarafi, an yi masa da rashin ladabi.
Hakkin Annabi kuma an fadi maganganu cutarwa a gareshi, wadanda ba yadda za a yi a fadi irinsa a gabansa, sannan a yi da’awar kareshi ake yi. Alkali Iyad ya yi bayanin cewa mnana ladabi a magana da bayani yana daga cikin cutarwa ga Annabi”-(Asshifa na Alkal Iyad: 2/252)
قال الإمام القاضي عياض:”واذا أخذ في أبواب العصمة وتكلم على مجاري أعماله وأقواله صلى الله عليه وسلم تحرى احسن اللفظ وأدب العبارة ما أمكنه وأجانب بشيع ذلك وهجر من العبارة ما يقبح”.
Wannan cutarwa kuwa an yiwa Manzonmu ita. Don haka ba zamu yafe ba.
Muna jan hankali ba a cewa mutane su je su kaddamarwa da Abduljabbar hukunci ba. An dai fadi irin tanadin da Shari’ar Musulunci take da shi ga wadanda suka zagi Annabi (S.A.W). An tambayi Imamu Asbag cewa wani mutum ya ga wani zindiki kuma tabbatar da cewa zindikin ne! Ai ya yi kwance-kwance ya kasheshi! Sai Imamu Asbag ya ce, ‘Ya kyauta a tsakanisa da Allah! Sai dai shugaban zata yi masa hukuncin horo saboda gaggawa da ya yi kafin gwamnati ta gama tabbatar da abubuwa. Sai dai ya kyauta saboda yawancin shuwagabanni suna barin irin wannan ya wuce ba sa zartar da shi”-(Attaju Wal-Iklil na Al-Mawwak:5/323)
قال الإمام المواق:”وسئل أصبغ عن رجل أيقن برجل أنه زنديق، فاغتاله فقتله! فقال: هو محسن فيما بينه وبين الله، لكن يعزره السلطان للعجلة قبل أن يثبت ذلك للسلطان! ولكنه محسن، إذ لعل الولاة تضيع مثل هذا ولا تصححه”.
Tun da Musulunci ya shigo wannan kasa mai albarka ake karanta da karantar da wadannan littafai na hadisai. Abin da aka koyo daga cikinsu shi ne girmama Annabi da bashi matsayin da kore masa duk wata tawaya a hakkinsa. Haka nan ma sahabbansa; kowa ya tashi a kan girmamasu da darajantasu. Ba kuma nan Nigeri kadai ba, abin ya shafi duk duniyar Musulunci. Amma ba malamin da ya gano suna dauke da zagi da cin zarafi da sifata Annabi da wasu sifofi marasa kyau ba, sai da Abduljabbar ya zo. Shi ma bayan ya karanta littafan Shi’a da na ‘yan kala-kato sai ya shiga irin wadannan maganganu!
Kada dai a manta Allah Madaukaki ya ce, “Hakika wadanda suke cutar da Allah da Manzonsa, Allah ya la’ance su a duniya da Lahira. Ya kuma tanadar musu da azaba ta wulakaanci”-(Al-Ahzab57).
“ان الذين يؤذون الله ورسوله لعنهم الله في الدنيا والاخرة، واعد لهم عذابا مهينا”.
Allah ka tsare imaninmu da zuriyarmu baki daya, ka taimakemu wajen girmama Annabinka da Sahabbansa da duk wadanda suke kan tafarkinsu, ka yi maganin duk masu cin fuska da tawaye hakkin Annabinmu Muhammad-Tsira da Aminci su kara tabbata a gareshi da Alayensa da Sahabbansa baki daya.
Allah ya bamu sa’a da dacewa.
1-Na fito yawo gabagadi
ba bu mai iya jijjigani.
2-Sai ruwan hujja da aya
Ko hadisi mai bayani.
3-Nai yabo gun sahabatu
Ba bu mai iya karkatani.
4-Ba ni ko jin hasashe
ko bayanai masu zarni.
5-Jaberi babu nisa ka yi zari
Ka yi kushe gun bayani.
6-Ka yi kulli ka yi zobe
Ka yi dungu gun ma’auni.
7- Ka yi wasa ka muzurce
Ka mugusta gun Kurani.
8-Ka fito yawo gabagadi
Na ga ka tumfe da rauni.
9-Ka yi kuri can a daki
ka yi rugin ba bu hauni.
10-Ka yi langwan zo da hujja
Ga shi yau kun tsoratani.
11-Na ci tauri can a Mushe
Kun yi burgin lankwasani.
12-Na ji zafi can a zuci
Wai gumi ya lullubeni.
13-An matsa wai sai na amsa
Yau fa zauren ba sukuni.
14- Ni fa na gano garinana
So fa ake a haukatani.
Fatfesa Ahmad Murtala shi ne shugaban sashen Nazarin addinin Musulunci da Shari’ah na Jami’ar Bayero
Hausa
Kwankwaso Congratulates Gov. Yusuf on NUT Award for Education Reforms
Former Kano State Governor and National Leader of the New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabiu Musa Kwankwaso, has congratulated the current governor, Abba Kabir Yusuf, on receiving the prestigious NUT Golden Award from the Nigeria Union of Teachers (NUT) in recognition of his significant contributions to the education sector.
In a message posted on his verified X (formerly Twitter) handle, Kwankwaso commended Governor Yusuf for his unwavering dedication to revitalizing Kano’s education system.
He described the governor as a “game changer” in the sector and encouraged him to remain steadfast in pursuing his educational reforms.
“Congratulations to His Excellency Abba Kabir Yusuf on the NUT Golden Award for his achievements in the education sector,” Kwankwaso wrote.
He further urged Governor Yusuf to strengthen his commitment toward achieving his broader goals in education reform.
The award was presented during the 2024 World Teachers’ Day celebration, which took place at Eagle Square, Abuja.
Organized by the NUT in collaboration with the Federal Ministry of Education, the event brought together teachers and educational leaders from across Nigeria to recognize and celebrate significant achievements in education reform.
Governor Yusuf was honored with the NUT Golden Award for his transformative efforts in rescuing Kano’s education system, which had suffered from years of neglect.
His administration has been lauded for implementing policies aimed at improving school infrastructure, increasing access to quality education, and ensuring the professional development of teachers in Kano.
This recognition comes as part of a broader acknowledgment of his leadership and commitment to enhancing educational opportunities for all in the state.
The event, which marked the 2024 edition of World Teachers’ Day, highlighted the importance of teachers and their role in national development, with the NUT acknowledging the critical support of political leaders like Governor Yusuf, who are spearheading reform efforts.
The governor’s administration has undertaken various initiatives to address the challenges in Kano’s education system, including rebuilding dilapidated schools, recruiting more teachers, and prioritizing student enrollment, especially for girls.
Governor Yusuf’s receipt of the NUT Golden Award serves as a milestone in his administration’s ongoing efforts to reposition Kano as a leading state in education, setting an example for others across the country. His reforms have drawn praise.
Hausa
The Chronicles of Kano #03 – Sarki Rumfa da kuma Taj–Al-Din Fi Ma Yajib Ala Al Muluk
Farfesa Abdalla Uba Adamu
A duk cikin Sarakunan da suka mulki Kano, guda uku sun yi fice fiye da sauran. Na farko shi ne Sarki Tsamiya (1307-1343) wanda shi ne na tara a jerin sarakunan. Ko da ya hau mulki ya tarar da bautar gargajiya a gari. Ya tara masu bautar ya yi musu bushara kamar haka: “Soyayya ana gadanta, ƙiyayya ma ana gadanta, babu wani abu tsakanina da ku sai baka da mashi da takobi, da garkuwa, ba yaudara, domin babu mayaudari sai matsoraci.”
Sarki na biyu shi ne Ali Yaji Ɗan Tsamiya (1349-1385). Shi ne wanda ya ci gaba da jihadin ba mahaifin sa ya fara. A lokacin sa Musulunci ya kafu a Kano, har manazarta suka laƙabawa Kano da darajar Sultanate. Wannan kuwa sakamakon umarnin da Sarki Ali ya bayar na cewa Kano ta zama ƙasar Musulumi daga 1349 bayan zuwan Malaman Wangarawa a ƙarƙashin Abdulrahman Zaite. na Farko, da suka kawo Musulunci su ka jaddada masa nasa Musuluncin (domin a kwai hasashen Musulumi ne shi).
Sarki na uku shi ne Muhammadu Rumfa Ɗan Yakubu (1463 -1499). A zamanin sa a ka samu bunkasar Musulunci da kuma ilimi. A wannan lokacin aka samu ingizowar Malaman Larabawa, Fulani, Kanuri, Buzaye suka yi wa Kano dirar mikiya domin neman ilimi.
A wannan lokacin ya yi abubuwa guda goma sha biyu na a-zo-a-gani, ciki har da kafa tushen reshen Jami’ar Sankore a Masallacin Madabo, wacce ta zama Jami’ar Madabo. A zamanin sa rukunin Wangarawa na biyu (in an tuna, rukunin farko sun iso Kano shekaru 114 da suka shuɗe a 1349), su ma a ƙarƙasahin Shugaba mai suna Abdulrahman Zaghaiti (na farkon sunan sa Zaiti, don kar ka ɓata!) suka zo Kano.
A zamanin wannan Sarki Malaman fada suka fito da Ajami a matsayin matakin farko na karatun yara a Tsangayu da makarantun Allo. Lokacin ne ma aka fito da ‘kuɗin laraba’ a matsayin kuɗin makaranta wanda za a bawa Alaramma domin yin cefanen ciyar da makaranta washe gari, watau ranar Alhamis.
Amma babban abin janyo hankali a zamanin Sarki Rumfa shi ne fitar da tsarin mulki a Kano – na farko a rubuce a kowacce daula a ƙasar Hausa. Wannan kuwa ya faru ne ƙarƙashin jagorancin mashahurin Malami Muhammad ibn Abd al-Karim al-Maghili, wanda ya zo tun daga ƙasar Algeria domin bayar da tasa gudunmowar wajen ciyar da ilimi gaba a Kano saboda shaharar da ta yi wajen kasuwanci da ilimin addinin Musulunci.
Da ya zo, Sarki Rumfa ya roƙe shi da ya ba shi shawara a kan tsarin mulki a Musulunci saboda inganta nasa mulkin da adalci. Al-Maghili nan take ya yarda ya rubuta masa littafi, Tāj al-Dīn fī Mā Yajib ʿalā al-Mulūk wa al-Salāṭīn. Wannan ya zamar masa jagora wurin tafiyar da al’amurran siyasa da mulkin ƙasar Kano.
A kwai kundaye digiri na uku aƙalla guda biyu waɗanda suka nuna sakamakon bincike mai zurfi a kan Al-Maghili and mulkin Sarki Rumfa. Ga jerin guda biyu sa suka fi shahara. Ba duk a ke samu a Acibilistan ba, amma in a ka ƙura ido, wataƙila a yi sa’a.
Gwarzo, Hassan. The Life and Teachings of al-Maghili with Particular Reference to the Saharan Jewish Community. Ph.D. Thesis. Univ. of London, 1972.
Starratt, Priscilla Ellen, Oral history in Muslim Africa: Al-Maghili legends in Kano. PhD thesis, University of Michigan, 1993.
A yau dai ga fassarar Tāj al-Dīn da Hausa, kuma an sarrafa ta a Ajamance. Bi rariyar liƙau ɗin da ke ƙasa ka tsinko shi.
https://bit.ly/3ZBDrHl.
Farfesa Abdalla Uba Adamu
Hausa
Shekara 60 na Hausawa a Doron Ƙasa (4) – Farfesa Malumfashi
Wannan wani raddi ne da Farfesa Ibrahim Malumfashi ya yi wa Abduljalil Ismail Ajis
Bayan dukkan wannan balaguro tare da sauran al’ummar duniya wannan ya haifar da damar da aka samu Hausawan wajen ƙasar Hausa suka sake haɗuwa da sauran ‘yan uwansu, musamman na ɓangaren jinin Uwa da ba su yi balaguro zuwa ko’ina ba a sassan duniya, waɗanda suke zaune a nahiyar Afirka a tsawon shekaru. Wannan haɗakar barbarar ‘yan’yawa ita ta samar da kai da ni da duk wani Badauri ko Bagobiri ko Bakatsine ko Bazamfare ko Bakabe ko Bazazzage ko Basantolo ko Bakano ko Bagunge ko Bahaɗeje ko Barane da wasu ƙasashe da al’ummun Hausawa da dama da suka yi rayuwa, suka ɓace a tsawon tarihi.
Wannan ba komi yake nuna mana ba sai al’ummar Hausawa ba na yanzu ba ne, shi harshen Hausa ne na yanzu, shi ma ba yanzun-yanzu, irin na yau ba ne, shekara dubbai ne ake magana. Ƙila tambayar da wasu kan iya yi zuwa yanzu ita ce yaya aka yi aka san waɗannan batutuwa da yawanci ba su a rubuce ko ba a ci karo da su ba a rubucen ko kuma me ya sa ba a zubo hujjoji da za a iya gani ƙwaro-ƙwaro domin tabbatar da batun ko akasin haka ba? Ta yaya yawancin irin waɗannan bayanai ba su bayyana ba ko da kuwa daga kunnuwa da suka girmi kakanni, ta ina aka samar da tunanin?
Ire-iren waɗannan tambayoyi an sha yin su game da wannan bincike, abin da zan iya cewa shi ne, yawancin bayanai ba su ɓullo daga tarihin da muka saba karantawa ba ne, sannan yawancin bayanan da yake sun tusgo ne daga rayuwar lokacin da ba tarihi a rubuce ko ajiye suna da wahalar karɓuwa nan da nan, haka kuma fagen nazarin tarihi da tarihihi da muka gwanance a ka, ba su iya fasalta su da kyau ba, amma wasu daga cikin bayanan na nan kimshe cikin adabinmu na gargajiya da waƙoƙi da kalamominmu na yau da kullum, ba mu dai kula ko nazarce su da kyau ba ne. Wannan giɓi shi ya sa aka koma cikin gonar nazarin ilmin ƙwayar halitta da ke tattare da jinin al’ummar duniya, ciki ko har da Hausawa domin samun mafita.
Shi wannan fage na nazarin ilimin ƙwayar halitta ya zama kandami ne na fahimtar rayuwa ta tsawon tarihi ko da kuwa ba a rubuta ko ajiye shi ba. Saboda binciken masana kimiyya ya gano cewa a cikin gudan jini ko ƙwayar halitta akwai tarihin al’umma da ke jibge, sai an buɗa shi za a kwashi ilimin da ke ɓoye. Domin kowane kalami ko waƙa ko zancen azanci ko gudanuwar addini ko kuma bazuwar al’adu na haihuwa ko aure ko soyayya ko mutuwa suna damfare a cikin jinin al’umma, ba su ɓacewa baki ɗaya, ke nan daga lokaci zuwa lokaci ana iya ƙwaƙulo su domin nazarin rayuwar yau.
Saboda haka yawancin bayanan da muka zubo a nan, sun samo asali ne daga bincike da nazari da aka samu yi daga ɗibar miyan bakina da jini, a matsayin Bahaushe aka ƙwanƙwance tarihin da ke ƙunshe a ciki a shekarar 2017, a can Amurka, a ɗakin bincike na (Genographic project), a lokacin kuma akwai tarin bayanai kan Hausawa da ‘yan uwansu da suka rigayi nawa, daga wannan banki ne aka samar da bayanai da suka nuna yadda rayuwar ‘Hausawa’ ta kasance a tsawon tarihi.
Daga sakamakon wannan bincike ne aka fitar da bayanan da ke haskaka mana yadda Hausawan wannan zamani suka wanzu, mai nuna daga ina Hausawa suka tuzgo, su wane ne ‘yan uwansu na kusa da na nesa. Abin da kuma ya fito fili ya haɗa da:
•Akwai jinin al’ummar yankin sassan ƙasashen Maleshiya zuwa Indonesiya da Filifins a cikin Hausawa wannan zamani, (miya ta kuka ko taushe da muke da su yanzu, akwai su a harshen Malay da makusanta).
• Akwai jinin Barbar na yankin Siwa a Arewacin ƙasar Masar har kashi 20 cikin 100 a cikin jinin Hausawan wannan zamani. A wannan yanki ne Hausawa suka yi bautar rana da muke bayyanawa ta waƙoƙin gargajiya da suka nashe a ƙasar Hausa tun da daɗewa. Wasun mu ba su manta irin wannan waƙa ba; ‘rana, rana buɗe, buɗe in yanka miki rago ki sha jini, shar, shar’. Ba aron wannan waƙa aka yi ba, jini da gado ne daga al’ummar Hausawa da suka rayu a Masar ta dauri. Nan kuma aka samo kalmomi irin na auratayya da soyayya da ke jibge a tunanin Hausawan yau, misali ‘so’ da ‘soyayya’ da ‘aure’ da ‘mata’ da ‘miji’ da wasu irin su da dama!
• Haka kuma Hausawa yau suna ɗauke da jinin mazajen da ke zaune a kudancin ƙasar Masar na kimanin kashi 6 cikin ɗari, shi ya sa ake cewa Hausawan yau tsittsigensu na Yahudawa da Kibɗawa ne, wato ‘yan uwa ne ga al’ummar Annabi Musa da ta Fir’auna.
Farfesa Ibrahim Malumfashi malami ne a Jami’ar jihar Kaduna ya wallafa wannan rubutun ne a shafinsa na Facebook.