Connect with us

Hausa

Hisba za ta tilastawa ma’aurata shiga makarantar nazarin zamantakewar aure a Kano

Published

on

Hukumar Hisbah ta ce za ta bude makarantar koyon zamantakewar aure a Jihar Kano cikin , a watan Nuwambar wannan shekara.

KANO FOCUS ta ruwaito babban kwamandan hukumar, Muhammad Haruna Sani Ibn Sina ne ya bayyana hakan a zantawarsa da gidan rediyon Freedom.

Ibn Sina ya ce, a matakin farko zabi ne ga wanda ke da sha’awar shiga, amma a nan gaba za su yi kokarin ganin an mayar da shi doka ga duk mai son yin aure a Kano.

“Kaso 75 daga cikin korafin da mu ke karba kan matsalolin aure ne, wannan ne ya sanya muka samar da makarantar don ba da horo.

“Matsalar yawaitar mutuwar aure a kullum karuwa take musamman a Kano, don haka makarantar za ta samar da hanyoyin dabarun koyar da ilimin zamantakewar aure,” cewar Ibn Sina.

Kazalika, kwamandan ya kara da cewa za su shigar da kudiri gaban majalisar dokokin Jihar don tilasta wa ma’aurata shiga makarantar.

Ibn Sina, ya kuma kara da cewa horaswar ba iya mata za ta tsaya ba, har da maza za a basu damar shiga don samun daidaito da raguwar matsalolin.

Matsalar aure a Jihar Kano na ci gaba da zama babbar kalubale musamman kan yadda Hisbah ke fama wajen warware su.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Hausa

Ta hanyar gyaran kundin mulki ne za a gyara kasar nan-Kawu Sumaila

Published

on

Tsohon Mataimakin Shugaban marasa rinjaye na Majalisar wakilai, Abdulrahaman Kawu Sumaila ya ce ta gyaran kundin tsarin mulkim kasa ne kawai zai ceto kasar nan daga halin da ta ke ciki

Ya ce  akwai bukatar a sake duba kundin tsarin mulkin kasar nan cikin gaggawa da kuma bada dama ga jihohi da kananan hukumomi wanda hakan zai magance yawancin kalubalen da kasar nan ke fuskanta.

KANO FOCUS taruwaito Kawu Sumaila ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

Ya ce shekaru goma 12 da ya yi a Majalisar karkashin shugabannin Kasa  3, ya sa ya fahimci Najeriya na bukatar tsarin da zai taba rayuwar al’umma tun daga tushe.

Ya kara da cewa baiwa kananan hukumomi damar cin gashin kansu ita ce mafuta.

Kawu wanda ya kuma yi aiki a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan majalisar wakilai ta kasar, ya ce, a fahimtarsa akwai matsaloli da yawa da kundin tsarin mulkin kasar nan ya haifar kamar rashin tsaro, tabarbarewar tattalin arziki da sauransu.

Kawu Sumaila Wanda jigo ne a Siyasar Kano kuma yake neman kujerar Sanatan Kano ta Kudu a karkashin jam’iyyar NNPP , ya ce idan ya lashe zaben zai mayar da hankali wajen gyaran kundin tsarin mulki da kuma yi masa kwaskwarima.

“Idan na zama dan majalisar dattawan Najeriya, zan dage wajen ganin an yiwa kundin tsarin mulkin kasar cikakken nazari da kuma gyara.” Kawu Sumaila

“Kasa mai yawan al’umma kamar Najeriya mai dauke da mutane sama da miliyan 200 ace tana da Babban sufeton ‘yan sanda guda daya ko shakka babu dole za’a fuskanci kalubalen tsaro”. Inji Kawu

“Ina goyon bayan samar da ‘yan sandan Jihohi domin sojoji su fuskanci nauyin da tsarin mulki ya dora musu na kare yankinmu, amma hakan na iya faruwa ne kawai idan muka samu ‘yan sandan jahohi ”.

Mu dauki misali jihar Kano, mu kusan miliyan 20 ne, kuma adadin ‘yan sanda a kano bai wuce dubu 8,000 ba, kuma a karamar hukumata ta Sumaila muna da chaji ofis din yan sanda guda biyu, ‘yan sandansu gaba daya ba su wuce 80 ba, a Karamar Hukumar da ta ke da mutane kusan 500,000”. a cewarsa.

Ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya ta dorawa kanta nauye-nauye Masu yawa, har ma aikin da ya kamata ace kananan Hukumomi ta yi Amma sai ka ga Gwamnatin Tarayyar tana inda ya ce gina cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da Gwamnatin Tarayya tana kamar Gina Asibitocin kula da lafiya a matakin farko Wannan bai dace ba.

Kawu Sumaila ya kuma yi tsokaci kan harkokin ilimi inda ya ce ilimin Jami’a na da matukar muhimmanci kuma dole ne a karfafawa matasa gwiwa su yi shi, ba Wai Kawai su Sami shaidar kammala digiriba, a’a su Sami ingantaccen Ilimi da zasu iya alfahari da shi ko’ina a duniya.

Sai dai yace duk wadannan da ma wasu zasu Samu ne kawai Idan “Muna da kundin tsarin mulki wanda zai sa a sami shugabanci nagari, da rikon amana, yin komai a bide, daina nuna wariya gaskiya, inganci, bin doka da oda da kuma kundin tsarin mulki wanda zai samar da sahihin zabe mai inganci

Continue Reading

Hausa

ADP: Zan kawo karshen matsalolin al’ummar Jigawa-Ibrahim Sabo

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Jam’iyyarADP mai alamar littafi ta tsayar da Alhaji Ibrahim Sulaiman Sabo, a matsayin ɗan takarar gwamna a jihar Jigawa.

Wannan na zuwa ne biyo bayan taron ƙaddamar da takarar tasa, wanda aka gudanar a Alhamis ɗinnan, a helkwatar jam’iyyar dake Dutse babban birnin jihar Jigawa.

Jam’iyyar ta zabi Sabo ne ta hanyar masalaha, inda delegate 16 suka amince da zabin.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan ayyana takarar tasa, Alhaji Sabo, wanda haifaffen ƙaramar hukumar Taura ne, yace ya shirya tsaf domin ceto al’ummar Jigawa daga ƙangin da manyan jam’iyyun kasarnan na APC da PDP suka jefasu.

Yace sabuwar dokar zabe da gwamnatin APC ta kawo, ta basu cikkaken gwarin gwiwar samun nasara.

“Lokacin PDP, Jonathan ne ke kan mulki, da Allah ya ƙaddara zuwan ƙarshensa, sai ya kawo Card Reader, wanda shine yayi silar faduwarsa. To itama gwamnatin APC da ta kawo dokar zabe, matukar za’abi ƙa’ida, to ta kada kanta.”

Alhaji Sabo ya ƙara da cewa idan suka kafa gwamnati, zasu baiwa bangaren noma fifiko, zuwa fannin lafiya da ilimi da kuma tattalin arziki.

“Bangaren noma, ina tabbatar maka cewa mudai nan a Arewa, mun rike noma, kuma rabon taki da ake, nima manomi ne amma ban taba samu ba, wannan ba ƙa’ida bace. Kamata yayi a tura wakilai ko ina, a gano gonarka hekta nawa ce, kuma buhu nawa ne zai isheka.”

“Na biyu bangaren lafiya, zan tabbatar cewa in Allah ya yarda, mutum yayi haɗari ya karye ko wani abu ya faru, ba zamu bari ya zauna babu kulawar lafiya ba, har yazo ya mutu.” Inji Alhaji Sabo.

Ya kara da cewa “idan kaba mutum wadataccen abinci da lafiya da ilimi ka gama masa komai.”

Tun daga 6 ga watan Yunin da muke ciki ne jam’iyyar ta ADP ta fitar da yan takarar majalisar jiha 30 ta hanyar masalaha, sannan a 7 ga wata, ta zabi yan takarar majalisar wakilai ta tarayya 11, har ila yau ta kaddamar da masu takarar Sanata gida 3, dukkaninsu ta hanyar masalaha.

Shugaban jam’iyyar na jihar Jigawa, Comrade Bua Abdul Azeez, yace sun zabi fitar da yan takarar ta hanyar masalaha ce bisa amincewar yayan jam’iyyar.

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa duk da jam’iyyar tasu ƙarama ce, zatayi nasara, kasancewar dukkanin manyan jam’iyyun sun gaza.

An gudanar da taron ƙaddamar da takarar ce gaban idanun wakilan hukumar zabe INEC, da jami’an yan sanda.

Continue Reading

Hausa

Kano Pillars ta doke Katsina United 1-0

Published

on

Kano Pillars FC

Jamilu Uba Adamu

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta samu nasarar doke Katsina United daci daya da nema (1-0 ) a fafatawar da suka yi yau Alhamis a filin wasa na Moshood Kashamu Abiola dake Babban birnin tarayya Abuja.

KANO FOCUS ta ruwaito cewa dan wasan Kano Pillars Auwalu Ali Mallam ne ya zura Kwallon a ragar Katsina United a ragowar mintunan da aka ware don karasa wasan.

Auwalu Ali Mallam

Idan za a iya tunatawa an daga wasan ne bayan da hatsaniya da ta barke ana tsakiyar wasa tsakanin kungiyoyin biyu a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata a kwanakin baya.

Sai dai, a yau aka kammala wasan a filin wasa na Moshood Kashamu Abiola dake Babban birnin tarayya Abuja.

Hakan ya ba wa Kungiyar Kano Pillars damar darewa matsayi na goma sha shida acikin jerin kungiyoyi ashirin dake fafatawa a gasar ajin Kwarraru na Kasa.

Continue Reading

Trending