Hausa
Tarihin rigingimu tsakanin magoya bayan kungiyoyin Kwallon kafa a Kano

JamIlu Uba Adamu
Hamayya da adawa tsakanin magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa ba sabon abu bane, musamman ga ma su bibiyar al’amuran wasanni. Tsohon abune wanda ya dade yana faruwa tun kirkirar wasan kwallon kafa.
Kwallon kafa ya kasance wasan da ya fi kowanne daukaka tare da samun magoya baya da yawa. Wasan ya samo asali ne a kasar Birtaniya, Kuma ya watsu zuwa ko Ina a fadin duniya.
Kamar yadda manazarta Suka fada, irin wannan rigingimun sun dade suna faruwa tun zamanin Sarki Edward II (na biyu ) na kasar Biritaniya, a cikin karni na goma sha uku.
A shekarun baya, a nan Jihar Kano rigingimu tsakanin magoya bayan kungiyoyi daban-daban, shi ne matsalar da ta addabi wasan kwallon kafa.

Kamar yadda, tarihi ya nuna, mafi yawancin wadannan rigingimun suna faruwa ne a tsakanin kungiyoyin dake buga gasar cin kofin kwallon kafa na ‘Tofa’ a wancan zamanin. (Amma wasu hammayar ana yin su tun kafin a maida sunan gasar ta zama Tofa)
Mafi yawancin kungiyoyin kwallon kafar wancan zamanin sunan unguwannin da suka fito suke amsa wa. Don haka mafiya yawan magoyan bayansu daga wadannan unguwannin nasu su ke.
Saboda haka, a wancan zamanin Idan dan kwallo ya na wata kungiyar kwallon kafa, wacce ke wakiltar wata unguwa ya sauya sheka ya koma wata, ba karamar rigima ba ce da hatsaniya a tsakanin magoya bayan kungiyoyin da hakan ta faru.
Misalan irin wannan rigingimu a tsakanin kungiyoyin Kwallon Kafa da magoya bayan su a wancan shekarun da suka gabata, na faruwa a tsakanin Golden Stars da Raccah Rovers (Amma su yawancin adawa ce ta fatar baki ba ta makami ba) kamar yadda na samu bayani.
Akwai adawa mai tsanani a tsakanin Kungiyar Cosmos ta Birged ko Kano United (Berger) dake cikin birni.
Hakazalika, Kungiyar Kwallon Kafa ta White Elephant dake Zage da ta Wambai United dake Kofar Wambai. (Ance Idan sukai wasa a stadium, ranar kowa dake unguwannin biyu tun yamma yake rufe gidan sa , saboda tashin hankalin da zai biyo baya).
Fagge Pele da Wambai United a wancan zamanin adawa ce mai tsanani a tsakanin su.
Haka Kuma da akwai Hammaya mai yawa a tsakanin Rimi market da Red Lion.
Ba a yin ga maciji tsakanin Soccer Strikers da Good Hope ko Tahir Babies dukkaninsu dake unguwannin cikin Gari.
A Irin wannan kazamar adawar da hammayar ne har ta kai ga tsohon dan wasan Kano Pillars ( Mai tsaron raga ) Jamilu Goalkeeper ya rasa kaninsa ( Allah ya kai rahama a gare shi, Ameen ).
Wannan rigingimun na kwallon kafa a kan fade su har a kafafen yada labarai kamar yadda bincike na ya nuna.
Misali, jaridar Weekly Trust shafin wasanni, 12-Nuwanba- 2000 ta rawaito cewar ” Fada mai tsanani ya barke a tsakanin magoya bayan Kungiyar Kwallon Kafa ta Cosmos da Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano United, inda magoya bayan sukai amfani da makamai, sanduna, da adduna, bayan dawowa daga hutun Rabin lokaci, inda kungiyoyin suke 0-0 “
Alhaji Tukur Babangida ( Tsohon Shugaba ne a hukumar wasanni ta Jihar Kano ) yace; ya sha ganin irin wannan tarzoma. Amma wacce ba zai manta da ita ba, itace wacce ta faru a wasan karshe tsakanin Raccah Rovers da Golden Stars a filin wasanni na Sabon Gari. Anyi barna mai yawa bayan an tashi daga wasan. An farfasa duk naurorin bada hannun dake kan titin filin wasannin, an yi wa masu shaguna barna,” a cewar sa.
Irin wadannan fadace-fadace a filayen wasannin kwallon kafa su suka sa a wancan zamanin, masu Sha’awar zuwa Kallon kwallon kafa ba sa zuwa filayen wasanni.
Jihar Kano, Allah ya albarkace mu da samun ma su jagorantar harkokin wasanni, ma su basira, hangen nesa da sanin makamar aiki.
Allah a cikin ikon sa, ya ba su damar dakile wannan musiba ta fadace-fadace da hammaya a tsakanin ‘yan uwa magoya bayan kwallon kafa.
A yanzu wannan musiba ta zama tarihi. Saboda jajircewar da masu ruwa da tsaki suka yi wajen ganin sun kawo karshen wannan matsala.
Bisa hakan ne, mutane dabam-dabam suka bayyana ra’ayoyin su akan wannan batu.
Alhaji Salisu Yaro ( Mai Kula da Harkar wal-wala ne, a kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pllars ) a tattaunawar da na yi da shi akan dalilan da suka saka aka daina irin wannan rigingimu yanzu, ya ce “tunda kulabluka suka daina saka sunan unguwa a sunayen su, aka samu saukin wanann fadace-fadace tsakanin magoya baya.”
Ahmed Garba Yaro-Yaro ( Mataimakin mai horarwa ne a kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ) ya ce “Kafa kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ya taimaka wajen dakile wannan fadace-fadace da hamayya tsakanin magoya bayan kulabluka kasancewar Pillars na daukar yan wasa daga kowane unguwa a fadin jihar Kano, wanda hakan yasa an zama tsintsiya madaurin ki daya, ba bare, an zama daya “
Wani Magoyin bayan Kano Pillars Hamza Haro Fagge ya ce “yanzu Kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars ce babbar kungiya a Kano, bata da Kishiya balle ayi adawa da ita.”
Shi ma Auwalu Ahmad Dan Bachirawa da ya dade yana marawa Kungiyar Kano Pillars baya ya danganta hakan da hadin kai da aka samu da wayewa ga masoyan kwallon kafa a jihar Kano.
Ya kara da cewar, magoya baya daga kowanne sashe a jihar Kano na kaunar Kano Pillars. Don haka ba rigima a tsakanin kananan kulabluka, saboda sabgar goyan bayan Kano Pillars ta hada tafiyar tare.”
Yanzu dai zamani ya canja, an samu yawaitar Ilimi, musamman na addinin musulunci da na zamani wanda ya shiga lunguna da sakuna na unguwannin Jihar Kano.
Hakazalika yawaitar sana’o’i da dogaro da kai ga matasa, wanda dama su ne mafi yawancin magoya bayan wannan kulublukan, ya yi tasiri kwarai wajen raguwar wannan tarzoma.
Jamilu Uba Adamu, mai nazari da sharhi ne akan al’amuran tarihin wasan kwallon kaf’a.
za a iya samun tuntubarsa a jameelubaadamu@yahoo.com

Hausa
FG kickstarts construction of Emerging Technologies Institute in Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
As part of significant milestone in the Federal Government of Nigeria’s efforts to secure the socio-economic wellbeing of the future generation, as the ground was opened for commencement of construction of the Sustainable & Emerging Technologies Institute (SETI) under the aegis of the National Agency for Science and Engineering Infrastructure (NASENI), The Presidency.
KKANO FOCUS reports that the Executive Vice Chaiman/Chief Executive Officer (EVC/CEO) of NASENI, Mr. Khalil Suleiman Halilu during the Ground-breaking ceremony held at the Bayero University Kano (BUK) New Campus said the new institute sits on 30 hectares of the BUK land to be built, featuring state-of-the-art facilities, including innovation hubs devoted to Artificial Intelligence and other cutting-edge technologies, complemented by reliable power supply. “NASENI will fully build and equip and support the new Institute” said the EVC/CEO.

The future of socio-economic development for nations rests on human creativity, innovation and cooperation, Artificial intelligence, robotics amongst others.
Halilu said that the establishment of SETI in Nigeria is to rapidly respond to the waves of young people globally revolutionizing world economies with unprecedented emergence of socio-economic frontiers as by-products of innovations and ingenuities of these young minds.
“We in NASENI are firm believers in the potential of young Nigerians to be the prime catalysts of the type of transformation that Nigeria requires. And we will do everything within our powers to support them to fulfil this important responsibility”
“We are gathered here today to kickstart a project that will transform the lives and careers of future generations of young Nigerians. The Sustainable & Emerging Technologies Institute (SETI), located at the Bayero University Kano (BUK) by NASENI. This is very much in line with our operating principles; what we call our 3Cs: Collaboration, Creation, and Commercialization. These 3Cs are the principles that passionately drive us and guide the work that we do to ensure the industrialization of Nigeria in line with the Renewed Hope agenda of President Bola Ahmed Tinubu.”
SETI will produce innovators, technologists, entrepreneurs who will make their mark not just in Nigeria but around the world. “I’m eagerly looking forward to the day, not too long from now, when the Institute’s first set of beneficiaries will astonish the world with what they’re capable of accomplishing. These stories will put not just BUK on the global innovation map, but also Kano State and the entire Nigeria” said Halilu.
While carrying out the symbolic foundation laying ceremony of the institute as Special Guest of Honour, the Minister of Innovation, Science and Technology, Chief Uche Geoffrey Nnaji, described the project as not only laudable but NASENI’s another way of fast-tracking the placing of Nigeria on the global map of innovation and industrialization. The minister called the project an “ace project” and a pointer to secure a veritable socio-economic development for the nation.
In his goodwill message, the Vice Chancellor of BUK, Professor Sagir Adamu Abbas described the new institute as a vehicle for bringing together the three critical tripods for economic and sustainable development for nations, that is, the government, academia and industry. He described the ground-breaking event as the beginning of Nigeria’s journey in pursuit of sustainable development, massive job creation opportunities for the youths, and that the BUK was delighted to be host to such laudable initiative and momentum.
There is also, in addition to SETI, a second NASENI project for BUK is an Agri-preneurship Training Hub, that will be equipped with modern greenhouses, and facilities for Soil-less Farming, and Tissue Culture; occupying 10 hectares of land at the Old Campus. These projects collectively represent what NASENI stands for, that is, building capacity, advancing industrialization, supporting economic growth and prosperity.
NASENI appreciates the Government and people of Kano State, and the Vice Chancellor, management and students of Bayero University Kano (BUK), for all the support. Special gratitude goes to the Honourable Minister of Innovation, Science and Technology, Chief Uche Geoffrey Nnaji, the Special Guest of Honour.
NASENI thanked members of the National Assembly for their support, especially the NASENI oversight Committees in both chambers. And of course, President Bola Ahmed Tinubu, who has given NASENI the opportunity to serve Nigeria through his unwavering demonstration of commitment to the success of the Agency.

Hausa
Illar siyasantar da harkar tsaro da zaman lafiya a jihar Kano

Jaafar Jaafar
Na jima ban ga tsantsar rashin kishi da cin amanar aiki da ya wuce ƙaryar da hukumar yansandan jihar Kano ta gilla ba saboda tsananin siyasantar da harkar tsaro da zaman lafiya da cigaban al’umma.
Babu wani rahoto na sirri kan wani mugun abu da ke faruwa a birni ko ƙauye wanda gwamna bai san shi ba. A wasu lokutan ma gwamnan ya kan riga jami’an tsaro samun wani rahoton sirrin. Duk wanda ya san yadda “special service directorate” (wadda ke karkashin ofishin gwamna) ke gudanar aiki, zai fahimci inda na dosa.

Kasashen da su ka ci gaba, ba sa wasa da duk bayanin da hukumar yansanda ta fitar. Domin su a kasashen su dansanda shi ya fi kowa adalci, shi ya sa zai wahala yansanda su tuhume ka da laifi ka ga alkali bai ɗaure ka ba.
Kafin harin Boko Haram na farko a Kano a ranar 20 ga Janairu 2012, akwai wani babban jami’in gwamnati da ya faɗa min cewa ƙasar Amurka na duba yiwuwar buɗe ƙaramin ofishin jakadanci (consulate) a Kano wanda zai riƙa ba da visa da gudanar da wasu shirye-shirye a jihar Kano. Kwatsam sai a ka kawo harin bam. Daga nan maganar ta mutu murus. A tunaninka in da a ce Amurka za ta sake duba yiwuwar bude consulate a Kano, sai ta ji sanarwar hukumar yansanda ta fitar, me ka ke tunanin za ta yi? Za ta fasa ne!
Haka fa muna ji muna gani British Council ta rufe cibiyarta da ke Kano. Wannan cibiya ta taimaka gaya wajen sa wa matasa sha’awar karatu, kuma ta samar da damarmaki na karatu da tafiye-tafiyen nazari kasashe ga mutane da dama. Ita ma wannan cibiya a dalilin rashin tsaro yanzu ta tattara inata-inata ta tafi.
Ta fuskar kasuwanci, watakil wannan sanarwar karyar da hukumar yansanda ta fitar ta sa masu son zuba jari daga wasu wurare (foreign investors) su fasa. Haka zalika, watakil wannan asarar ta sa masu zuwa fatauci kasuwannin Kano su ja jiki. Ka ga sun jawo wa yan kasuwa da jihar asara.
Tarihi ya nuna tun kafin Kano ta yi shuhura a harkar kasuwanci, Katsina ita ce cibiyar kasuwanci a kasar Hausa. Babban abin da ya sa Katsina ta koma baya shi ne yaƙe-yaƙe da ta sha fama da shi, musanman a ƙarni na 18.
Kira na ga gwamnatin jihar Kano shi ne kada ta bar wannan cin amana ya wuce ba ta yi wa tufkar hanci ba. Kamata ya yi gwamna da kan shi ya kira gagarumin taron zantawa da yanjarida wanda ya ƙunshi manyan gidajen jaridu na ƙasa da waje domin fayyace wa duniya zancen. Idan ma da yiwuwar kai yandansan kotu, to yakamata gwamnati kada ta yi ƙasa a gwiwa.
Allah Ya zaunar da mu lafiya.
Jaafar Jaafar, shi ne mawallafim jaridar Daily Nigerian, ya kuma wallafa wannan rubutun ne a shafinsa na Facebook.

Hausa
EFCC arraigns one for N108 million fertiliser fraud in Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
The Kano Zonal Directorate of the Economic and Financial Crimes Commission, EFCC, has arraigned one Sanusi Hashim for allegedly misappropriating and converting to his personal use, the sum of 108 million Naira.
KANO FOCUS reports that Hashim was arraigned before Justice Kabiru Dabo of the Kaduna State High Court sitting in Zaria on a one -count charge of misappropriation contrary to Section 293 and punishable under section 294 of the Penal Code.

He was alleged to have collected a total sum of 108 million Naira from one Ahmad Mohammad Liman and Basiru Mohammad for the supply of fertilizer but instead misappropriated and diverted the money for his personal use.
The lone-count charge reads ‘’That you Sanusi Hashim sometime in April 2020 under the jurisdiction of the Kaduna State High Court dishonestly misappropriated and converted to your own use, the sum One Hundred and Eight Million Naira (N108,000,000) property of one Ahmad Mohammad Liman and Basiru Mohammad for the supply of fertilizer from Indorama Eleme Fertilizer and Chemicals and you thereby committed an offence under Section 293 and punishable under Section 294 of the Penal Code’’.
The defendant pleaded not guilty when the charge was read to him.
Counsel to the prosecution, Bright C. Ogbonna prayed the court for a trial date in view of the defendant’s plea.
Consequently, Justice Dabo remanded the defendant in a Correctional Centre and adjourned the matter to February 10, 2025 for hearing of bail application.
