Connect with us

Hausa

Tambayoyi 10 da shugaba Buhari zai amsa da kansa

Published

on

By Salisu Ismail Kabuga

Tabbas idan kaji korafi akwai rashin gamsuwa kamar yadda indai kaji tambaya akwai abinda ya shigewa mutum duhu.

Assalamu Alaika Ya Shugaba Muhammad Buhari. Shugaban Najeriya.

Duba da ya yanayin yadda lamarin tsaro da sauran harkokin rayuwa, Wadanda sai da rai da lafiya ake batunsu suka kara tabarbarewa a Najeriya, Musamman Arewa.

Yadda batun Ta’addanci da zullumin kai farmaki a garuruwa da hanyoyi, da wajajen noma ko wajajen neman halak (Kasuwanni) suka kara jefa rayuwar Takala cikin kunci, Sune dalilan rubuta wannan Wasika “Kai-Tsaye” cikin girmamawa gare ka.

Abinda yasa wannan wasika ta zama “Kai-Tsaye” kuma da sigar tambaya gare Ka ya Shugaban Najeriya Muhamnadu Buhari shi ne, Mu dai a Muslinci munkwana da sanin cewa akwai abinda aka yadda wani zai iyayi a madadin wani, Yayin da wani lamarin kuma kowa sai dai yayiwa kansa, Ma’ana wani baya wakiltar wani.

Haka kuma, Su kansu a abubuwan da ake iya bada wakilcin matukar akwai abinda ya shiga duhu tsakanin wanda aka aikawa wakilin da kuma wakilin, akwai damar tafiya kai tsaye zuwa ga wanda ya bada wakilcin.

Wannan shi ne dalilin neman wannan amsar daga gare ka Shugaban mu, Muhammadu Buhari domin kaine wanda Al’umar Najeriya muka dankawa Amanar jagorancin mu.

Mai Girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Kasan cewa dukkannin Dan Adam Gajiyayye ne kuma Ajizine, Yakan dada himma ko ya rage a Al’amuran rayuwa, Hakan yasa Amsa wadannan (TAMBAYOYI GUDA 10) da kanka nake da yakinin ko ba komai wata hanyace da za kasan matsayin da Kake wanda mu kuma Yan’Najeriya muma zamu fa’idantu wajen ganin sauyi a zahiri yayin da Allah ya baka ikon amsawa kanka-da-kanka wadannan TAMBAYOYI wadanda basa bukatar wakilcin wani mukarrabin Ka.

Ga Tambayoyin daya-bayan-daya, wadanda Allah yasa ni ban yisu da kudurin izgili ko wata manufa ba, face na ganin Al’amuran kasa sun gyaru, wadan da kuma nake fatan zasu samu duba na tsanaki.

{1} Ya Shugaba Muhammadu Buhari, Anya kuwa Kana iya tuna yadda a baya kafin mu zabe ka, Ka dinga kushewa Shugabannin baya saboda abinda mu da Kai muka yadda sakaci ne wajen iya jagorancin Yan’Najeriya ?

{2} Anya kuwa Kana tuna yadda Ka dinga bibiyar Yan’Najeriya domin mu yarda zaka iya share mana hawaye har muka aminta muka baka Amanar kanmu data rayuka da dukiyoyin mu da hakkin kare mutuncin mu a 2015 ?

{3} Anya kuwa Kana iya tuna rahotannin yadda tsaffi masu shekaru da yawa (Old-ages) da Mata masu juna biyu (Pregnant women) da yadda wadansu daga cikin wadan da ke jinya a Gida dana Asbitoci suka rarrafa suka je suka wuni a layin zabe cikin ishurwa da yunwa da zafin rana domin zabar Ka ?

{4} Anya kuwa Kana iya tuna yadda Yan’Najeriya (Talakawa) suka ki ci, Suka ki sha, Suka dinga kankare kati domin aika maka da tallafin kudi domin Ka kai ga Nasara a zaben 2015 ?

{5} Anya kuwa Kana iya tuna yadda rashin lafiya wadda tana kan kowa ta same ka, Jin kadan bayan an zabe ka, Talakawan da suka zabe Ka suka kasa zaune suka kasa tsaye a gidajensu da makarantunsu da Masallatai da Majalisu dare da rana suka dinga yi maka addu’a domin ka samu lafiya ka futar dasu daga takaici ?

{6} Anya kuwa Shugaba Buhari a matsayin Ka na Musulmi kana iya tuna kalaman dake cikin rantsuwar kama mulki da ka saba lokutan rantsar dakai a Abuja da sauran jawaban da kayi a ranar ?

{7} Shin Shugaba Buhari Kama yarda cewa Najeriya da Yan’Najeriya musamman Talakan Arewa na cikin mawuyacin hali da zullimin tsaro ?

{8} Ya Shugaba Muhammadu Buhari shin Kasan cewa yin tallaki domin jajantawa da yin sannu hadi da addu’a ga wanda ke cikin damuwa koda bazai samu waraka ba abune mai dadi ga wanda ke cikin irin wannan hali? Kamar yadda sanda ka kwanta rashin lafiya a Landan Talakawan ka sukai tayi maka addu’a harda yin yanka da bada sadaqa, wanda nasan a lokacin inda ace Birnin Landan kamar nisan Jakara zuwa Gauron Dutse yake da duk da baza’a basu damar ganin ka ba, dasun yi dafifi a garin da kake jinya domin nuna Alhini amma Kai gashi gari ya gari, jirgi kawai zaka hawo ka jajantawa Katsinawa da Sokkwatawa da sauran gururuwan Arewa amma abin ya faskara.

{9} Har ila yau, Anya kuwa Buhari a matsayin Ka na Musulmi wanda ya samu tarbiyyar Kasar Hausa, Kayi makarantar addini kamar yadda duk Musulmi keyi, Ka yarda cewa akwai hisabi bayan mutuwa kuma cikin hisabin za’a tambayeka duk abinda kayi dama wanda yaki yi wanda a dalilin hakan rayuwar mutane da mutuncin su ke salwanta ?

{10} Shin sai a wanne lokacin ne Shugaba Buhari Kake zatan Alkawura da kuma kyawawan kudurori da ka zawarci kuri’un Yan’Najeriya sazu cika, In kuma kai kanka ya yanke haso, abin yafi karfin ka to yaushe zaka yiwa Yan’Najeriya bayani kai tsaye saboda musan mataki na gaba ?

Wadannan suke jerun Tambayoyi ko kuma ka lallesu a matsayin tuhumar da indai Allah ya baka iko ka iya amsawa Kanka-da-Kanka su kuma ka dauki matakin da ya dace yanzu-yanzu to kuwa nan take muma zamu ji amsar a jikin mu da kuma ganin amsar da idan mu, domin amsar Tambayoyin kamar yadda nace a aikace Yan’Najeriya zamu gani.

Allah ya baka ikon dubawa dana daukar matakin da ya dace akan lokaci.

Ko wanne Dan kasa da iyakacin aikin da hurumin kundun mulki ya sahale masa, wannan shine nawa hurumin a matsayin na na Dan Jarida mai fatan ganin Kasata, Najeriya ta kyautatu.

Comrade Salisu Ismail Kabuga salkabuga@gmail.com
+2348052529040

Hausa

Mutane 18,000 sun amfana da aikin ido kyauta ta Gidauniyar Mangal a Katsina

Published

on

 

Kimanin marasa lafiya masu rauni 18,000 da ke fama da cututtukan ido daban-daban a jihar Katsina sun amfana da ayyukan kulawar ido da tiyata kyauta da Gidauniyar Mangal ta dauki nauyi tun bayan kafuwarta a shekarar 2016.

 

Wani mamba na kwamitin amintattu (Board of Trustees) na gidauniyar, Malam Hussaini Kabir, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin kaddamar da aikin tiyatar ido na zangon karshe na shekarar 2025 a Cibiyar Ido ta Katsina.

 

Kabir ya bayyana cewa kimanin mutane 7,000 ne suka amfana a shekarar 2025 kadai, daga sassan jihar Katsina, jihohin makwabta, har ma da wasu yankuna na Jamhuriyar Nijar.

A cewarsa, gidauniyar ta fara tantance wadanda za su amfana kimanin makonni biyu da suka gabata, inda marasa lafiya da dama suka samu magunguna kyauta da tabarau na likita.

 

Kabir ya kara da cewa wadanda ke bukatar tiyata an dauki nauyin dukkan zaman asibitinsu gaba daya, yana mai cewa kimanin marasa lafiya 2,000 aka tantance a yayin aikin zangon karshe da ake ci gaba da yi.

Ya sake jaddada kudirin gidauniyar na inganta samun kulawar lafiya, yana bayyana shirin a matsayin wani bangare na nauyin alhakin zamantakewar kamfanoni (corporate social responsibility).

 

“Manufarmu ita ce tallafa wa kokarin gwamnati tare da rage nauyin kudin kula da lafiya ga mafi rauni, musamman wadanda ke fama da matsalar biyan bukatun rayuwa,” in ji shi.

Wani likitan ido a cibiyar, Dokta Ahmad Hamza, ya bayyana cewa an gano marasa lafiya da dama na fama da cutar idon toka (cataract) da glaucoma, cututtuka da galibi ke bukatar tiyata.

 

Ya jaddada muhimmancin duba ido akai-akai, yana mai cewa gano cuta da wuri na taimakawa wajen hana asarar gani ta dindindin da cututtukan ido masu zuwa a boye ke haifarwa, kamar glaucoma, cataract da lalacewar macula (macular degeneration).

Daya daga cikin wadanda suka amfana, Malam Yusufa Usman, ya ce ya shafe sama da shekaru biyu yana fama da matsalar gani amma ba shi da ikon biyan kudin tiyata.

 

“Tsawon shekaru biyu ban iya gani sosai ba, amma yau na yi tiyata kuma ina da fatan ganina zai dawo.

Ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya saka wa Gidauniyar Mangal da alheri bisa wannan kyakkyawan aiki.

 

“Ina fatan sauran masu kudi za su yi koyi da wannan abin a yaba,” in ji Usman.

Wata mai amfana, Aisha Muntari daga kauyen Bakuru, ta bayyana kwarewarta yayin da take jiran a kai ta dakin tiyata.

 

Muntari ta ce ta kamu da matsalar ido kimanin shekara guda da ta wuce kuma ta kusa yanke tsammani kafin ta samu labarin shigar gidauniyar, tana mai bayyana kwarin gwiwar cewa nan ba da dadewa ba ganinta zai dawo.

Continue Reading

Hausa

FG kickstarts construction of Emerging Technologies Institute in Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

As part of significant milestone in the Federal Government of Nigeria’s efforts to secure the socio-economic wellbeing of the future generation, as the ground was opened for commencement of construction of the Sustainable & Emerging Technologies Institute (SETI) under the aegis of the National Agency for Science and Engineering Infrastructure (NASENI), The Presidency.

 

KKANO FOCUS reports that the Executive Vice Chaiman/Chief Executive Officer (EVC/CEO) of NASENI, Mr. Khalil Suleiman Halilu during the Ground-breaking ceremony held at the Bayero University Kano (BUK) New Campus said the new institute sits on 30 hectares of the BUK land to be built, featuring state-of-the-art facilities, including innovation hubs devoted to Artificial Intelligence and other cutting-edge technologies, complemented by reliable power supply. “NASENI will fully build and equip and support the new Institute” said the EVC/CEO.

 

The future of socio-economic development for nations rests on human creativity, innovation and cooperation, Artificial intelligence, robotics amongst others.

 

Halilu said that the establishment of SETI in Nigeria is to rapidly respond to the waves of young people globally revolutionizing world economies with unprecedented emergence of socio-economic frontiers as by-products of innovations and ingenuities of these young minds.

 

“We in NASENI are firm believers in the potential of young Nigerians to be the prime catalysts of the type of transformation that Nigeria requires. And we will do everything within our powers to support them to fulfil this important responsibility”

 

“We are gathered here today to kickstart a project that will transform the lives and careers of future generations of young Nigerians. The Sustainable & Emerging Technologies Institute (SETI), located at the Bayero University Kano (BUK) by NASENI. This is very much in line with our operating principles; what we call our 3Cs: Collaboration, Creation, and Commercialization. These 3Cs are the principles that passionately drive us and guide the work that we do to ensure the industrialization of Nigeria in line with the Renewed Hope agenda of President Bola Ahmed Tinubu.”

 

SETI will produce innovators, technologists, entrepreneurs who will make their mark not just in Nigeria but around the world. “I’m eagerly looking forward to the day, not too long from now, when the Institute’s first set of beneficiaries will astonish the world with what they’re capable of accomplishing. These stories will put not just BUK on the global innovation map, but also Kano State and the entire Nigeria” said Halilu.

 

While carrying out the symbolic foundation laying ceremony of the institute as Special Guest of Honour, the Minister of Innovation, Science and Technology, Chief Uche Geoffrey Nnaji, described the project as not only laudable but NASENI’s another way of fast-tracking  the placing of Nigeria on the global map of innovation and industrialization. The minister called the project an “ace project” and a pointer to secure a veritable socio-economic development for the nation.

 

In his goodwill message, the Vice Chancellor of BUK, Professor Sagir Adamu Abbas described the new institute as a vehicle for bringing together the three critical tripods for economic and sustainable development for nations, that is, the government, academia and industry. He described the ground-breaking event as the beginning of Nigeria’s journey in pursuit of sustainable development, massive job creation opportunities for the youths, and that the BUK was delighted to be host to such laudable initiative and momentum.

 

There is also, in addition to SETI, a second NASENI project for BUK is an Agri-preneurship Training Hub, that will be equipped with modern greenhouses, and facilities for Soil-less Farming, and Tissue Culture; occupying 10 hectares of land at the Old Campus. These projects collectively represent what NASENI stands for, that is, building capacity, advancing industrialization, supporting economic growth and prosperity.

 

NASENI appreciates the Government and people of Kano State, and the Vice Chancellor, management and students of Bayero University Kano (BUK), for all the support. Special gratitude goes to the Honourable Minister of Innovation, Science and Technology, Chief Uche Geoffrey Nnaji, the Special Guest of Honour.

 

NASENI thanked members of the National Assembly for their support, especially the NASENI oversight Committees in both chambers. And of course, President Bola Ahmed Tinubu, who has given NASENI the opportunity to serve Nigeria through his unwavering demonstration of commitment to the success of the Agency.

Continue Reading

Hausa

Illar siyasantar da harkar tsaro da zaman lafiya a jihar Kano

Published

on

Jaafar Jaafar

 

Na jima ban ga tsantsar rashin kishi da cin amanar aiki da ya wuce ƙaryar da hukumar yansandan jihar Kano ta gilla ba saboda tsananin siyasantar da harkar tsaro da zaman lafiya da cigaban al’umma.

 

Babu wani rahoto na sirri kan wani mugun abu da ke faruwa a birni ko ƙauye wanda gwamna bai san shi ba. A wasu lokutan ma gwamnan ya kan riga jami’an tsaro samun wani rahoton sirrin. Duk wanda ya san yadda “special service directorate” (wadda ke karkashin ofishin gwamna) ke gudanar aiki, zai fahimci inda na dosa.

 

Kasashen da su ka ci gaba, ba sa wasa da duk bayanin da hukumar yansanda ta fitar. Domin su a kasashen su dansanda shi ya fi kowa adalci, shi ya sa zai wahala yansanda su tuhume ka da laifi ka ga alkali bai ɗaure ka ba.

 

Kafin harin Boko Haram na farko a Kano a ranar 20 ga Janairu 2012, akwai wani babban jami’in gwamnati da ya faɗa min cewa ƙasar Amurka na duba yiwuwar buɗe ƙaramin ofishin jakadanci (consulate) a Kano wanda zai riƙa ba da visa da gudanar da wasu shirye-shirye a jihar Kano. Kwatsam sai a ka kawo harin bam. Daga nan maganar ta mutu murus. A tunaninka in da a ce Amurka za ta sake duba yiwuwar bude consulate a Kano, sai ta ji sanarwar hukumar yansanda ta fitar, me ka ke tunanin za ta yi? Za ta fasa ne!

 

Haka fa muna ji muna gani British Council ta rufe cibiyarta da ke Kano. Wannan cibiya ta taimaka gaya wajen sa wa matasa sha’awar karatu, kuma ta samar da damarmaki na karatu da tafiye-tafiyen nazari kasashe ga mutane da dama. Ita ma wannan cibiya a dalilin rashin tsaro yanzu ta tattara inata-inata ta tafi.

 

Ta fuskar kasuwanci, watakil wannan sanarwar karyar da hukumar yansanda ta fitar ta sa masu son zuba jari daga wasu wurare (foreign investors) su fasa. Haka zalika, watakil wannan asarar ta sa masu zuwa fatauci kasuwannin Kano su ja jiki. Ka ga sun jawo wa yan kasuwa da jihar asara.

 

Tarihi ya nuna tun kafin Kano ta yi shuhura a harkar kasuwanci, Katsina ita ce cibiyar kasuwanci a kasar Hausa. Babban abin da ya sa Katsina ta koma baya shi ne yaƙe-yaƙe da ta sha fama da shi, musanman a ƙarni na 18.

 

Kira na ga gwamnatin jihar Kano shi ne kada ta bar wannan cin amana ya wuce ba ta yi wa tufkar hanci ba. Kamata ya yi gwamna da kan shi ya kira gagarumin taron zantawa da yanjarida wanda ya ƙunshi manyan gidajen jaridu na ƙasa da waje domin fayyace wa duniya zancen. Idan ma da yiwuwar kai yandansan kotu, to yakamata gwamnati kada ta yi ƙasa a gwiwa.

 

Allah Ya zaunar da mu lafiya.

Jaafar Jaafar, shi ne mawallafim jaridar Daily Nigerian, ya kuma wallafa wannan rubutun ne a shafinsa na Facebook. 

 

Continue Reading

Trending