Connect with us

Hausa

Rufe kogin Tiga: Za a samu matsananciyar tsadar tumatur a Kano

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Manoman tumatir a Jihar Kano sun ce nan gaba farashinsa zai yi tashin gwauron zabo saboda rufe Madatsar Ruwa ta Tiga da ke samar musu da ruwa domin noman rani.

KANO FOCUS ta ruwaito Manoman sun ce tun bayan da aka rufe madatsar ruwan a ranar 1 ga watan Nuwamban bara harkokinsu noman rani suka ja baya.

A cewarsu dole wadansu suka bar gonakinsu ba tare da nomawa ba, saboda rashin ruwa.

Galibin masu manoman tumatir na rani sun koma wadansu wuraren da ke kusa da ruwa domin ci gaba da harkokinsu.
Sai dai duk da cewa wasu sun samu wurin noman amma bubu isassu, a cewar manoman.

Wani mai sayar da kayan lambu a Kasuwar Kayan Gwari ta ’Yan Kaba a Kano, Mansur Bello Seemon, ya ce a halin yanzu ana kawo musu tumatir ne daga Zariya da wasu sassan jihohin Katsina da Kano.

A yanzu haka dai ana sayar da babban kwandon turmatir N10,300, sabanin farashinsa na N3,100 a irin wannan lokaci a bara.

“Bara ko’ina ka duba a kasuwar nan tumatir ne, amma tun da aka rufe Madatsar Ruwa ta Tiga muka koma sayowa daga Katsina da Zariya.

“Yanzu babban kwandonsa N10,200 ne kuma bisa dukkan alamu tumatir zai yi tsada matuka a bana,” inji Seemon.

Rahotanni sun nuna rashin ruwan noman rani ya sa manoma da ke aiki a filin noman rani na Kadawa mai fidin kadada 22,000 sun yi kaura.

Wasu daga cikinsu sun koma wuraren da ke da kusanci da ruwa a gabar Kogin Kano domin ci gaba da noman tumatir.

Shugaban Kungiyar Manoman Tumatir ta Najeiya (TOGAN), Alhaji Sani Danladi Yadakwari, ya ce gonakin da manona suka noma a Kadawa ba su kai kashi 10 cikin 100 na gonankinsu ba, a sakamakon rufe Madatsar Ruwar ta Tiga.

Ya ce manoman na cikin tsaka mai wuya, wanda ke iya haifar da karancin tumatir da kuma tsadarsa.

“A sakamakon rufe madatsar, wasu mambobinmu sun koma wuraren da ke kusa da ruwa domin ci gaba da noman tumatir, amma bai kai abin da aka noma a filin Kadawa bai kai kashi 10 cikin 100 da abin da aka noma a bara ba,” inji Yadakwari.

Shi ma wani manomin na tumatir, Malam Abdullahi Garba, ya ce shi da yawancin takwarorinsa ba su yi noma ba a bana.

Ya ce rufe madatsar ta sa sun kasa samun inda za su noma, saboda haka sai dai jama’a su yi hakuri, domin bisa dukkan alama zai yi tsada nan gaba.

A nata bangaren, Hukumar Kula da Kogin Hadejia Jama’are (HJRBDA) da ke da alhakin kula da madatsar, ta bayyana cewa rufewar ta zama dole, domin tana matukar bukatar gyara.

Kakakin hukumar, Salisu Baba Hamza ya ce akwai kwararan dalilan da rufe madatsar ruwan gaba daya.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

EFCC arraigns one for N108 million fertiliser fraud in Kano

Published

on

Sanusi Hashim

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

The Kano Zonal Directorate of the Economic and Financial Crimes Commission, EFCC, has arraigned one Sanusi Hashim for allegedly misappropriating and converting to his personal use, the sum of 108 million Naira. 

 

KANO FOCUS reports that Hashim was arraigned before Justice Kabiru Dabo of the Kaduna State High Court sitting in Zaria on a one -count charge of misappropriation contrary to Section 293 and punishable under section 294 of the Penal Code.

 

He was alleged to have collected a total sum of 108 million Naira from one Ahmad Mohammad Liman and Basiru Mohammad for the supply of fertilizer but instead misappropriated and diverted the money for his personal use.

 

The lone-count charge reads ‘’That you Sanusi Hashim sometime in April 2020 under the jurisdiction of the Kaduna State High Court dishonestly misappropriated and converted to your own use, the sum One Hundred and Eight Million Naira (N108,000,000) property of one Ahmad Mohammad Liman and Basiru Mohammad for the supply of fertilizer from Indorama Eleme Fertilizer and Chemicals and you thereby committed an offence under Section 293 and punishable under Section 294 of the Penal Code’’.

 

The defendant pleaded not guilty when the charge was read to him.

 

Counsel to the prosecution, Bright C. Ogbonna prayed the court for a trial date in view of the defendant’s plea.

 

Consequently, Justice Dabo remanded the defendant in a Correctional Centre and adjourned the matter to February 10, 2025 for hearing of bail application.

Continue Reading

Hausa

Gov. Yusuf Directs Reassigned Commissioners to Handover and Assume Duties by Tuesday, 17th December

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

The Governor of Kano State, Alhaji Abba Kabir Yusuf, has directed all reassigned commissioners to ensure a smooth handover and assumption of duties by Tuesday, 17th December 2024.

Speaking through his spokesperson, Mr. Sanusi Bature Dawakin Tofa, the Governor stated that the cabinet changes will take full effect during the next council meeting on Wednesday, 18th December 2024.

He emphasized the need for the completion of all transition processes before then.

“All commissioners affected by the changes are directed to hand over their responsibilities between Monday, 16th and Tuesday, 17th December 2024,” the statement reads.

The Governor further urged members of the state executive council to redouble their efforts and uphold a strong spirit of teamwork, dedication, and commitment to supporting his administration in serving the good people of Kano State.

Continue Reading

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Trending