Hausa
Shigar Osinbajo masallaci da takalmi ya tada kura a Kano
Mukhtar Yahya Usman
Al’umma a Kano na ci gaba da yin tofin ala tshine ga mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo bayan da ya shiga masallaci da takalmi.
KANO FOCUS ta ruwaito mataimakin shugaban kasar ya zo Kano ne ranar Talata domin halartar taron tunawa da Sardaunan Sokoto da kuma ta’aziyyar manya da suka rasu.
An dai hango hoton mataimakin shugaban a masallacin Darul Hadith da ke Unguwar Tudun Yola sanye da takalmisa akan kujera, bayan da ya ke ta’aziyyar Dr Ahmad Ibrahim BUK da ya rasu a Juma’ar Makon jiya.
Kodayake galibin masu yin tofin alatsinen na dora laifin ne akan gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da ministan sadarwa Isa Ali Pantami da suka gaza nusar da mataimakin shugaban kasar bukatar cire takalminsa yayin shiga masallaci.
A cewar Yasir Ramadan Gwale “Obama ma da zai shiga Masallaci sai da ya cire takalmi, watakila saboda ya girmama Musulmin da suke Sallah a ciki saboda ya san suna cirewa in zasu shiga.
“Amma shi Osinbajo ba wanda ya iya ce masa ya tube takalmi, Musulmi basa Sallah da takalmi akan dadduma.
“Gaskiya cin fuska ne ana kallonsa da takalmi amma ba wanda ya nuna masa ya cire alhali duk ‘yan tawagar kowa ya cire nasa da zai shiga.
“Abin tambaya anan Masallacin Villa da Shugaban kasa idan zai shiga sai ya cire takalmi, shin in dalili yasa Osinbajo zai shiga, shima da takalminsa zai shiga alhali shugaban kasa ya cire nasa a waje?
“Ya kamata ace Mataimakin shugaban kasa ya zama very diplomatic a lokacin da yake neman Musulmi su yarda da shi saboda yana da bukata a 2023” a cewar Yasir Ramad Gwale.
Shi kuwa Bashir Muhammad cewa ya yi shiga Masallaci da takalmi mai tsafta ba Laifi Bane.
“Haƙiƙa hotunan da ake ta yadawa, ba ‘wai’ tayar da hankali suke yi na sosai ba – sabida ba akan Osinbajo aka fara ganin haka ba.
“To amma, hakan ba ya nufin cewa duk lokacin da wani ya aikata haka, ba za a kalle shi a matsayin wanda bai aikata wani na ba-wai ba.
“Ko da shiga cikin Masallaci da takalmi (idan musamman ana da yaƙinin cewa yana da tsarki) ba laifi ko matsala bane.
“Yana da kyau ace su Ganduje da Pantami, sun fada masa cewa “ranka ya dade, ana dan cire takalmi idan za a shiga.”
“Wannan kuwa, sabida martaba Masallatan da muke dasu; da kuma kyakkyawar tarbiyyar da muke ita, ta tsaftace wuraren bautar mu” a cewar Muhammad Bashir.
Shi kuwa Ali Imam ya wallafa cewar baya goyon bayan shiga masallaci da takalmi da mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya aikata.
Sai dai ya ce wasu na fakewa da hakan suna cin zarafin Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje tare da dora masa laifi.
“Dama karamin sani kukumi ne. Wanda idan muka ratsa duniyar ilmi za mu ga cewa shiga masallaci da takalmi ba aibu ba ne.
“Akwai nassosin da suka nuna yin sallah da takalmi ma babbar sunnah ce matukar babu najasa a tattare da shi.
“Bukhari da Muslim sun rawaito cewa Sa’id Bin Zaid ya tambayi Sayyaduna Anas RA ko Manzon Allah SAW ya kasance yana sallah da takalmi? Sai ya amsa cewa Eh yana yi.
عن أبى سلمة سعيد بن زيد قال: سألت أنساً: “أكان النبي -صلى الله عليه وسلم- يصلي في نعليه؟. قال: نعم”.
Abu Dauda ya rawaito cewa daga Shaddadu dan Ausu Manzon Allah ya ce ku sa’ba wa Yahudawa domin su ba sa sallah cikin takalmansu da khuffofinsu.
عن شداد بن أوس رضي الله عنه قال: قال رسول الله -صلى الله عليه وسلم-: “خالفوا اليهود فإنهم لا يصلون في نعالهم ولا خفافهم”
Imam Ahmad da Abu Dauda sun fitar da shi daga Abu Sa’id Alkhudry Manzon Allah SAW ya ce idan d’ayanku ya zo masallaci ya duba takalminsa idan ya ga datti ko kazanta ya tsaftace su, sannan ya yi sallah da takalminsa.
أبو سعيد الخدري أنه قال: قال رسول الله -صلى الله عليه وسلم-: “إذا جاء أحدكم إلى المسجد فلينظر فإن رأى في نعليه قذراً أو أذى فليمسحه وليصل فيهما”.
Abu Dauda ya fitar an karbo daga Abuhuraira RA cewa Manzon Allah SAW ya ce” Idan dayanku ya yi sallah zai iya cire takalminsa, amma kar ya cutar da kowa da hakan, idan ya so zai iya ajiye su tsakanin kafafuwansa ko ya yi sallah suna kafafunsa.”
وما رواه أبو داود من حديث أبي هريرة أن الرسول -صلى الله عليه وسلم- قال: “إذا صلى أحدكم فخلع نعليه فلا يؤذ بهما أحداً، ليجعلها بين رجليه أو ليصل فيهما”
Kazalika hadisi ya inganta Annabi SAW yana jan sahabbansa sallah, sai ya cire takalmin da ke kafarsa. Da sahabbai suka ga haka sai su ma suka cire, bayan an gama sallah sai Annabi SAW ya tambaye su dalilin cire takalmansu sai suka ce sun ga ya cire nasa ne sai su ma suka cire nasu, sai Annabi SAW ya ce Jibrilu ne ya zo ya bayyana min akwai najasa a tare da takalmin sai na cire.
أبو سعيد الخدري أنه قال: “بينما النبي -صلى الله عليه وسلم- يصلي بأصحابه إذ خلع نعليه فوضعها عن يساره، فلما رأى ذلك القوم ألقوا نعالهم، فلما قضى رسول الله -صلى الله عليه وسلم- صلاته قال: ما حملكم على إلقاء نعالكم؟ قالوا: رأيناك ألقيت نعليك فألقينا نعالنا، فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم: إن جبريل عليه السلام أتاني فأخبرني أن فيها قذراً”
Wannan ya sa ake yin sallar Gawa da takalmi. Sai dai hakan ba zai saka na goyi bayan abin da Osibanjon ya aikata ba, amma abun sam bai kai yadda jama’a ke kwaza shi ba.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Kwankwaso Congratulates Gov. Yusuf on NUT Award for Education Reforms
Former Kano State Governor and National Leader of the New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabiu Musa Kwankwaso, has congratulated the current governor, Abba Kabir Yusuf, on receiving the prestigious NUT Golden Award from the Nigeria Union of Teachers (NUT) in recognition of his significant contributions to the education sector.
In a message posted on his verified X (formerly Twitter) handle, Kwankwaso commended Governor Yusuf for his unwavering dedication to revitalizing Kano’s education system.
He described the governor as a “game changer” in the sector and encouraged him to remain steadfast in pursuing his educational reforms.
“Congratulations to His Excellency Abba Kabir Yusuf on the NUT Golden Award for his achievements in the education sector,” Kwankwaso wrote.
He further urged Governor Yusuf to strengthen his commitment toward achieving his broader goals in education reform.
The award was presented during the 2024 World Teachers’ Day celebration, which took place at Eagle Square, Abuja.
Organized by the NUT in collaboration with the Federal Ministry of Education, the event brought together teachers and educational leaders from across Nigeria to recognize and celebrate significant achievements in education reform.
Governor Yusuf was honored with the NUT Golden Award for his transformative efforts in rescuing Kano’s education system, which had suffered from years of neglect.
His administration has been lauded for implementing policies aimed at improving school infrastructure, increasing access to quality education, and ensuring the professional development of teachers in Kano.
This recognition comes as part of a broader acknowledgment of his leadership and commitment to enhancing educational opportunities for all in the state.
The event, which marked the 2024 edition of World Teachers’ Day, highlighted the importance of teachers and their role in national development, with the NUT acknowledging the critical support of political leaders like Governor Yusuf, who are spearheading reform efforts.
The governor’s administration has undertaken various initiatives to address the challenges in Kano’s education system, including rebuilding dilapidated schools, recruiting more teachers, and prioritizing student enrollment, especially for girls.
Governor Yusuf’s receipt of the NUT Golden Award serves as a milestone in his administration’s ongoing efforts to reposition Kano as a leading state in education, setting an example for others across the country. His reforms have drawn praise.