Connect with us

Hausa

Rikicin APC a Kano: Matsayin da ake ciki akan sulhu – Shekarau

Published

on

Malam Ibrahim Shekarau

A’uzu Billahi Minashshaidanirr Rajim, Bismillahir Rahmanir Rahim, Ma Sha Allahu La Kuwwata Illa Billah. 

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wa Barakatuhu.

Ni Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano, kuma Sanatan Kano Ta Tsakiya, kuma jagoran ‘Yan Bakwan Alheri.

A madadin dukkan abokan tafiyarmu, ina mika godiyarmu ga Allah Madaukakin Sarki mai kowa mai komai, a bisa nasarori da yake bamu a cikin wannan gwagwarmaya da muke yi don tabbatar da adalci a cikin jam’iyyarmu ta APC a jahar Kano.

Babban burinmu  shi ne a tabbatar da tsarin gaskiya da adalci wajen samar da shugabanci a jam’iyyar APC a dukkan matakai ta hanyar mutuntawa, da girmamawa ga ‘yan jam’iyya, kuma yin hakan shi ne abin da zai haifar mana da gwamnati ta gari a gaba In Sha Allah.

Muna kara godiya ga dukkan magoya bayanmu da masu yi mana addu’o’i da fatan alheri.

Muna tabbatarwa al-ummar jahar Kano cewa wannan gwagwarmaya ba ta nufin cin mutunci ga kowa ko tozarta wani.

Ina amfani da wannan dama na tunasar da mu cewa Allah ne da kan Sa ya ce:- “Sulhu Alheri Ne”. Amma kuma Allah din a gurare da dama Ya yi kira a gare mu da mu zama masu hankali, masu tunani, masu tsari da adalci a dukkannin al-amuranmu, don haka a shirye muke da mu karbi tsarin sulhu a bisa rubutattun sharuda da za su tabbatar da adalci ga kowa a cikin jam’iyyarmu ta APC.

Kuma muna sanar da al’ummar Kano cewa, shugabannin jam’iyyar APC na kasa suna nan suna tattaunawa akan koke-koken da muka gabatar musu, musamman kuma gabobi na shari’a da nasara da muka samu a kotu, don haka muna kira ga dukkannin ‘yan jam’iyyarmu na APC da masoya da magoya baya da su kara hakuri tare da ci gaba da addu’ar Allah Ya samar mana da mafita mafi alheri a gare mu da Addininmu.

A bisa wannan yunkuri na jam’iyya da shugabanni na kasa, na samar da masalaha da samar da mafita a cikin wannan jayayya na jam’iyya a jahar Kano, shugabannin jam’iyya bisa jagorancin shugaban jam’iyya na kasa Mai Girma Gwamnan Jahar Yobe, suka neme mu don tattaunawa akan halin da ake ciki, wannan gayyata ita ce ta haifar da haduwarmu tare da shugabanni na kasa da kuma wakilan Mai Girma Gwamnan Jahar Kano, wadda aka yi a ranar Talata 25 ga watan January, wannan tattaunawa ba ta yanke wani hukunci ba, ba a yanke wata matsaya ba.

Mun tashi akan cewa za a ci gaba da tattaunawa bisa jagorancin shugaban jam’iyya, don haka muna tabbatarwa da al’umma cewar za mu ci gaba da sanar da su halin da ake ciki, kuma muna tabbatarwa al’umma cewar za mu tsare mutuncin ‘yan jam’iyyar APC akan kowane mataki tare da tabbatar da sharuda wanda za su tabbatar da adalci ga dukkannin ‘yan jam’iyya da kuma al’jmmar jahar Kano.

Allah Ya tabbatar mana da adalci a duk kannin matakai a tsakankaninmu, Allah kuma Ya ba mu lafiya da zama lafiya.

Wassalamu Alaikum Warahmatullahi Wa Barakatuhu!

Ibrahim Shekarau (Sardaunan Kano), kuma Sanatan Kano Ta Tsakiya, kuma jagoran ‘Yan Bakwan Alheri.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

An fake da taimako, ana yaɗa da’awar luwaɗi da maɗigo a jihar Kano!

Published

on

 

 

Misbahu Hamza

 

Zuwa Ga Gwamnatin Jihar Kano, Masarautar Kano, Hukumar Hisba, Da Ƙungiyar Mallaman Jihar Kano

Assalamu Alaikum,

Da sunan ƴancin ɗan Adam; da sunan nema wa ƴaƴanmu mata ƴanci da sana’a mai ɗorewa; da sunan taimakawa marayu, gajiyayyu da masu buƙata ta musamman, ana ta ƙoƙarin yaɗa da’awar luwaɗi da maɗigo a jihar Kano!

Ana yaɗa wannan manufa ne a bainar jama’a babu kunya ballantana ganin girmanku ko shakkarku a matsayinku na masu faɗa a ji a jihar Kano—a makarantu da unguwanni. Abin takaici ma har da ma a tsakanin ma’aikatun gwamnati (masu ɗamara)!

Ƙungiyar da ta ke ta wannan mummunan aiki a jiharmu ita ce “Women Initiative for Sustainable Empowerment and Equality.” Suna kiran kansu “WISE” a taƙaice kuma a bayanin da muka gani a shafukan su, har ofishi suke da shi mai zaman kanshi a Yankaba Kawaji, Bompai GRA, Kano.

A wani bayani da muka gani a shafukan wannan ƙungiya, mun ga sun taɓa haɗa bita wa jami’an Hisba, da na KAROTA, da na NDLEA, da sauransu!

Domin tabbatar da duk waɗannan abubuwa, a duba shafinsu kawai na Facebook mai suna “Wise Wage.”

In har wannan ƙungiya ta yi ƙarfin da za ta tara waɗannan jami’ai a wuri guda da sunan yi musu bita—a kan ko ma mene ne—to muna tsoron irin tasirin da suka riga suka yi a cikin jihar mu. Jihar musulunci.

Za ku iya tunawa a makon nan me ƙarewa ne ake ta dambarwar kuɗaɗe da gwamnatin tarayya ta karɓo daga ƙasashen Turai wanda ake zargin cewa ɗaya daga cikin sharuɗɗan amfana da wannan maɗuɗun kuɗaɗe shi ne a sakarwa masu da’awar luwaɗi da maɗigo mara, irin su WISE, su fantama baɗalarsu yadda suke so.

Wannan ya jawo kace nace a ƙasarnan. Kuma mun ga yadda Mallaman jihar Kano ku ka tashi tsaye a mimbari, kamar yadda muka yi tunanin za ku yi, domin yin tofin Allah tsine da wannan yunƙuri matuƙar ya tabbata gaskiya.

Wannan dambarwar ta ƙara bayyanar mana cewa a ƙasarnan akwai doka da kai tsaye ta yi hani da duk wani yunƙuri ko yaɗa manufar luwaɗi da maɗigo. Kuma mun ƙara samun natsuwa ganin yadda Musulmi da Kirista suka haɗa kai domin barranta da wannan ɓarna.

Da wannan muke kiran Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da Sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sanusi II, da Shugaban Hisba ta Kano, Mallam Aminu Daurawa, da Shugabancin Kungiyar Mallaman Jihar Kano, da su tabbatar wannan ƙungiya ta WISE ta tattara ƙomatsonta ta bar mana gari kuma a haramta mata aiki a jihar ta kowace hanya da za a iya.

Al’ummar jihar Kano amana ne a wajanku! Kuma Allah zai tambaye ku amanar da ya damƙa muku ranar alkiyama!

Mu mun yi namu—isar muku da saƙon. Idan da ba ku san da wannan kungiya ba ko aiyukanta, to yanzu mun sanar da ku.

Bissalam,

Misbahu Hamza

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Hausa

Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.

Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.

Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.

Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.

Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.

“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.

“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”

Continue Reading

Upcoming Events

There are no upcoming events at this time.

Facebook

Twitter

Trending