Hausa
Kano ba ta dace da APC ba – Bello Sharada
Bello Muhammad Sharada
A tarihi Kano gari ne na ilimi. Kano gari ne na addini. Kano gari ne na kasuwanci. Kano gari ne na sarauta. Kano gari ne ‘yanci da walwala da tarbiyya. Kano ana yi mata kirari da Tumbin Giwa, jallabar Hausa ko da me ka zo an fika. Limisliki alfun.
Ka auna tarihin Sarakunan Kano na Hausa da Sarakunan Kano na Fulani. Ka koma yadda Kano take bayan Turawan mulkin mallaka sun zo har suka ci mu da yaki a 1903 da lokacin da aka bamu ‘yancin kai a 1960, da sanda aka kirkiro jihar Kano a 1967, da zamanin soja na Audu Bako da Sani Bello da Ishaya Aboi Shekari kafin a baiwa farar hula mulki a jamhuriya ta biyu a shekarar 1979 da zamanin mulkin Rimi da Abdu Dawakin Tofa da Sabo Bakin Zuwo a tsakanin shekara biyar 1979-1984. Da yanayin da gwamnonin sojoji suka yi mulki a shekara 15 tun daga watan Augusta 1985 har zuwa watan Mayu 1999, aka yi gwamna Hamza Abdullah da Idris Garba da Ahmad Daku da Ndatsu Ummaru da Kabiru Gaya da Abdullahi Wase da Dominic Oneya da Aminu Isa Kwantagora basu saba da tsarin Kano ba sai a shekara bakwai da take hannun Hadimu.
Abin da ya jawo haka, an kauce tsarin Kaka da kakanni na siyasar Kano da tsarinta da dabi’unta. Jihar Kano ta dada sukurkucewa ne a zamanin mulkin APC na Gandujiyya. Duk girman Kano da daukakarta da yawan jama’a da Allah ya hore mata, mutum biyar ne kadai sai abin da suka shata, suka kitsa ko kana so ko baka so. Sun ce lokacinsu ne. Da sannu zasu tafi. Na farko gwamna Ganduje. Na biyu uwargidansa Farfesa Hafsat. Na uku Murtala Sule Garo. Na hudu Abdullahi Abbas. Na biyar Alasan Ado Doguwa. Mataimakin gwamna Ganduje sunansa ma Mota ba Fasinja saboda ba shi da wani tasiri, an ajiye shi safayar taya. Takarar gwamna da aka ba shi dole ce uwar naki. Shi kuma Usman Alhaji Sakataren gwamnati hoto ne. A gefe guda kuma suka dan dosana shugaban majalisar jiha Rt Hon Chidari. Wanda duk bai gamsu ba ya tambayi Dr Baba Impossible.
Babu wani abu da za a yi sai da izinin wadannan mutanen. Rigimar G7 da kafuwar NNPP ita ce kadai ta rage kaifin Goggo da Dan Sarki da Alasan Doguwa. Burin dan Sarki ya zama Sarki, burin Goggo kwamanda ya zama gwamna, burin Ganduje ya zama Sanata ko mataimakin shugaban kasa. Burin Alasan Ado Doguwa ya maye gurbin Femi Gbajabimilla.
SU biyar din nan kowa da bukatar da ta hada su. Zaka gansu jumlatan, amma zuciyoyinsu daban-dabam. Dukkansu suna jifan juna. Murtala ya taba keta Alasan, ya taba cakume Abdullahi Abbas, a kwanan nan kuma Alasan Ado sai da ya mari Murtala a gaban Gawuna kuma a cikin gidansa. Alasan zai iya zagin kowa da sunan siyasa. Hatta Ahmed Aruwa sai da Alasan ya hankade shi a gaban mahaifiyarsa. A gaban Abdullahi Adamu shugaban jam’iyya na kasa na APC da gwamna Ganduje ya hayayyako wa Sardaunan Kano, har suka yi cacar baki da Aliko Dan Shuaiba, aka shiga tsakani. Yan wannan guruf din sune suka tsangwami Barau, an kai matsayin da Sanata Barau bai isa ya zo taro ba a Kano sai dai ya yi harkarsa a Abuja. Kwanan nan Sanata Barau ya baiwa Ganduje kyautar miliyan 150.
Abin da ya nace APC ba ta dace da Kano ba, a wadannan shekarun ne gwamna Ganduje ya kalli manyan masu daraja ya keta musu alfarma, sannan ya kirasu da Dattawan Wukari. A wannan lokacin ne gwamna ya dauki aikin da aka zabe shi domin ya aiwatar amma ya danka shi a hannun uwargidansa, har kuma ta nada wanda zai gaje shi.
An kai matsayin da komai ba a yinsa daidai a Kano a mulkin Ganduje. In kuma ka tanka sai a daureka. Ko a saka wasu karnuka su yi tayi maka haushi. GA Kano garin kasuwanci an yanka kasuwa ko ina ba tsari. Kullum a cikin rigimar fili. Kano garin Sarauta, ita kanta masarautar an yi mata filla-filla, Alasan Ado Doguwa ma Sardaunan kasar Rano ne, da rawaninsa ma ya kwankwashi bakin Murtala. Kano garin malanta, Council of Ulama sai da aka yi mata kishiya, hatta halifancin Tijjaniya sai da aka kutsa ga na Sarki ga na gwamna. Siyasa kuma ba a zancenta, Rarara ya taba zambo da tsulan biri aka yi masa tafi. Ya yi habaici da duna aka yi masa dariya. Ya buga misali da hankaka ana shirin kulle shi.
Babu wani lamarin APC da ake yi cikin adalci. Kowa kuka yake yi. Ga shi kansa Mai gidan APC na kasa babu wani abin alheri mai girma da aka yi wa jama’ar Kano a saboda kauna da biyayya da goyon baya da suke yi masa tsawon shekara 18.
APC bata dace Kano ba. A 2023 Sai an canza da kuri’armu cikin yardar Allah.
Bello Muhammad Sharada jigo ne a Siyasar gidan Malam Ibrahim Shekarau
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Kwankwaso Congratulates Gov. Yusuf on NUT Award for Education Reforms
Former Kano State Governor and National Leader of the New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabiu Musa Kwankwaso, has congratulated the current governor, Abba Kabir Yusuf, on receiving the prestigious NUT Golden Award from the Nigeria Union of Teachers (NUT) in recognition of his significant contributions to the education sector.
In a message posted on his verified X (formerly Twitter) handle, Kwankwaso commended Governor Yusuf for his unwavering dedication to revitalizing Kano’s education system.
He described the governor as a “game changer” in the sector and encouraged him to remain steadfast in pursuing his educational reforms.
“Congratulations to His Excellency Abba Kabir Yusuf on the NUT Golden Award for his achievements in the education sector,” Kwankwaso wrote.
He further urged Governor Yusuf to strengthen his commitment toward achieving his broader goals in education reform.
The award was presented during the 2024 World Teachers’ Day celebration, which took place at Eagle Square, Abuja.
Organized by the NUT in collaboration with the Federal Ministry of Education, the event brought together teachers and educational leaders from across Nigeria to recognize and celebrate significant achievements in education reform.
Governor Yusuf was honored with the NUT Golden Award for his transformative efforts in rescuing Kano’s education system, which had suffered from years of neglect.
His administration has been lauded for implementing policies aimed at improving school infrastructure, increasing access to quality education, and ensuring the professional development of teachers in Kano.
This recognition comes as part of a broader acknowledgment of his leadership and commitment to enhancing educational opportunities for all in the state.
The event, which marked the 2024 edition of World Teachers’ Day, highlighted the importance of teachers and their role in national development, with the NUT acknowledging the critical support of political leaders like Governor Yusuf, who are spearheading reform efforts.
The governor’s administration has undertaken various initiatives to address the challenges in Kano’s education system, including rebuilding dilapidated schools, recruiting more teachers, and prioritizing student enrollment, especially for girls.
Governor Yusuf’s receipt of the NUT Golden Award serves as a milestone in his administration’s ongoing efforts to reposition Kano as a leading state in education, setting an example for others across the country. His reforms have drawn praise.