Connect with us

KANUN LABARAI

An Rufe wuraren badala biyar a Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

Kwamitin da gwamnatin Kano ta kafa dake kula da da  guraren shakatawa a jihar nan na gudanar da sana’ar su yadda ya kamata ya rufe wasu guraren shakatawa  biyar.

Wuraren shakatawar dai ana zargin su da fakewa da sana’a, suna aikata masha’a iri-iri, da suka hadarda sayar da miyagun kwayoyi, karuwanci da sauransu.

Shugaban kwamitin Alhaji Tahir Abdullah El Kinana ne ya bayyana haka ya yin zantawarsa da Kano Focus ranar Alhamis.

Ya ce guraren da aka rufe su ne ‘Snap Café’ da State Road da ‘Falamanki’ da ke titin Audu Bako da kuma ‘Coffee and More’ shima akan titin Audu Bako.

Ragowar sune ‘Macbanas’ dake Race Course da Bakori Motors a Katsina Road sai kuma ‘Plan Garden’ da ke Sokoto Road.

Ana dai zargin matasa da ‘yan mata na fakewa da sunan shakatawa a wadannan wurare su dinga yin shaye-shaye, da neman mata da dukkanin irin badalar da suka ga dama.

Hisba ta kama mabarata 178 cikin watanni uku a Kano

Gwamnatin Kano za ta samar da kotun tafi da gidanka a hukumar Hisba

Ranar yaki da kanjamau: Hisbah ta kama masu yada kanjamau sama da 40 a Kano

Ko a watannin baya ma sai da gwamnanti ta rufe wani gidan shakatawa mai suna 3 star a unguwar Badawa, da ya yi kaurin suna wajen tara karuwai, ‘yan shaye-shaye da sauransu.

“Mun fita ne saboda akwai abubuwan da ake a ‘Plan Garden na badala da suka saba da ka’idoji da addin da kuma al’adar Hausawa.

“Hakan ta sanyan hukumar Hisba ta sanar da mu irin hali da wuraren ke ciki mu kuma muka dauki matakin gaggawa.  a cewar sa.

Ya kara da cewa akwai korafe-korafe da dama game da abubuwan da suke faruwa a guraren shakatawar, da suka hada da zargin saida miyagun kwayoyi da aikata munanan dabi’u da suka ja aka rufe su.

“Hakkin wannan kwamiti ne akan duk wani abubuwa da ake yi a gefen titi don haka duk wani abu da zai zo ya bata kawata birnin Kano a gefen titi muna da hurumi mushiga ciki,” inji El Kenana.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending