KANUN LABARAI
Za a fara kamen wadanda ba sa sanya ‘Face Mask’ a Kano
Zulaiha Danjuma
Gwamnatin Kano za ta fara kama wadanda ke yawo ba tare da sanya takunkumin fuska ba wato (Face Mask) da ga ranar Laraba mai zuwa.
Kano Focus ta ruwaito dowo da dokar sanya takunkumin ya biyo bayan sake barkewar cutar ‘Kwarona’ a jihar Kano dama kasa baki daya.
A cewar mashawarci na musamman kan kafafene sadarwa na zamani ga gwamnan jihar Kano Salihu Tanko Yakasai, dama dokar ba sabuwa bace, kuma gwamnati batace ta janye ba, jama’a ne dai kawai suka yi watsi da ita.
Ya ce ya zama dole a dowa da dokar, duba da yadda annobar ta sake kunno kai, domin a kubutar da jama’a da ga hadarin kamuwa da cutar da kuma yadawa jama’a.
Salihu Tanko Yakasai ya ce ya zama wajibi ko wanne dan jihar Kano ya zama yana yawo da takunkumin fuska domin kare kai daga ibtila’in annobar.
“Gwamnatin jihar Kano taga ya kamata a dawo da dokar sanya takunkumin fuska, da kuma bada tazara tsakanin mutane, la’akari da barkewar korona a karo na biyu.
“Kuma umarnin gwamnati ya fara ne nan take, duk wanda bai sanya ba za a dauki mataki me tsananin a kansa” A cewarsa.
Haka zalika wata sanrwa da ke yawo a kafafene sada zumunta na zamani na nuna cewa za a fara kamen wadanda basu da takunkumin fuskarne daga ranar Laraba mai zuwa.
Hausa
Mutane 18,000 sun amfana da aikin ido kyauta ta Gidauniyar Mangal a Katsina
Kimanin marasa lafiya masu rauni 18,000 da ke fama da cututtukan ido daban-daban a jihar Katsina sun amfana da ayyukan kulawar ido da tiyata kyauta da Gidauniyar Mangal ta dauki nauyi tun bayan kafuwarta a shekarar 2016.
Wani mamba na kwamitin amintattu (Board of Trustees) na gidauniyar, Malam Hussaini Kabir, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin kaddamar da aikin tiyatar ido na zangon karshe na shekarar 2025 a Cibiyar Ido ta Katsina.
Kabir ya bayyana cewa kimanin mutane 7,000 ne suka amfana a shekarar 2025 kadai, daga sassan jihar Katsina, jihohin makwabta, har ma da wasu yankuna na Jamhuriyar Nijar.

A cewarsa, gidauniyar ta fara tantance wadanda za su amfana kimanin makonni biyu da suka gabata, inda marasa lafiya da dama suka samu magunguna kyauta da tabarau na likita.
Kabir ya kara da cewa wadanda ke bukatar tiyata an dauki nauyin dukkan zaman asibitinsu gaba daya, yana mai cewa kimanin marasa lafiya 2,000 aka tantance a yayin aikin zangon karshe da ake ci gaba da yi.

Ya sake jaddada kudirin gidauniyar na inganta samun kulawar lafiya, yana bayyana shirin a matsayin wani bangare na nauyin alhakin zamantakewar kamfanoni (corporate social responsibility).
“Manufarmu ita ce tallafa wa kokarin gwamnati tare da rage nauyin kudin kula da lafiya ga mafi rauni, musamman wadanda ke fama da matsalar biyan bukatun rayuwa,” in ji shi.

Wani likitan ido a cibiyar, Dokta Ahmad Hamza, ya bayyana cewa an gano marasa lafiya da dama na fama da cutar idon toka (cataract) da glaucoma, cututtuka da galibi ke bukatar tiyata.
Ya jaddada muhimmancin duba ido akai-akai, yana mai cewa gano cuta da wuri na taimakawa wajen hana asarar gani ta dindindin da cututtukan ido masu zuwa a boye ke haifarwa, kamar glaucoma, cataract da lalacewar macula (macular degeneration).

Daya daga cikin wadanda suka amfana, Malam Yusufa Usman, ya ce ya shafe sama da shekaru biyu yana fama da matsalar gani amma ba shi da ikon biyan kudin tiyata.
“Tsawon shekaru biyu ban iya gani sosai ba, amma yau na yi tiyata kuma ina da fatan ganina zai dawo.
Ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya saka wa Gidauniyar Mangal da alheri bisa wannan kyakkyawan aiki.
“Ina fatan sauran masu kudi za su yi koyi da wannan abin a yaba,” in ji Usman.

Wata mai amfana, Aisha Muntari daga kauyen Bakuru, ta bayyana kwarewarta yayin da take jiran a kai ta dakin tiyata.
Muntari ta ce ta kamu da matsalar ido kimanin shekara guda da ta wuce kuma ta kusa yanke tsammani kafin ta samu labarin shigar gidauniyar, tana mai bayyana kwarin gwiwar cewa nan ba da dadewa ba ganinta zai dawo.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
