Connect with us

KANUN LABARAI

Zaben Kananan hukumomin Kano zai lakume sama da Naira miliyan dubu biyu

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta kashe Naira biliyan biyu da miliyan dari uku wajen shirya zaben kananan hukumomin da ke tafe.

Kano Focus ta ruwito kwamishinan yada labarai na jihar Kano Muhammad Garba ne ya sanar da haka ga manema labarai jim kadan bayan kammala zaman majalisar zartarwa ta jihar Kano a ranar Laraba.

Muhammadu Garaba ya ce kudaden za ayi amfani da sune wajen sayan kayayyakin da za a gudanar da zaben, da sauran bukatu da ka taso yayin zaben.

Idan ba a manta ba dai a cikin makon jiya ne, hukumar zabe ta jihar Kano ta ce za ta gudanar da zaben Kananan hukumomi a ranar 16 ga watan Janairun shekara 2021.

Jadawalin zaben da hukumar ta fitar ya baiwa Jam’iyyun siyasa tsawon watanni uku su yi shirye shiryen da suka kamata domin tunkarar zaben.

Shugaban hukumar zaben Garba Ibrahim Sheka ya ce baya ga tsare tsare da ganawa da daukacin masu ruwa da tsaki domin samun nasara, hukumar ta fitar da farashin takardun shiga zabe ga ‘yan takara.

A wannan karon dai hukumar zaben ta Kano tace kamfanonin cikin gida zata baiwa kwangilar buga takardun zabe domin rage kudaden da take kashewa.

Tuni dai shugaban hukumar zaben ta Kano ya ce zai tabbatar da adalci ga dukkanin Jam’iyyu da zasu shiga zaben.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending