Connect with us

KANUN LABARAI

KEDCO ce ke jawo matsalar karancin ruwan sha a Kano-Water Board

Published

on

Zulaiha Danjuma

Hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano (KNSWB) ta ce rashin isashshiyyar wutar lantarki da hukumar KEDCO ke hana su ya sanya ake samun karancin ruwan sha a jihar Kano.

Kano Focus ta ruwaito shugaban hukumar Ahmad Garaba Kofar Wambai ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Talata a nan Kano.

Mista Wambai ya ce Hukumar sa na iya kokarinta wajen ganin ta wadata al’ummar jihar Kano da ruwan sha, amma Hukumar ta KEDCO na dakile kokarin nata.

“Basa bamu lantarki yadda ya kamata, kuma idan wani al’amari ya faru da za su janye lantarki basa gayamana da gaggawa domin musan abun yi sai dai kawai muga babu.

“Duk da cewa muna daya daga cikin manyan abokanan huldar su amma basa yimana abin da ya kamata.” A cewar Mista Wambai.

Sai dai yayin da Kano Focus ta tuntubi Kamfanin na KEDCO kan wannan zargi da ake yi masa, Kamfanin ya musanta zargin.

A cewar jami’in hulda da jama’a na Kamfani Sani Ibrahim Shawai, ko kadan matsalar rashi ruwa a jihar Kano bata da alaka da KEDCO.

Mista Shawai ya ce Hukumar na son daura musu jakar tsaba ne kawai domin sun gaza fahintar da al’umma dalilan su na hana su ruwan sha.

“Wannnan ma ai ba abin da hakali zai dauka ba ne, Hukumar Water Board tana kan tsarin bangarorin da suke samun wuta sama da ta awa ashirin a rana.

“Idan suna da wata matsala da suke ganin ta hana su samar da ruwa ga al’umma to su nemota amma ba batun wutar lantar ki ba.” Shawai ya ce.

Haka zakila Mista Shawai ya kara da cewa ba wannan ne karo na farko da Hukumar ke alakanta mtsalar da kamfanin na KEDCO ba.

 

 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Upcoming Events

There are no upcoming events at this time.

Facebook

Twitter

Trending