Connect with us

KANUN LABARAI

Kwankwaso ya budewa ‘ya’yan makiyaya makaranta a garin Rano

Published

on

Aminu Abudullahi

Tsohon gwamnan jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya  bude sabuwar makarantar firamare ta makiyaya mai dauke da azuzuwa shida a kauyen Munture da ke karamar Hukumar Rano.

Kano Focus ta ruwaito an gudanar da bikin bude makarantar ne tare da masallacin juma’a a Talatar nan.

An kaddamar da makarantar ne da dalibai dari uku da za a fara yin karatu da su.

Idan ba a manta ba tun a shekarar 2019 ne tsohon gwamnan Rabi’u yasamar da makarantar Islamiyya a kauyen na Munture wanda.

Baya ga samar da makaratar ne kuma ya dasa dambar gina makarantar Firamare da aka bude a yau.

Da yake jawabi yayin bude makarantar Rabi’u Musa Kwankwaso ya ya ce daliban da za a dauke za su yi karatu ne  kyauta.

Kwankwaso ya kuma ce nan bada jimawa ba za su samar da kwamfutoci a makarantar domin samar da ilimin na’ura mai kwakwalwa ga ‘ya’yan makiyayan.

Haka zalika ya ja hankalin iyaye da malaman da za su koyar a makarantar da su jajirce don samar da ilimi nagartacce ga yaran kauyen.

Haka kuma a nata bangaren gidauniyar Kwankwasiyya wato (Kwankwasiyya Development Foundation) ta ce za ta dauki nauyin malaman da za su dinga koyarwa a makarantar.

Wasu daga cikin al’ummar yankin sun bayyana jin dadin su bisa samun makarantar.

Malam Abdullahi Usman dattijo ne a kauyen mai kimanin shekaru 70 ya ce kafin samar da wannan makaranta ‘ya’yan su na tafiyar kilomita uku akafa zuwa makaranta da hakan ya sa suka daina zuwa baki daya.

Ya kara da cewa bai yi zaton ganin irin wannan ci gaba a kauyen na su ba.

Shima wani dattijo mai suna Muhammadu Tukur Adamu dan shekaru 65 ya ce ‘ya’yan sa basa zuwa makaranta saboda nisa amma samar da wannan makaranta yazama wajibi ya rinka tura ‘ya’yan sa makaranta.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending