KANUN LABARAI
Ra’ayi:Yanayin sanyi ke samu sanya takunkumin fuska a Kano ba cutar Korona ba
Zulaiha Danjuma
Jama’a da dama a nan Kano sunce yanayin sanyi da kura da ake fama dashi a wannan lokaci ke sanyasu sanya takunkumin rufe hanci wato ‘face mask’ amma ba cutar Koronaba.
A wani kewaye da jaridar Kano Focus tayi a wasu wurare na birinin Kano, ta gano yadda sanya takunkumin hanci ya karu a tsakanin mutane.
Da yake ana zamanin cutar Korana ne ya sanya jama’a da dam ke zaton ko ana sakawane domin magance kai daga kamuwa da cutar.
Sai dai dayawa daga cikin mutanen da aka tattauna da su sunce ko kandan badon kariya daga Korona suke sanya takunkumin ba sai dan maganin kura.

Bashir Usman wani mazaunin unguwar Sharada ya ce dama kafin billar cutar Korona yana sanya takunkumin fuska.
“Ni ba Korona ke sani sanya takunkumi ba dama can yana daga cikin dabi’ata sanyawa.
“Ko da Korona ko bubu ita zan ci gaba da sanyawa, kuma ni ina sakawane saboda maganin kura ba wata Korona ba.” A cewar sa.
Shi ma wani da aka iske na tafiya a kan hanya a unguwar Tukuntawa Rabi’u Isma’il da ke sana’ar dinki ya ce ko kadan baya sanya takunkumin fuska don cutar Korona.
“Indai ka ganni da takunkumin fuska to ba don kariya daga Korona na sanya ba sai dan kare kai daga kura da mura a lokacin sanyi.
“Kodayake lokacin da Korona ta bulla na sanya, saboda a lokacin an firgitamu da ita, da ko shago bana fita sai da shi, amma yanzu kam ko oho”
Shima wani dan kasuwa a unguwar Sharada Sadiq Isah ya ce Korona ba ta isa ta sanya shi sanya takunkumin fuska ba.
A cewarsa sanyi ne kawai da kura ke da ikon sanya shi sanya takunkumin fusaka.
“Ina sanya takunkumin fuska saboda kura, saboda bana son kura ko kadan

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
