KANUN LABARAI
Dole ne manyan makarantu su bi doka wajen yaki da cutar Covid-19 a Kano-Kwamishina
Mukhtar Yahya Usman
Gwamnatin Kano ta bukaci manyan makarantun jihar nan da su tabbatar suna bin dokoki da ka’idojin da hukumomi suka gindaya na yaki da cutar Covid-19 a makarantunsu.
Kano Focus ta ruwaito kwamishiniyar manya makarantu ta Kano Dakta Mariya Muhammad Bunkurece ta yi wannan kira ya yin taron bita kan yadda za a magance yaduwar cutar Covid-19 a manyan makarantun jihar nan a ranar Talata.
Kwamishinar ta ce ya zama wajibi manayan makarantun jihar nan sa baiwa bangaren kula da lafiyar daliban su fifiko a wawannan yanayi da ake ciki na yaduwar cutar Covid-19
A cewarta wannan ne ma yasa gwamnati bati yi kasa a gwiwaba wajen tallafawa makarantun da kayayyakin da za su yaki cutar.

Wasu daga cikin kayayakin da aka baiwa makarantun sun hadar da injinan wanke hannu, randuna, da sabulun wanke hannu, da takukunkumin fuska da kuma na’urar gwajin zafi.
Gwamnatin Kano za ta dauki malaman makaranta 2000
Ranar bandaki: Yadda matsalar bandaki ke tagayyar dalibai mata a makarantun Kano
Sarkin Karaye ya bukaci a gina makarantar horas da sojoji a masarautarsa
Haka zalika kwamishinar ta bukaci makarantun da su yi amfani da wadannan kaya yadda suka kamata, su kuma taimakawa gwamanti wajen yaki da wannan cuta.
Da yake nasa jawabin mataimakin shugaban kwamitin kartakwana na yaki da cutar ta Covid-19 a Kano, Dakta Sabitu Shuaibu Shanono ya ce gwamnati ta zabi yin wannan aiki ne domin dakile yaduwar cutar a tsakanin dalibai.
A cewarsa wannan mataki da aka dauka na cikin ayyukan da kwamitin nasu ya sanya a gaba.
Ya kuma godewa ma’aikatar manyan makarntu ta jiha bisa kokarinta na ganin ta kawo karshe cutar a manyan makarantun jihar nan.
Makarantun da suka amfana da wannan tallafi sun hadar da Jam’ar Yusuf Maitama Sule, Jami’ar Kimiyya da Fasaha da ke garin Wudil, da Kwalejin nazarin addinin Musulnici da shari’a ta Kano wato Legal.
Sauran sun hadar da kwalejin koyon ikin noma ta Audu Bako da ke garin Danbatta, sai kwallejin kimiyya ta jihar Kano, da kwalijin Ilimi ta Sa’adatu Rimi.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
