Connect with us

KANUN LABARAI

IAR ta samar da irin masara da ke jure fari, kuma tsutsa ba ta ci

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Cibiyar nazari da bunkasa al’amuran noma ta jami’ar Ahmadu Bello wato Institute for Agricultural Research (IAR) ta ce nan da shekarar 2022 za ta fito da sabon irin masara da ke jure karancin ruwa kuma tsuta ba ta iya ci da ake kira TELA maize.

Kano Focus ta ruwaito shugaban cibiyar Farfesa Isyaku Muhammad ne ya bayyana haka ya yin taron jin ra’ayoyin manoma kan yadda za a rungumi sabuwar fasahar da ya gudana ranar Talata a Kano.

Farfesa Isyaku ya ce matukar manoma suka rungumi wannan sabuwar fasaha to shakka babu za su samu amfanin masara da ya zarta wanda suka saba samu idan sun yi noma.

Ya ce cibiyar ta dade tana nazari kan yadda za a samar da wannan iri da zai taka rawa wajen inganta noman masara, ya kuma taimakawa manoma rage kudaden da suke kashewa wajen nomanta.

Sabuwar fasahar mafita ce ga manoma.

Farfesa Isyaku ya ce sau dayawa akan zo da sabuwar fasaha, kuma yana da wahala al’umma su karbeta nan ta ke ba tare da jin dar ba.

Manoma ma ba a barsu a bayaba wajen kaucewa a abinda ba su sanshi ba.

A don hakanne ya bukaci manoman da kada zuciyarsu ta kadu, da zarar wannan iri ya fito, to su karba su gwada za kuma su ga nasarar da hakan zai haifar musu.

Ya ce idan manomi yana samu buhu ashiri a gonarsa da tsohon irin masara, idan aka samar da wannan na zamanin to manomi zai iya samu buhu 35 zuwa 40.

Sabuwar fasahar za ta magance yunwa a kasar nan

Haka zalika Farfesan ya ce idan manoma suka fara amfani da wannan iri, to ba shakka zai taimaka wajen samar da abinci mai yawa da zai yi maganin yunwa a kasar nan.

Ya ce hatta hanyoyin samar da kudin shiga a kasar nan za su habaka ta dalilin wannan sabuwar fasaha.

A cewarsa ana gudanar da sana’o’I da dama da suka hadar da abincin kaji da sauran abubuwa da masara.

Inda ya ce matukar za a bunkasa wadannan sana’o’I jama’ da dama za su samu aikinyi za kuma a fita daga kangin yunwa.

Ko me manona ke cewa?

Ko da ya ke wasu daga cikin manona da aka zanta da su ya yin taron jin ra’ayin sun nuna jin dadin su dangane da sabuwar fasahar amma suna bukatar akara fahitar da su muhimmancin wanna iri.

A cewar Yusuf Ibrahim zai yi amfani da wannan fasaha da zarar an fito da ita domin ya tantance tsaba da tsakuwa.

Ya ce ko shakka babu ya yarda da binciken kimiyya, kuma zai karfafi abin da zarar an fito da shi.

Shima Kabiru Isa manomine da ya halarci taron ya ce su dai sai sun gwada sun gani a zahir kafin su fara ammfani da sabuwar fasahar.

Ya ce zai ware gona guda a cikin gonakin sa idan sabon irin ya fito ya kuma gwada, idan ya bashi yadda ake fada to ko shakka babu zai rungumi fasahar ka’in da na’in.

Ko menen amfanin TELA maize

La’akari da cewa adadin al’ummar kasar nan ya kai miliyan 200, Najeriya na bukatar a kalla tan miliyan 20 na masara domin ciyar da al’ummar kasarta.

Ko da ya ke rahotanni sun bayyana cewa Najeriya ce kasar da ta fi kowacce noman masara a nahiyar Afrika.

Amma ko a shekarar 2019 Najeriya ta samar da tan miliyan 18 ne kawai, da hakan ke nuna har yanzu dai ba a iya noma masarar da za ta wadaci ‘yan kasa.

Hakan ta sanya dole kasar nan ke laruwa da shigo da masara da ga kasashen ketare domin cike gibin da ake shi.

Haka zalika masana na gani sai an shigo da kimiyya wajen magance matsalar karancin masarar da ake da shi a kasar nan.

Hakan ce ta sanya cibiyar (IAR) ta tsunduna bincike a bangaren kimiyyar sauya sarrafa halitta wato (Biotechnology)

Cibiyar ta yi nazari kwarai kan yadda za a samar da sabon irin da zai taimaka wajen magance matsalar karancin masarar.

A karshe dai ta fito da wannan sabuwar fasaha ta Tela maize, wani sabon irin masara da aka kirkira da zai jure karancin ruwa, ya kuma ya ki tsutsa, ya kuma samar da amfani mai yawa fiye da wanda aka saba gani.

Haka zalika cibiyar IAR a yanzu ta dukufa wajen ganin an samarwa da manoma wannan iri da zai taimaka wajen kawo karshen karancin masara a kasar nan.

Amfanin sa

Sabon irin zai taimaka wajen rage kudaden da manoma ke kashewa wajen noma masara.

Haka irin yana yabanya me kyau ko babu wadataccen ruwa a inda aka shuka.

Haka zalika irin yana yaki da duk wata tsutsa da ke cin masara, ma’ana ita wannan masarar tsutsa bata kamata.

Sanna sabon irin yana kara adadin kwayar masarar fiye da wace ake samu idan an yi shuka ba da irin ba.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending