KANUN LABARAI
Mako daya kafin biki uwargida ta kashe amarya a Kano

Rafi’atu Ilyasu
Wata mata mai suna Suwaiba Shu’aib da ke zaune a kauyen Gimawa da ke karamar hukumar Doguwa ta kashe budurwar da mijinta zai aura mai suna Aisha Kabir mako guda kafin a daura auren.
Kano Focus ta ruwaito tun a ranar 1 ga Janairun wannan shekara ne aka nemi budurwar aka rasa, sai dai daga bisani aka sameta cikin wani kango bayan an hallakata.
A cewar rudunar ‘yan sandan jihar Kano, ta sami korafine daga mahaifin Aisha, Kabiru Ja’afar cewar sun gano gawar ‘yarsa a yashe a cikin wani kango.
Ya ce ‘yar tasa ta bata tun a ranar 01 ga watan Janairun 2021 sai daga baya ne kuma suka sameta a wani kango kusa dasu an hallakata.

Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce bayan sun karbi korafin suka garzaya domin kai dauki.
Kiyawa mai mukamin mataimakin sufurtandan ‘yan sanda ya ce sun dauki gawar budurwar zuwa babban asibitin karamar hukumar Tudun Wada domin gudanar da bincike.
‘Yan sanda sun kama mace mai garkuwa da mutane a Kano
Gwanda mu auri yayyen iyayenmu da mu auri samari marowata- Yan mata a Kano
‘Yan Film basu tallafawa Ashiru Nagoma ba-Abokanansa
Ya ce bayan da aka zurfafa bincikene kuma aka kama Suwaiba Shu’aib, wadda matace ga Shahrehu Ali da ake sa ran zai auri Aisha.
Ya ce bincikensu ya gono cewa Marigayiyar ta kwashe shekaru shida tana soyayya da mijin wadda ta yi kisan, har ma an tsayar da ranar 09 ga Janairu domin daura musu aure.
Haka zalika Kiyawa yace bayan da aka tsananta bincikene kuma sai wadda ake zargin ta amsa laifinta.
A cewar Suwaiba ta kira Aisha ne a waya, inda ta yaudareta ta kuma ja ta zuwa wani kango a makotansu.
Ta ce daga nanne kuma ta yi amfani da wuka mai kaifi ta yanketa a wuya da kirjinta da wasu sassan jikinta da hakan ya yi sanadiyyar ajalinta.
Ta kuma ce ta kashetane saboda kishin za ta aurar mata miji, kuma mijinta ya ki yarda ya fasa auren.
Kiyawa ya ce tuni aka mika lafin zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundanar yan sandan domin fadada bincike.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
