Connect with us

KANUN LABARAI

Gwamnati ta fara gididdiba gidan rediyon Kano

Published

on

Police Tricycles

Aminu Abdullahi

Gwamnatin Kano ta fara aiwatar da shirinta na yanka filaye a cikin gidan rediyo manona da ke unguwar tukuntawa da ke karamar hukumar Birni da ya shafe sama da shekaru 40.

Kano Focus ta ruwaito wannan na nuna cewa mutane sama da 1000 za su rasa sana’arsu da sukeyi a gidan

Al’umma da dama ne ke gudanar da sana’ar noman lambu a cikin gidan radiyon, inda kuma aka basu wa’adin tashi kafin shukarsu ta nuna.

An rushe dakunan yada labarai

A binciken da Kano Focus ta gudanar ta gano yadda aka rushe dakin watsa labarai dake cikin gidan rediyon, tare da sauke doguwar area dake watsa labarai.

Haka zalika an fara fitar da filotai a filin gurin wanda wata majiya tace za a fitar da filotai guda dari shida tare da fara rushe wani bangare na katangar da ta kewaye gidan rediyon.

Munyi asarar shukarmu

Danlami Muntari mai shekaru 55 ya ce da suna jin jita-jitar za a tashe su amma yanzu suka gasgata.

Ya ce masu aikin gurin sun basu sati biyu ne kawai su tashi, ya yin da galibi daga cikin masu shuka a wurin, sai nan da wata uku amfaninsu zai nuna.

Ya kara da cewa tun yana yaro karami ake zuwa dashi noman lambu a cikin gidan rediyon, har ya girma shima ya fara sana’ar ta lambu sai gashi rana tsaka za a tashe su, ba tare da sanin makomar su ba.

“A zahirin gaskiya ba wata sana’a da nasani fiye da wannan,  kuma irina suna da yawa.

“Amma ba wani shiri da akayi na sauya mana wani wurin, kuma mun shigar da korafinmu, amma har yanzu shiru kakeji, sai muyi addu’a allah ya yi mana zabi nagari.

“Ko da ba za a sauya mana wani gurin ba, yakamata a cikin fulotan muma a sanmana wasu wuraren a ciki,” a cewar sa.

Ba a sanarda mu za a yanka filaye ba

Adamu Sule mai shekaru 80 da ya shafe shekaru 60 yana sana’ar lambu ya ce ba wata sanarwa da suka samu, kawai dai sun wayi gari sunga ana aiki a cikin gidan rediyon.

“A nan nake yini, kullum da safe idan nafito nan nake zuwa inayin aikin lambu, kaga yanzu sai dai na koma gida tunda babu abinda na iya inba aikin lambu ba,” inji Adamu.

Gadon iyayenmu ne za a kwace

Dauda Balarabe dan shekara 40 ya ce sun kafa kwamiti da suka je gidan Gali Umar Na’abba don mika korafinsu, har yanzu ba wani abu da aka yi musu.

Ya kara da cewa shekara da shekaru suna samun na cin abinci a gurin, amma rana tsaka ance sutashi, wanda a yanzu basu san makomar suba.

Wani mai suna Garba Bala mai shekaru 65 ya ce sun gaji filayen gidan rediyonne a gurin kakanninsu, don kuwa shima a wancan lokacin naira dari shida ya siyi nasa filin a ciki.

Ya ce kaso 90% na mutanen da ke sana’a a wurin basu da madogara matukar aka tashesu batare da an sauya musu wani wurin ko an tallafa musu ba.

Amayarda wurin makabarta

Saidai kuma wasu daga cikin al’ummar dake yankin gidan rediyon sun bayyana mabanbanta ra’ayoyi kan matakin rushe gidan rediyon.

Sulaiman Kabiru ya ce fatansu ga gwamnati shi ne ta samar musu da makabarta a cikin fulotan da zata yanka a gurin.

A cewarasu al’umma gidan maza da sabuwar gandu na fama da rashin makabarta.

“Munyi maraba gaskiya da tashin wannan guri da za ayi, sai dai muna so gwamnati ta yiwa al’ummar wannan unguwa wani abu da zasu amfana,” a cewar sa.

Muhsin Lawan ya ce sau tari idan batagari suka yi sata da zarar sun haura gidan shikenan sun sha.

Sai dai ya ce yana fatan gwamnati za ta  tallafawa wadanda suka dauki shekaru masu yawa suna neman abinci a wurin, tare da samarwa al’ummar yankin makaranta.

“Gaskiya bana goyan bayan yanka filaye a wannan wuri duba da yadda gurin ke daya daga cikin gurararen da a jihar Kano ke samar da kayan lambu.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending