KANUN LABARAI
‘Yan bindiga sun harbe magidanci har lahira a Kiru
Aminu Abdullahi
Wasu ‘yan bindiga da ba a kai ga sanin ko su waye ba sun harbe wani magidanci mai suna Abdullahi Yunusa har lahira a garin kwanar Dangora dake karamar hukumar Kiru a jihar Kano.
Kano Focus ta ruwaito cewa maharan da ake zargi sun kutsa kai cikin gidan mutumin da karfe goma sha daya na daren ranar Lahadi inda suka harbeshi da bindiga da hakan yayi sanadiyar mutuwar sa.
A cewar matar marigayin, lokacin da maharan sukaje sun kwankwasa kofar gidan ne, bayan da suka ki budewane suka haura gidan.
A cewarta suna haurowane kuma ba wata-wata suka bude masa wuta ba tare da sun bukaci komai ba.

Ta ce lokacin da suka haura gidan saida mai gidan nata ya tambaye su ko akwai abinda suke bukata amma sai suka ce rayuwar sa kawai suke so.
Sai dai bayan suk kasheshi ne suka tattare wayoyinsa da na matan sa suka gudu.
Ta kara da cewa a iya saninta bai samu sabani da kowaba, ko a lokacin da maharan sukaje ba a iya gane kowa a cikin su ba kasancewa da daddare al’amarin ya faru.
A nata bangaren ‘yar uwar mamacin zuwaira Gambo Na’ibawa ta ce dan uwan nata sana’ar noma da kiwo da kuma sana’ar achaba ya keyi.
Ta bukaci jami’an ‘yan sanda dasu bi musu hakkinsu na kashe mata dan uwa da akayi.
Koda muka tuntubi runudunar ‘yan sanda ta jihar Kano mai magana da yawunta Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce zai tuntube mu.
Sai dai kawo loakacin hada wannan rahoto bamu samu munji daga gareshi ba.
Amma dai za mu ci gaba da bibiya domin jin matakim da jami’an yan sandan za su dauka.
Idan za a iya tunawa a makon daya gabata saida aka samu rahoton wasu da ba a san ko suwa ye ba suka bindige wani mutum mai suna Ibrahim Shuaibu a kauyen Diraman dake karamar hukumar ta kiru.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
