KANUN LABARAI
Yadda rikicin Abduljabbar ya jawowa Ganduje farin jini a Kano
Mukhtar Yahya Usman
Farin jinin gwamna Kano Abdullahi Umar Ganduje na ci gaba da habaka a jihar Kano tun bayan da ya dauki matakin dakatar da Abduljabbar Nasiru Kabara daga yin wa’azi.
Binciken da Kano Focus ta yi ta gano yadda gwamnan ke ta shan yabo daga mutanen da a baya suka nuna a zahiri basu kaunarsa saboda dalilan siyasa.
Galibin matasan sun wallafa kalamai na nuna jinjina da yabo ga gwamnan a shafukansu na sada zumunta wato Facebook, twitter da saurasu
Haka Zalika irin manyan mutane masu fada aji da kuma malamai da a zahiri ake ganin basa tare da gwamnan sun fito karara sun nuna jin dadinsu da goyon bayansu kan matakin na gwamna.

Sarkin Sunusi II
Tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi II wanda ake ganin ba a ga miciji tsakanin sa da gwamnan Ganduje na daga cikin wanda ya fito karara ya yabawa gwamnan.
Sunusi ya ce gwamnan Kano Abdullahi Ganduji ya yi matukar koakri kan matakin da ya dauka, kuma ya cancanci yaba masa.
Ya kuma yi wannan yabo ne lokacin da yake gabatar da karatun da ya sabayi duk mako ta kafar ZOOM mai taken ‘Muhammadu Sunusi weekly lecture’
Ya kuma yabawa malaman Kano da suka hade kansu wuri guda suka kalubalanci Abduljabbar.
Sheik Amiunu Ibrahim Daurawa
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa na daga cikin malaman Kano da suka goyi bayan gwanan dari bisa dari kan matakin da ya dauka akan Abduljabbar Kabara.
Haka kuma ana ganin kamar akwai taukun saka tsakanin gwanan da malam Daurawa, amma hakan ba ta hana malamin ya yaba kokarin nasa ba.
Wannan dai ya nuna irin namijin kokarin da gwmnan ya yi wajen ajiye siyasa ya kuma yi abinda ya kamata, a cewar jama’a da dama.
Sheikh Karibullah Kabara
Sheikh Karibullah sheik Nasiru Kabara na daga cikin malaman Kano da suka fito fili karara suka nuna goyon bayan su ga matakin da gwamnan ya dauka kan dan uwanasa.
Malamin ya fito fili inda ya nuna takaicinsa kan irin abinda Abduljabbar aka ce yana yi.
Ya kuma yi fadan malaman da za su zauna da shi su samu galaba akan dan uwan nasa.
Haka zalika jama’a da dama ne suka hau shafukasu na internet suka kuma yabi Gandujen kan irin kokarin da suka ce ya yi.
Galibin irin wadannan mutane basa ga miciji da gwamnan saboda dalilin siyasa.
Abu-fatima Abdulwahidi ya rubuta a shafinsa na facebook cewar “abinda zai sanya Dan Kwankwasiyya ya yabawa Ganduje Wallahi kai kasan wannan yakin ya wuce aikin duk wani dan adam.
Ka isa kaja da wadanda suka yi yaki tare da taimakon mala’iku.
Abba Aminu shima ya wallafa a shafinsa na facebook cewar.
“Mai girma gwamna Ganduje bai taba burgeni ba irin yau,Allah ya saka da alkhairi khadimul islam’
Allah ya kara mana son Annabi da sahabban sa da alayensa.
Musa G Usman Damaturu, ya ce “Ganduje mun yafe maka saboda aikin kirkin da kayi”
“Dole mu yabawa Ganduje kan aikin alheri da yayi na ruguza wannan dan tamoren Abduljabbar
“Ah Gaskiya Ganduje ka kyauta kuma muna maka fatan alheri dafatan samun cikakken shiriya daga Allah.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
