Connect with us

KANUN LABARAI

Zamu ci gaba da tsaftace harkar magani a Kano-Bappa Dan Agundi

Published

on

Aminu Abdullahi

Halastaciyyar kungiyar masu saida ingantattun magunguna ta kasa reshen jihar Kano ta mika gurbatattun magunguna na kimanin naira miliyan 100 data kama ga hukumar dake kare hakkin masu ciniki ta jihar Kano.

Kano Focus ta ruwaito cewa wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar kare hakkin masu ciniki ta jihar Kano Nabulusi Abubakar Kofar Na’isa ya rabawa manema labarai a ranar Litinin.

Shugaban kungiyar Hussain Labaran ya ce sun samu kwarin gwiwar hada hannu da gwamnatin Kano wajen yaki da jabun magunguna da wadanda wa’adin su ya kare sakamakon irin kokarin da gwamnatin keyi.

Ya kara da cewa mambobin kungiyar sun amince su tallafawa  hukumar ta consumer protection ne don tabbatar da kudirin shugaban hukumar Bappa Babba Danagundi na tsaftacewa tare da tabbatar da yin amfani da magungunan da aka yarda dasu.

A nasa bangaren shugaban hukumar Baffa Babba Dan’agundi ya bayyana shirin sa na hada hannu da kungiyar don yaki da jabun magunguna a fadin jihar Kano.

Haka zalika ya yabawa kungiyar bisa kokarin ta na hada kai da gwamnati wajen kawo karshen ta’amali da miyagun kwayoyi ta hanyar fitar da gurbatattun dake cikinsu, musamman wadanda ke shigo da magungunan da aka haramta amfani da su.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar Kano ta basu umarnin hadakai da kungiyar kuma za su lalata jabun magungunan da suka karba nan bada dadewa ba.

Ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki dasu hada hannu da gwamnatin jihar Kano don yaki da masu safarar miyagun kwayoyi dake barazana ga lafiyar al’umma jihar.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending