KANUN LABARAI
Baka da ‘yancin da ya fi mallakar katin dan kasa-Sarkin Karaye
Mukhtar Yahya Usman
Mai martaba sarkin Karaye Ibrahim Abubakar na II ya bukaci al’ummar masarautar sa da su tabbata sun mallaki katin dan kasa.
Kano Focus ta ruwaito wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na masarautar Haruna Gunduwawa ya fitar a ranar Litinin.
Ta cikin saanrwar sarkin na wannan kira ne ya yin da ya karbi bakuncin shugaban Hukumar katin dan kasa (NIMC) shiyyar Kano Lawan Yahya ranar Litinin a Fadar sa.
Sarkin ya ce katin dan kasa na da muhimmancin gaske a don hakan ne ma ya zama waji ba jama’a su ta shi su mallaka domin kare kansu da ga wasu matsalolin rayuwa.
Ya kara da cewa masarautar Karaye a shirye ta ke ta baiwa Hukumar ta NIMC dukkanin hadin gwiwar da suke bukata wajen ciyar da ayyukan su gaba.
Mr Ibrahim ya kara da cewa yana daga cikin abin da masarautar ta sanya a gaba, rungumar duk abin da ke da muhimmanci hannu biyi.
A nasa jawabin shugaban Hukumar ta NIMC shiyyar Kano Lawan Yahya ya ce sun je fadar Sarkin ne domin neman taimakon sa wajen gudanar da ayyukan su.
Ya kara da cewa da hadin gwiwar masarautar zai taimaka musu ainun wajen cimma nasarar ayyukan su.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.